← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 142

Sashe 127

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi.
Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa.
Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka.
Cikin ƙarfin hali Jamil yace.
"Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan.
Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden."
Cikin tashin hankali Ummi tace.
"Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa Lamiɗo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama."
Da sauri Aunty Juwairiyya tace.
"Eh yafi kam".
Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti.
Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace.
"Shatu! Shatu!! Shatu!!!".
Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi ɗaya bayan ɗaya.
Ganin hakane Jamil ya matso.
Tofi ya farayi mata.

Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi.
Cikin tsoro Hibba tace.
"Ummi kinga idonta ya koma dai-dai."
A tare sukace Alhamdulillah.
Sai kuma Ummi ta kuma kiranta.
"Shatu!".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi.
Murya a sanyaye tace.
"Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona.
Gaya min ya za'ayi sharar".
Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
"No ki huta kawai my Aunty zan share".
Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar.
Bazata iyaba jikinta duk a mace.
Hakane yasa tace to.
Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa.
"Ummi ɗan jamin hannuna mana".
To tace tare da kamo hannun.
Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanɗa ta juya ta nufi hanyar fita.
Binta sukayi a baya gaba ɗayansu.

Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin ɗakin kana.
Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows.
Kana ya goge ko ina fes
Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.

Su kuwa suna biye da ita har falonta.
Ganin ta wuce bedroom ɗinta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.

Ita kuma Ummi tabi bayanta.

Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.

Can babban falon suka koma suka zauna.
"Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki".

Ummi ta faɗa cikin al'hini.

Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace.
"Sosai kam wannan al'amari ya firgitani".
Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.

Nan sukayi ta mamakin wannan abin.

Jamil na fito shida Jalal suka tafi.

Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.

Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna.
Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa.
"Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru".

Kai kawai Hibba ta kaɗan mata.

Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.

Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo.
Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun.

A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati.
Kana ta tashi zaune.
Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan ɗumi.
Kana tayi al'wa tana fitowa.
Ta zura Hijabi tayi salla.
Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror.
Simple makeup tayiwa fuskarta.
Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai ɗan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da ɗigo-ɗigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta.
Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar.
Ta saketa bisa kafaɗunta.
Ɗaurin asseta tayi ya zauna ɗas a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaɗunta.
Kana ta fesa turarukan ta masu daddaɗan ƙamshi.

Sosai jan lallen gargajiya dake kan ƴan fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau.
Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ƙafafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai,
Ta fito ras da ita.

Baki ɗauke da sallama ta foto falon.
Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta,
Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu.
Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na ɗaukarta hoto tana cewa.
"My Happiness Aunty kinyi kyau".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na kaiki ne?".
Da sauri Hibba tace.
"Kin fini ma".
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
"Ngd matuƙa".
Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me zamuyi abincin dare".
Cikin jin tausayinta Ummi tace.
"A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki".
Kai ta jujjuya alamar a a kana tace.
"To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko".
Cikin gamsuwa Ummi tace to.

A can Airport kuwa ƙarfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar Joɗa ta sauƙa.
Nan motoci suka kwatsosu.
Suna isa masarautar ana kiran sallan la'asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan.
Masallaci suka wuce.
Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki ɗayansu.

A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daɗi tayi tare da cewa.
"Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata...!

By
*GARKUWAR FULANI*Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin.
Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu.
Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi.
Zuciyarshi nike da mamaki.
Haka yaci gaba da ɗawafin.
Saida sukayi. Kana suka fito.
A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco.
nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta.
Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma.
Kuma sa'ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu.
Cikin hausarsu data fara basu wuya tace.
"Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take"

Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba".
Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu.
Kuma suna masifar shiri.
Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.

Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi.
Shiyasa taketa murmushi.
Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa.
"Wai auren ya kusa ko?".
Cikin jin kunyar Umaymah tace.
"Ban saniba."
Haka dai sukaci gaba da tafiya.

Washe gari da safiya.
Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.
Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai.

Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma.
Wanda ciki ƙasar Nigeria yake.
Tun daga idar da sallan asuba.
Saratu da Larai sukazo.
Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen.
Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar.
Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa.
Bayan sun gamane suka killace shi gefe.

Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau.
Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu.
Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace.
"Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau".
Cikin jin daɗi Ummi tace.
"Gsky nima naji daɗin wannan abu.
Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota.
Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu.
Su kuma akeci kullum".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu".
Da sauri Hibba tace.
"Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal.
Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya.
Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko".
Cikin sauri tace.
"Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?".
Da sauri tace sosaima.
Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago.
Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin".
Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin.
Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama.
Chapter 127 · 0% Book details