← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 142

Sashe 108

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ana idar da salla zai shigo, gida al'adar rayuwarsace tun yana yaro.
Zaiyi baccin awa ɗaya tsakanin azahar da la'asar.
Ƙarfe uku dai-dai na yamma zai tashi zaiyi wonka, ya canza shiga, kafin ya gama an kira salla.
Yana fitowa zai wuce masallacin Masarautar Joɗa, inda yake limanci ana idar da salla zai tafi masallacin jumma'ar dake jami'ar Joɗa. Inda zaiyi tabsir daga ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma zai taso.

Akan hanyar shi ta dawowa yana tsayuwa wurin mashigar laleko zai sayo kayan buɗa baki ƴaƴan itatuwa.
Yana dawowa zai ajiyesu.
Ya wuce Side ɗinsa, wonka zaiyi kana yasa sauƙaƙƙun kaya, ya dawo falonshi ko ya wuce cikin Garden acan zaiyi ta karatun al'ƙur'ani ko kuma wani lokacin ya ɗan konta ya huta.

Kafin lokacin shan ruwa, Ni kuma da hadimar da Gimbiya Aminatu ke bani duk Ramadan ta tayani aiki.
Tuni mun gama aikin buɗa baki. An shirya komai a dinning table, nasu Jalal kenan.
Suma kuma gab da magriba zasu zo.
Shi ma zai fito yakan zauna tsakiyar Jalal da Jamil ko kuma tsakiyar Jalal da Jafar.

Baya cin abu mai nauyi iya karshi dabino da inabi da tuppa, sai ruwan zam-zam wanda dashi yakeyin buɗa baki.
Daga nan zai wuce masallacin Masarautar Joɗa wani lokacin zai fita dasu wani lokacin zai rigasu fita.

Ana shirya mishi abincinsa na musamman a ajiye mishi a dinning table ɗin dake can falonshi a Foodflaks ɗin shi na musamman, wani lokacin Gimbiya Aminatu ke aiko mishi.

In ya fita bazai dawoba sai anyi sallan isha'i Dana asham.
Amman su Jalal su zasu dawo suci abinci kafin isha'i sai su koma masallacin.

Idan ya tashi daga Masallacin kai tsaye zai wuce.
Gidan radiyo ABC Ɓadamaya, inda yake gabatar da shirin.
"Fatawa. Za'a ayi mishi tambaya kan Ramadan dama sauran abinda ya shafi addini yana amsawa, wasu kan tura tambayoyin wasu kuma kira sukeyi a da number da ga suke badawa, suyi tambaya ya bada amsa.
Ƙarfe takwas da rabi ake fara shirin tara dai-dai ake gamawa.
Tara da mintuna ashirin yake isowa gida".
Ɗan tsagaitawa tayi ta kalli Shatu dake cewa.
"Tab agogo sarkin aiki to shi baya gajiya ne, ga azumi ga zirga-zirga ga kuma duk inda yaje dole ba shiru zaiba mgna zaiyi ai ƙishi zai mishi illa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To ai in yaje gidan radiyo tarba ta musamman akeyi mishi, sai dai shi ba ko ina yake cin abinci ba tunma yana yaro.
Ko a gida nan ba abincin kowa yake ciba.
To shiyasa tara da rabin nan zai dawo a gajiye cikin yunwa,
to nan zaici abinci sosai.
Kana yayi wonka zuwa sha ɗaya dai yayi bacci.

To ƙarfe biyu kuma zai tashi, wani lokacin ma biyu bayayi zai tashi yayi ta nafilfilinshi da karatun Alqur'ani.

Daga nan kuma baya komawa bacci.
Har ayi sahur ayi sallan asuba.
In ya dawo yayi Azkar, to nanne yake samun yayi bacci mai tsawo dan tun bakwai da rabi ko takwas na safen zaiyi bacci sai goma zai tashi ya fara shirin tafiya masallacin jumma'a na kasuwa."
Kallonta ta ɗan yi tare da cewa.
"Kin gane lokutan da yake aiki Dana hutuwa dana bacci ko dana cin abinci ko?".
Cikin murmushi tace na gane.
"Da safe zai sha bacci son ranshi, daga takwas zuwa goma kafin ya tashi ya shirya.
Yaje masalacin jumma'a na kasuwa sha ɗaya tayi yayi tabsir ɗin awa ɗaya, daga nan ya dawo masallacin Masarautar Joɗa,
shabiyu ya fara tabsir sai ƙarfe ɗaya ya gama, ayi salla ya dawo.
Ya sake shan baccin awa ɗaya.
Kafin kuma ayi la'asar ya tafi masallacin Joɗa state University. Yaje yayi tabsir in ya dawo, kuma ya lokacin hutawane har magriba.
Daga nan kuma ayi buɗa baki a wuce masallacin daga can a wuce ABC.
Sai tara a dawo.
To yaseen wataran yunwa zata kadashi a hanya, ƙattin rigunan nan da yake sawa sune zasu jashi su kaishi ƙasa.
To ma wai Ummi to yaushe yake zuwa aiki kuma?".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To in baya garin an turashi wani state ɗin yana zuwa aikin ne?".
Kai ta girgiza alamun a a.
Cikin murmushin Ummi tace.
"Shiyasa ko yana nan in dai a Ramadan ne baida lokacin zuwa Valli Hospital, bare Genaral Hospital ko kuma Asibitin jami'ar Ɓadamaya.
Shine dalilinshi na ƙin yin aiki a asibitin gwamnati sai ƙarshen sati-sati yake zuwa sau ɗaya, duk wanda zai duba kyautane aiki".
Naɗa hannunta tayi tare da cewa.
"Batun yunwa ta kadashi kuma, yanzu aikin kine, kula da abinda zaici".
Taɓe baki tayi tare da cewa.
"To shi wannan da tsarabe-tsaraben falsafa nasan irin abinda zai cine ma.
Mutun fuska a haɗe kullum kamar mai damuwar rashin jigo".
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
"To kika sani ko hakanne.
Kuma ai gani duk abinda kike son sani a kanshi tambayeni.
Abincin da yafiso kuma yafi son ganyayyaki, fruits and vegetables sai kuma kayan ruwa, kana yana son nama da kifi in an mishi irin sarrafawar da yakeso.
Sannan yana son abincin gargajiya wasu lokutan musamman a wurin yin sahur.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Uhumm lallai kam, wannan ai yafi Lamiɗo ma iya ƙasaita".
Dariya tayi tare da cewa.
Zo muje store kiga kayayyakin da yasa aka kawo ɗazu."

To tace tare da miƙewa tabi bayanta.
Suna shiga kitchen ɗin suka ɗan haura suka taka steps ɗin da zai sadasu da ƙofar store wanda wani ƙaton freezer ke konce a wurin sai ma dai daicin Fridge.

Hannu Ummi tasa ta buɗe freezer'n.
Motsowa tayi tare da zaro ido ganin yadda aka cika freezer'n maƙil dasu Kabej Karas kokumba green beans, masu kyau sabbi.
Ɗaya sashin kuma nama ne jibge sai kifi a gefe,

Sai ɗaya Fridge ɗin kuma cike yake da ababen sha na ya'yan itatuwa dana kwalba.

Rufewa tayi kana ta buɗe mata drower'n kitchen cabinets ɗin.
Kiret-kiret ɗin kwaine kusa goma suke jere a wurin ɗaya gefen kuma katon ɗin manyan gongonayen madara da millo ne.
Sai katon ɗin sugar irin mai ƴaƴan nan. Sai katon ɗin Lipton. Da ganyen na'ana. Sai can gefe kuma su maggine da sauran kayan ɗanɗano.
dasu kanan fari citta da dai sauransu.
Cikin yin hamma tace.
"Ummi duk yaushe aka kawosu?".
Juyawa tayi suka nufi cikin cikin store tace.
"Ɗazu da yamma kina bacci ya dawo, suda Jalal da Jamil".
Kai ta gyaɗa tare da bin bayan Ummi. store ɗin cike yake da kayan masarufi na buƙatar rayuwa.
Danginsu shinkafa, gero, waken suya, wake ƙosai dasu alale, sugar katon-katon na taliyar manya data yara, da dai sauransu.

Sai kuma doya da dankali dake jibge a gefe, kana sai al'basa da sauransu.

Fitowa sukayi kana suka dawo kitchen.
tukunya Ummi ta ɗaura tare da ɗebo nama tazo ta wonke sabida an yanka wasu dai-dai misalin na miya, wasu kuma anyisu dogo-dogon yanka.
a tukunyar ta zuba shi, kana ta ɗauko al'basa mai girma ta yayyanka a ciki.
Sannan tasa tafarnuwa kaɗan kana tasa garin citta da kanamfari.
Tare da maggi da kori da sauran kayan ɗan-ɗano.

Kana ta kunna Gas ɗin ta ɗaura tukunyar,
ɗanyen kuɓewa ta ɗebo ta miƙawa Shatu tare da cewa.
"Wonke ki yanka min shi".
To tace tare da amsa ta wonke kana ta fara yankawa, ita kuma Ummi al'basa da tattasai da tatuhu kaɗan ta ɗiba ta wonkesu kana ta markaɗesu dai-dai yadda takeso.

Zuwa lokacin kuma gaba ɗaya kitchen ɗin dama Side ɗin gaba ɗaya ya cika da ƙamshin tafashen naman.

Juyeshi tayi a wani kwano.
Kana tasa mai kaɗan tasa manja kaɗan. Tare da watsa jajjagen kayan miyar,
ta soyasu. Kana tasa naman da sauran ruwan tafashen.
ta kuma ɗauko bandan kifin tarwaɗa bandanshi, ta gyara ta wonƙeshi da ruwan ɗumi.
ta watsa a ciki. Sannan tasa ɗan dakekken yajin daddawa kaɗan."
sannan ta rufe tukunyar.
ta amshi kuɓewar tana ƙarisa yankan. Tukunyar data ɗaura ruwan tuwo ta ɗan kalla ganin yana tafasane tace.
"Gacan garin semo na tankaɗeshi ɗibi kiyi mana talge."
To tace tare da juyawa ta ɗebo tayi talgen.
Ita kuwa kuɓewar ta saka, kana ta tsalli ɗan toka ta saka.

Bayan wasu yan daƙiƙu miyar tayi lugub tayi kyau tayi kalar kore mai kyau. sabke tukunyar tayi kana tasa,
man shanu a ciki.
Sannan ta meda tukunyar gefe.
Tuwon ta tuƙa ya ɗan turara kafin ta kwasheshi tana yin mal'mala tana sawa a leda.
Saida ta cika wani madaidaicin Foodflaks mai ɗan girma.
Kana ta ɗauka ruwan zafi.
Ta tafasa tea ta ɗura a flaks tare da tarfa kanumfari da citta sai na'am.
Sannan ta rufe, ta kimtsa komai a kitchen ɗin.
Ganin Shatu nata Hamma ne tace.
"Jeki kwanta tunda mun gama aikin. Sai kuma da asuba."
Cikin alamun bacci tace.
"To Ummi saida safe".
Ta fita tana haɗiye minyau dan ƙamshin da miyar keyi.

A falo taci karo da Hibba Aunty Juwairiyya ta rakota, da Foodflaks a hannunsu alamun abincin sahur ne a ciki.
Cikin baccin da takeji tace.
"Mun yi girki ma, Aunty Juwairiyya".
Kai Juwairiyya ta ɗan gyaɗa tare da cewa.
"A lallai kam sannu da aiki".
Ta ƙarishe mgnar tana ajiye kulolin bisa dinning table.
Ita kuwa Shatu harara ta watsawa kulolin tare da wucewa tayi ciki.
Hibba ce ta biyo bayanta bayan tayiwa Aunty Juwairiyya Saida safe.

Har sun shiga Ummi ta kira wosu.
Falo suka dawo duk suna hamma alamun bacci, ganin Hamma Jabeer na zaune ne, gasu Jalal gaba ɗaya yasa suma suka ƙarasu cikin falon.
Gyara zanshi yayi tare da kallon Hibba da Aysha da duk alamun bacci ya cikasu, cikin sakekkiyar murya yace.
"T....!

Uhummm Ramadan da daɗi, Ya Allah ka nuna mana ka kaimu watan lfy ka nuna mana ƙarshensa lfy ka maimata mana.

Rayuwar Masarautar Joɗa a Ramadan yanada tsari da masifar daɗi da burge duk musulmi.

Kabcen Shatu da Sheykh a kwanakin Ramadan da bikin salla yana sani murmushi da shauƙi.😘🥰🤝🏻
Chapter 108 · 0% Book details