← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 142

Sashe 124

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri tace.
"Dama.. dama!!...".
Gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Sauri nakeyi zan tafi masallaci, kada kisa na rasa damata".
Cikin rauni da muryar dake nuna cewa tana zubda ƙwalla tace.
"Ayyah dan Allah da Manzonsa.
In kaje kayi min addu'a a harami mana".
Juyowa yayi yana kallon Haroon da Ya Hashim da suka shigo yanzu alamun kiranshi zasuyi.
Cikin wata iriyar murya a hankali yace.
"Addu'ar me zan miki?".
Murya na rawa tace.
"Allah ya dawo min dasu Yayana lfy, ya kare minsu a duk inda suke, ya baiyana sucikin gaggawa".
Cikin rashin fahimtar zancen nata yace.
"To zan miki saboda Allah da Manzonsa da kikace".
Cikin jin daɗi tace.
"Ngd matuƙa Allah ya biya maka buƙatunka."
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da lumshe ido a hankali yace.
"Amin ya rabbil izzati, kema kuma kiyita addu'a ki dage da ambaton Allah zai cika mana dukkan burinmu".
Yana faɗin haka ya katse kiran.

Ita kuma murmushi tayi tare da share hawayenta.
Cikin sanyi tace.
"Ya Allah ka dubemu da idon rahama".
Hibba dake shigowane tace.
"Amin Amin."

Daga nan suka fito falo suka kama sabgoginsu.

A kwana a tashi asarar mai rai.
Yau da gobe kayan Allah.
Kamar yau aka kama azumi gashi yau an kai azumi na ashirin da tara.
Wanda ake tsammanin tsalla gobe ko jibi.

Irinsu Hibba duk sunfi fatan wata ta dawo yau.

Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne.
Zabbin da Jalal ya kawo bisa umarnin Hammansun.
Da kuma kajin da Lamiɗo yasa aka rabawa al'ummar masarautar Joɗa.
Ko wani Side in dai akwai mace kaji goma ake kaiwa.
Da tarin kayan miya komi da komi, wanda shi cikin lambun masarautar ake cirewa.
Kajin kuma daga gidan Gidan gonar MJ aka kawo, kana zabbin da aka kawo manyan sashin Masarautar Joɗa ma daga gidan gonar MJ aka kwasosu. Haka ƙoyayen kaji.
Duk an rarraba ko ina.
kuma duk saida aka yanka su aka gyarasu aka rarrabusu, dan haka aiki kawai aka fara babu kama hannun yaro.
Hadimai da bayi sunata aiki.

Duk sauran ɗinku nan suma sun dawo.

Kasan cewar kusan a kitchen ɗin suka wuni ne, yasa Shatu ta ɗauki zabbi uku tun da azahar tayi musu gyara na musamman.
Hibba kuwa tana Side ɗin Aunty Juwairiyya anayi mata zanen lalle.

Akan sai dare za'ayiwa Shatu shiyasa taketa kimtsa aiyu kanta da wuri.
Dama sunje da sassafe an wonke musu kai an gyara musu.

Ummi kuwa tayi lallenta na gargajiya tana kwance a falo.
Hakane yasa Shatu ta kira Gimbiya Aminatu.
Cikin wasa tace.
"Gimbiya a ƙaro min mai taya aiki yau Ummi na tasa lalle, Hibba ma tana can ana zana mata, nida Sara ce kaɗai a kitchen."
Dariya Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"To Sayyadar Sheykh bari Larai tazo".
Cikin jin daɗi tace.
"To Gimbiyar Lamiɗo".
Dariya sukayi duka kana sukayi sallama.

Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"Tace zata turo Larai, Ummi ta iya aiki ko?".
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
"Sosai ma kuwa".
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana ta miƙa wa Ummi wayarta tare da cewa.
"Ummi sai mun nitsu ki bani number Gimbiya Aminatu".
To tace kana ta koma kitchen ɗin.

Wanke zabbin tayi fes tare da ɗan matsa lemun tsami kaɗan a ciki.
Kana ƙara lallaɓeshi.
A tukunyar ƙirar ƙasar Cameroon ta zubasu.
Kana tasa al'basa, Curry, Maggi, kanamfari, citta, tafarnuwa kaɗan, da gishiri ɗan ƙanƙani.
Ta rufe tukunyar da zabbin uku suka cikashi.

Bisa gas ta ɗaurashi kana tasa wutan dai-dai.

Saratu kuwa sa sauran tayi a babbar tukunta tasa kayan ƙamshi da ɗanɗano.
Sannan ta ɗaura.

Dai-dai lokacin Larai ta shigo.
Bayan sun gaisa ne, ta ɗauki markaɗen waken ƙosan da zasuyi na kaiwa masallaci.

Da markaɗen tattasan da taruhu da al'basan.

Ita kuwa Shatu yau kunun basise ta dama mai kyau, ta cika kulolin.
Kana
Ta daura ruwan tea
Yana tafasa ta ɗura a flaks.

Duk wannan zabbin sunata sulaluwa suna bararraka sai wani irin masifeffen ƙamshi da yake tashi.
Har yawunsu na tsinkewa.

Fruits ta ɗebo a Fridge ta gyarasu ta shiryasu a tray biyu shiri mai kyau.
Kana ta medasu cikin ƙaramin Fridge ɗin data kashe dan sanyi su ya daidaita.

Larai na dawowa, suka fara suya.

Ita kuma ƙullun waken kaɗan ta ɗiba.

Kana tasa dafaffan ƙan data ɓare.
Da al'basan da kifin data tafasa ta murmusa a cikin ƙullun ta sa mai da Maggi curry da dai sauran kayan haɗi ta kulla alala.
Ta ɗaura a gefen tukunyar zabbin.

A ƙalla awa ɗaya zabbin na ɓararraka kana tazo.
Tasa jajjagen taruhu da al'basan,
A ciki.
Sai ta ɗan tarfa soyayyan mai kaɗan a ciki ganin kamar man jikin zabbin bazai mata yadda takeso ba.
Kayan ɗanɗano ta kuma sawa, da yankekken al'basa mai yawa ta zuwa a ciki.
Kana ta maida marfin tukunyar ta rufe. A hankali danderun zabbin ya fara taushi yana lugub cewa,
Ƙasusuwan suna saɓulewa daga jikin naman.

Tuni su Sara kuma sun gama soya ƙosan, nan ta ciccika kulolin da za'a fidda kana ta ɗiba musu nasu, daban.
Sannan suka tattare mata wurin suka tafi sabida ita ta kusa gama nata aikin.

Koda alalan ya nuna ta kwashe tasa a kuloli biyu.
Sai kuma ƙaramar kula daya.

Ya rage zabbin ne kawai a wuta.
Rage wutan tayi sosai yadda zasuke jin wutar na ratsasu da kyau.

Tattare wurin tayi ta kimtsa komai.
Kana ta fito falo.
Ƙarfe biyar da rabi.
Tace lokacin data zauna ta ɗauki wayarta Ummi kuwa na cire lallenta.
Ya kuwa yi baƙi yayi kyau.
Hibba ce ta shigo cikin
Langwaɓe kai tace.
"Aunty Shatu me ake dafa mana yau tun waje can ake jiyo ƙamshin na fitowa a gidanki".
Cikin gajiya tace.
"Tuwone miyar taushe".
Cikin zumbura baki tace.
"Tab wlh bazanci ba, inyi azumi a bani tuwo ta yaya zan haɗiyeshi, yaseen zan koma wurin Aunty Juwairiyya nagama tayi awara, ƙamshin gidanki na jiyo na gudo".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Hibba dai cokali a saki a daɗi ko?".
Murmushi sukayi dukansu kana suka konta
A kan kujerun.
Ganin Ummi ta miƙene yasa Shatu cewa.
"Yauwa Ummi duba mana kitchen ɗin kiga ko Danderun yayi".
To tace kana ta shiga ta duba.
Sannan ta fito tare da cewa.
"Yayi sosaima, kai gskyar Hibba nima da bana jin ƙamshi yau naji ƙamshin girkin.
Jeki sauƙe kawai kiyi wonka kuzo ki huta kafin a kira salla".
To tace kana.
Ta miƙa taje ta sauƙe. Binta a baya Hibba tayi tare da cewa.
"Wai Aunty Shatu bakuga lallena bane banji kunce yayi kyau ba".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kayya Hibba ai yanzu kam idanunmu basa gani".
Ta ƙarshe mgnar tana sauƙe tukunyar,
Kana ta ɗauki Foodflaks guda uku biyu manya ɗaya karami.
Gaba ɗaya ƙasusuwan sun saɓule.
Romon yayi kaurin diddigin nama.
Rabin zabuwa ta sawa Sara da Larai a ƙaramar kular.
Kana tasawa Gimbiya Aminatu gudar.
Su kuma tasa musu ɗaya da rabin a kularsu.
Kular datasa alala data kosai ta jere a babban tray'n.
Da tray'n fruits, ɗin a gefe.
sannan da flaks ɗin kunu ta bawa Hibba tare da cewa.
"Ki kawai Gimbiya Aminatu.
Na ƙaramar kular nasu Sara ne".
Amsa tayi kana ta fita.

A can ta samu Ya Jafar shida Lamiɗo bisa alamu yau tare zasuyi buɗa baki.

Ita kuwa Shatu Hibba na fita.
Ta sauƙe babbar tukunyar tafashen naman kajin ta ajiye gefe.
Dama zabbin duk a freezer'n suka sasu.

Ɗan buɗe bakin tukunyar tayi yadda zasu sha iska su kama jikinsu. Jajjageggen Attaruhu da al'basan kuma ta sashi a Fridge.

Kana ta fito da komai ta jere musu a dinning table.

Sannan ta wuce ɗakinta. Wonka tayi da ruwan sanyi duk da bata son sanyi
To amman duk jikinta huruwa yake tamkar wuta.
Haka yasa tayi da ruwan sanyi.
Tana fitowa ko mai bata shafa ba.
Wata atamta mai taushi riga da zani, ɗinkin Borno sitayel
yayi masifar yi mata kyau.
Ɗan kwalin ta ɗaura a sauƙaƙe sabida duk jikinta rawan yunwa da azaba yakeyi.

Cikin falon ta fito nan ta samu Hibba ta dawo.
Jalal, Jamil, suma sun zo.
Ummi ma ta fito da alamun tayi wonka.

Tana isa ana kiran salla.
Nan sukayi buɗe baki da fruits kawai sai kunun suka ɗansha, kana kowa yaje yayi sallan.
Sannan sukazo sukaci sauran kayan kwalamarsun.

Suna tashi sukayi sallan isha.
Zuwa lokacin kuma anata raɗe-raɗin ba'aga wata bafa.
Wannan lbrin shiya tada hankalin Hibba da sauran mutane irinta, a gefe harma da Jamil
Sabida azumi ɗayan nan da za'a ƙara wasu ganinshi suke kamar shekara ɗaya za'ayi ana azumin sai kaji anata gunaguni da cewa wai anƙi a faɗa ne.
Shatu kuwa murna tayi dan ita bata samu tayi lalle ba.
haka yasa gobe zata ƙarisa aikinta a nitse.
Jin an kira salla za'ayi Asham ne yasa Hibba zubda hawaye tare da cewa.
"Wlh zan kira Umaymah da Hamma Jabeer ina dai saudi sunyi salla Ni babu ruwana salla zanyi".
Ta ƙarishe mgnar tana kiran layin Umaymah yanata ringin ba'a ɗagawa.
Hamma Jabeer kuwa data kira baya shiga ma gaba ɗaya. Haroon kuma shima yana shiga baya ɗagawa.
Dariya Shatu tayi tare da kunna tv tace.
"kalli Hibba suma asham sukeyi".
Da sauri tace.
"A a kam Isha'i ne".
Ganinfa da gaske Hibba keyi yasa suka sherata sukaje sukayi asham kana suka dawo.
Kitchen suka shiga, soya kajin sukayi suya mai kyau kana suka ajiye.
A gefe.
Jalal ne ya leƙo kitchen yace.
"Ummi azumi talatin zamuyi bana".
Dariya tayi tare da cewa.
"Aiko gacan Hibba nata fushi."
Shigowa yayi plate ya ɗauka ya miƙawa Shatu tare da cewa.
"Aunty a samin nan".
Amsa tayi tare da saka mishi soyayyen naman kazan.
Dakekken yaji ta saminshi a gefen
Fridge ya buɗe ya ɗauki Du-du tare da cewa.
"Wannan fa yaushe aka fara kawoshi".
Ummi ce ta kalleshi tare da cewa.
"Naga Shatu tafi sonshi ne yasa nace akawoshi".
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
"To nima bari in taɓa shi".
Nan ya fita falon.
Chapter 124 · 0% Book details