← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 142

Sashe 54

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Jalal, shiru yayi yana riƙe da hannun Jafar ɗin.
Jamil kuwa katse kiran yayi.
Affan kuma wanda dama tare suka shigo, fuska ya ɗan kele, cikin irin matsayin da ƴan auta kedashi a wurin iyayensu yace.
"Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaɗamu, ya za'ayi keda kanki ki rinƙa suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamɓaɗe mukeba,
Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki ɗan uwanmu nefa".
Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace.
"Ɗan uba dai ba ɗan uwaba".
A tare suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya.

A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa ɗinne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu.
Shiru mutanen fadar sukayi baki ɗayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ƙare zancensa da cewa.
"Babban tashin hankalinmu, kullum ɗauki ɗaɗɗayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu.
Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu."

Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa.
Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin.
Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi.
Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace.
"A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa.
Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!".
Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa.
"An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki."
Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu.

Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu,
cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace.
"Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa,
Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake."
Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu.
Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe,
Da sauri ya rusana ya koma gefen.
Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa.
"Imrana, kiramin Sheykh Jabeer."
Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi.
Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu.

Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi.

Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa.
"Wata ƙil baya kusa da wayar."
Kai ya jinjina mishi tare da cewa.
"A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira".
Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa.
Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala.

Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.

Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.

Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa,
cikin tarin girmamawa yace.
"Barka da hantsi, Hamma Jabeer".
A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru.
Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace.
"Afwan Sheykh Assalamu alaikum ".
Murya can ƙasa yace.
"Wa alaikassalam".
Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko.
"Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?".
A taƙaice yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Imrana yace.
"Masha Allah, ga Lamiɗo".
"Na'am". Yace a takaice.
Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi.
A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace.
"Assalamu alaikum".
Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu.
Kana, ya ɗoro da cewa.
"Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace.
"In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah.
hakan bazai kuma faruwa ba.

Da haka sukayi sallama.

A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.

Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu.
Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum.
Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.

Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu.
Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi.

Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi.
Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba,
Cikin harshen ɓacamancin yace.
"Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za'a sauraresu a can.
Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin.
Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can.
Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab.
Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji."
Da sauri wani daga cikin su yace.
"Harda gidansu Shatu?".
Cikin izaya yace.
"Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi ɗanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al'barka a aurenmu".
Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daɗin bayaninshi sukayi baki ɗayansu.
Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki ɗayansu.
Dariya mai amo mara daɗin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ƙahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya.

Nan fa duk suka rinƙa shiga, cikin maƙerarnan suna ɗaukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje...

Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara ɗaukar ƙorarensu, suna fita garin.
Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na ɗebo ruwa, wasu na ɗebo kayan lamɓu.
Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi.

Cikinsu kuwa harda Junainah.

Tafe take da saurinta da ɗan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta,
da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanɗon zabari wanda yake cike da ƴaƴan itatuwa.
Murmushi ta ɗanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace.
"Har naji tsoro!".
ta ƙarishe mgnar tana kallonshi,
Murmushi yayi mata shima cikin son ƴarinyar yace.
"Haba dai, tsoron me kuma zakiji, tunda gani, babu abinda zai sameki muddin ina raye, zan zame miki Garkuwa".
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tare da cewa.
"Kai! Kai! Ya Junaidu, sunan Babanmufa ka kira".
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
"Au na manta ashe sunan surki nane".
Kai ta gyaɗa mishi kana tasa hannu ta amshi, nonon inabin da yake miƙa mata,
baki ta buɗe da nufin sawa a baki,
sai kuma ta tsaya tare da tura baki jin yana ce mata.
"No kada kici ba'a wonke bafa."
Sai kuma ya ajiye kondon, ya amshi inabin ya ɗan gangara, gefe kaɗan ya wonkeshi a bakin ruwan wutsiyar Kogin da yayiwa Rugar tasu ƙawanya.
Ya tahowa tana kallonshi.

Koda ya iso miƙa mata yayi,
kana ya ɗauki kondon, ganin still tanata kallonshi ne ya sashi cewa.
"Ya dai?".
Kai ta kauda tare da fara tsinkar ƴaƴan inabin tana afawa a baki tana taunawa,
Murmushi ya kumayi ganin yadda ta lumshe idonta.
A hankali tace.
"Ya Junaidu kayi kyau sosai yau, har kamar ka fini kyau".
Dariya ya ɗanyi kana yace.
"Yo dama ai na fiki kyau".
Maƙe kafaɗa tayi tare da cewa.
"Uhum a a kam".
A haka dai suna tafe suna hira.

Can cikin gida kuwa, Ummiy ce zaune bisa kujera ƴar tsuguno da buta a gabanta, alamun al'walan sallan walaha, zatayi.
Inna kuwa, da wasu maƙotansu uku Biba, Hari, da Innawuro. suna zaune bisa taburma a tsakar gidan. Suna amsar gaisuwa.

Can cikin garin kuwa su Alhamdulillah Manu dasu Siddine da dai sauran dattawan garin ne zaune a fada.
Sai yara daketa kai komo.
Chapter 54 · 0% Book details