← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 142

Sashe 123

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa jikin masallacin sai ga wani ƙaton rumfa na ƙara an lailayeshi da wani irin yashi fari ƙal-ƙal kana ga hasken wuta a cikinsa.
ko wacce da sallaya a hannunta tuni wasu kuma sunma shimfiɗa sallayunsu sunbi jam'i hakanan matan maƙota da sauran matan bayi da hadimai duk nan suke zuwa.
A jeru gaba ɗaya ananne ga kafaɗar matar sarki gata baiwa.
Babu matsayi ko milki bare isa ko ƙasaita.

Haka dai suka bi jam'i sai ƙarfe uku aka idar akayi addu'o'in kana akashafa aka kai sujjadar ƙarshi ta witirin.

Kana akayi taiya akayi sallama duk kowa ya nufi gidanshi.
Daga nan kuma aka kama aikin sahur.

Suna dawowa Hibba ta kuma kunna TV nan ta samu su tuni su sun idar. Wasu nata ɗawafi ne sai addu'o'in ake jerawa.
wanda sai kaji tsikar jikinka na tashi sabida yadda yake ratsa zuciya da jini.

Washe gari da bayan sallan isha'i da asham, yanzu Jalal da Jamil ne kaɗai ke zuwa dan Imran da Sulaiman ma dasu aka tafi.

Haka yasa yanzu duk suna zama a Dinning table suyi buɗa baki a tare.
Jalal ne ya ɗan kalli Ummi cikin cin Beans salad da Shatu tayi musu.

Hibba ce keta santi tana cewa.
"Alhamdulillah yanzu dai saura mana azumi tara ko takwas".
Murmushi sukayi, ita kuwa da sauri tace.
"Kai takwas nema in sha Allah".
Jamil kam tuni yake dariya tare da cewa.
"Tara ne".
da sauri ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi wai haka ne?".
Cikin dariya tace.
"A a ban saniba Hibbat."
Plate ɗin data zuba ferfesun jan nama ta jawo tare da fara ci tana lumshe ido tace.
"Takwas ɗin nema in Allah ya yarda".
Allah yasa haka Shatu tace.
Sai yanzu Jalal ya ɗan kallesu tare da cewa.
"Ashe dai duk kanwar jace".
Murmushi Ummi tayi kana sukaci gaba da cin abinci.

Yau dai ana zaton salla saura kwana biyar ko shida.

Da hantsi suna zaune dan yau sun tashi da wuri.
Aunty Juwairiyya ce tayi sallama tare da shigowa, Bayan Ummi ta amsa mata.
Gefen Hibba ta zauna tare da cewa.
"Alhamdulillah Ummi ɗinkunan mu sun dawo, yanzu KB ya kawosu ya shigo ko?".

"Eh ya shigo mana".

Juyawa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
"Je kice ya shigo Hibba yana nan zaki kanshi cikin baƙar mota".
To tace tare da miƙewa da sauri.

Jim kaɗan suka shigo tana gaba da jaka a hannunta yana biye da ita a baya da ƙattin jakunkuna guda biyu da wani yaro shi shima da manyan jakukkunan biyu.

A tsakiyar falon bisa carpet suka aniye jakunkunan kana, ɗaya yaron ya juya ya fita.
Shi kuwa Kabir ya zauna a ƙasa bisa carpet ɗin tare da cewa.
"Barka da hantsi Ummi".

"Barka dai Kabiru, munyi Sa'a an cika mana al'ƙawarin ko".

Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Ummi aini telane mai amana".
Hibba ce ta ɗanyi murmushi tace.
"To ka bari a yebeka mana".
Cikin dariya ɗan matashin yace.
"A a ai duniyar yanzu kawai ka yabi kanka, dan ba lallai bane wani ya yaba maka".
Dariya sukayi duka.
Kana ya fara firfito da kayayyakin.
Ko wanne da sunan maishi a jikinshi.

In ya fito dana Ummi sai ya miƙa mata, in ya fito dana Aunty Juwairiyya da yaranta sai ya miƙa mata.

Hakama na Hibba yana fitarwa yana miƙa mata.

Shatu da yanzu ta fitone, ya kalla tare da cewa.
"Barka da safiya Sayyada Shatu".
Murmushi tayi Allah ya sani in sun ce mata Sayyada dariya suke bata wato irin ita matar Al Sheykh ko.
Cikin nitsuwa da danne dariyarta tace.
"Barka dai".
Sai kuma ta ƙara so ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi waye ne shi?".

"Telan mune". Ta bata amsa a taƙaicd.
Cike da mamaki tace.
"To ina ya sanni?".
Hibba ce ta amshi zancen da cewa.
"A hoto ya sanki, da mukaje kai ɗinkunanki hotonki kawai aka nuna mishi, ya ɗinka kuma kinga komai yayi dai-dai ko".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Lallai kam yayi ƙoƙari".

Cikin dariya yace.
"Uhum ai na iya aikina sosai Sayyada".
Yanzu kam dariya sukayi duka.
Kana ya zaro kayanta a ƙalla kala takwas ya miƙa mata.
Amsa tayi tare da cewa.
"Sannu".
Hibba kuwa irga kayan tayi tare da cewa.
"Kb saura kala bibbiyu a namu nan gani basu".
Kanshi ya ɗan sosa tare da cewa.
"Wannan yarinya akwai son kalato laifin mutum to sai jibi zan kawosu ko kuma in bawa Su Jamil in sunje amsar kayansu".
Cikin murmushin Aunty Juwairiyya tace.
"Yauwa ka bawa su Jalal ɗin ma kawai".

To yace, kana ya miƙowa Ummi ƙatuwar jakukkuna guda uku tare da cewa.
"To Ummi ga na yaranki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ka kyauta min Kabiru ngd matuƙa, Allah yayi al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.

Ita kuwa Ummi Saratu ta kwaɗawa kira tana zuwa.
Ta tace.
Jeki kira duk sauran hadimai suzo duk wadannan Kabiru yazo ya gansu ranar."
Da sauri tace.
"To kana ta juya ta fita.
Ita kuwa Ummi. Inda take zaune ta nunawa Shatu.
Tare da cewa.
"Zo nan ki zauna, zasuzo, ko wacce zata gaya miki sunanta, sai ki duba sunan jikin kayan sai kibata, su duk kala ur'uku akayi musu.

Zaki basu da kuɗi dubu biyar-biyar.
Kai ta gyaɗa kana da sauri ta koma ɗalinta.
Sabida. Sai yanzu ta gano me zatayi da wannan kuɗin da ya bata kenan.
Kuɗin ta kwaso kana tazo ta zauna.

Nan suka rinƙa zuwa suna gaidata da gaya mata sunansu. Kana Hibba ta irga dubu biyar, ta ɗaura kan kala bibbiyu sun ta basu.
Ummi kuwa jakan gabanta ta buɗe tana basu takalma.
Aunty Juwairiyya kuwa jakar hijabai ta buɗe tana basu.
Suna godiya suna tafiya.
Haka sukayi tayi har kusan awa biyu kafin suka gama, duk kayan sun ƙare sai kuɗin ne ya rage.

Ganin lokacin salla yayi ne, suka tafi.

Bayan sun idar da salla ne, suka fito.
Nan a falon Shatu suka zauna.
Suna ɗan hira sabida yau aikinsu baida yawa, kuma Saratu nacan na rage musu.

A hankali wayar Ummi ta fara suwa, alamun ana kiranta.
Da sauri ta kalli Hibba tare da cewa.
"Hibba ɗauko min wayata a ɗaki".

Miƙewa tayi tare da cewa to.
Jim kaɗan ta fito da wayar da sauri ta miƙa wa Ummi wayar a kunne tare da cewa.
"Amshi Ummi kiyi mgna na amsa kiran Hamma Jabeer ne, kin sanshi baya kira biyu."
Cikin sauri da tarin jin daɗi Ummi tace.
"Assalamu alaikum".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a can saudia yana tsaye ne a gaban dreesing mirror yana gyara igiyoyin al'kyabbar jikinshi.
Tare da saƙala wayar a kunnenshi ya matseta da kafaɗarshi.
Alamun sauri yake yana shirin tafiya haramine.

Cikin sanyi yace.
"Wa alaikissalam. Barka da gida Ummi".
Fuska a sake tace.
"Barka dai Sheykh, ya ibada?".

"Alhamdulillah Ummi, yasu Jalal".

"Suna lfy, kuma basa wasa da ibada, yanzu Jamil ya dena zuwa hirama wata ƙil kuma ya ɓata da Khadijah naji yanzu wata Maryam yake kira, Jalal ne dai yake ɗan fita shima ba sosai ba".
Gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"To Alhamdulillah, eh shi Jalal ba matsala fitanshi, nasan dashi.
Ya Hibba kuma tana azumi ko batayi?".
Cikin murmushin da kallon inda Hibba take tace.
"A a Hibba ai an girma yanzu ta rage rakinma".

Ɗan karamin mataji ya ɗauka yana kontar da sajenshi yace.
"To Ummi na gaisheku, na kira Aunty Juwairiyya kam nani jikin ya Jafar da sauƙi sosai mun gaisa da Hajia Mama, har take cemin Affan ɗina zai dawo a salla".
Da sauri tace.
"Uhum Sheykh".
Ajiye kum ɗin yayi tare da cewa.
"Na'am Ummi".
Cikin sanyi tace.
"Ga Shatu".
Shiru yayi baiyi magana ba, kuma bai katse kiranba,
jin haka yasa ta kuma cewa.
"Sheykh".

"Na'am Ummi".
Ya kuma cewa.
A hankali tace.
"Ga Shatu".
Still baiyi mgn ba, hakanne yasa a hankali ta mannawa Shatu wayar a kunne ta.
Kana ta sa hannunta ta kamo hannun Hibba suka fita babban falon.

Shi kuwa Sheykh Jabeer shiru yayi tsaye gaban dreesing mirror, yana kallon gemunshi.
A hankali yake jiyo sautin sauƙar numfashin can ƙasa-ƙasa, ɗis ɗas haka yaji ƙasan zuciyarshi na harbawa.

Ita kuwa shiru tayi tanajin sautin tasbihi da yakeyi can ƙasan-ƙasan maƙoshinsa,
Lips ɗin shi na motsawa a hankali suna fidda sautin can ƙasa.
Jin shirun yayi yawane yasa a hankali ta buɗe bakinta tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Sai kuma tayi shiru ta kasa kunnen dan jiran amsarshi.
Gyara zamanta tayi tare da ƙara riƙe wayar, numfashi ta sauƙe a hankali.
Hakan yasa yaji sautin iskar.
Har ta cire tsammanin zai amsa sai kuma taji muryarshi can ƙasa yana cewa.
"Wa alaikissalam. Ashe kin iya sallama?".
Ya jefo mata tambayar a gajarce.
Cikin juya ido tace.
"Ba'a koya min da wuri bane!."
Shine mgnar da tayi niyar gaya mishi, sai kuma tayi mgnar a zuci, ta danne abun.
Sabida tana son ta nemi al'farman addu'o'in a kaba, aka yayunta da suka bace, shiyasa cikin sanyi tace.
"Eh, Ummi ta koya min".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
ita kuwa a hankali tace.
"Ina kwana".
Kanshi ya ɗan kalla a madubi tare da cewa.
"To Kifin rijiya su nan yanzu wunine".
Cikin sanyi da sassauta Muryar son isar da buƙatar ta tace.
"To ina wuni".

"Alhamdulillah".
Ya bata amsa.

Miƙewa tsaye tayi ta nufi bedroom ɗinta.
Tare da cewa.

"Ya ibada?".

"Alhamdulillah". ya kuma cewa.
"Har ya kai hannunshi zai janye wayar sai kuma ya tsaya jin tana cewa.
"Uhmm, Ayyah Yah Sheykh..".
Sai kuma tayi shiru. Cikin saurin jin an kira salla murya a nitse yace.
"Uhumm Ayyah, me ɗin?".
Chapter 123 · 0% Book details