← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 142

Sashe 82

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya gama komai na gaban Mirror kana ya nufi babban drower'nshi da sauri-sauri yakeyin komai.
Wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da taushi fari ƙal ya zaro.
Kana ya ɗan yi sama da kanshi ya kalli cikin tsep ɗin ƙarshe na drower'n inda al'kyabbanshi suke jere a kimtse tamkar shagon saidasu.
Hannu yasa ya zaro wata sabuwa dal tana cikin ledanta tana haɗe da hiramin ta da komai.
Rufe wannan wurin yayi kana, ya buɗe wani sashin inda ƙananan kayan shi ke jere, boxes and singlet ya zaro farara ƙal suma sabbi ne.
Da sauri ya rufe drower'n kana yazo ya ajiyesu bakin gadonshi.
Ba tare da ya cire jallabiyar jikinshi ba, ya saka boxes ɗinshi saida ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi da kyau ya kimtsa komai nashi yadda zaiji daɗi tafiya, kana ya zare jallabiyar ya ajiyeta bakin gadon
Singlet ɗin ya yasa, sannan ya ɗauki farar tattausar jallabiya mai dogon hannun ya saka, jallabiyar daya cire ya ɗauka ya gaban ƙaton drower'n nashi ya nufa, wani side ɗin ya buɗe nan ya saƙalata.
Kana ya dawo bakin gadon.
Ledan al'kyabbar ya farka da ƙarfi da kuma sauri sabida ganin tuni ƙarfe ɗaya da rabi tayi, yasan yanzu masallacin ya cika maƙil da mutane.
Ɗan gajeren tsaki yaja, tare da ci gaba da warware al'kyabbar.
Yana gamawa ya zurata a jikinshi, al'kyabbar baƙace, sai gefen bakinta da akayiwa kolliya da wani zare mai masifar kyau Golding color irin mai sheƙi da ɗaukar ido, hakama, kan kafaɗunsa har zuwa hannunta anja zirin irin wannan kolliyar.
da sauri ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi, kana
Ya juya ya nufi, gaban dreesing mirror da hiraminshi a hannunshi,
Yana isa ya ajiye baƙin abin, kana ya ware farin hiramin shima da kolliyar Golding color a jikinshi, ya ninkeshi kamar yadda muke ninke dankwali, bayan ya gama ne.
Ya ɗaurashi a kanshi ya dai-dai-ta zamanshi kana, ya ɗauki baƙin abin wanda shima an zagayeshi da Golding color ya sakashi a akanshi, ya fito ras tamkar a Saudia.
Allah ya sani yana masifar son wannan shigar da jin daɗinta a jikinshi babu takura babu matsi gashi ka suturtu da kyau mayu masu kallon tsiya irinsu Jazrahda Batool duk basa iya ganin komai a jikinshi ba.

Da sauri ya nufi wurin aje takalma shi wanda yake na glass ne marfin ya buɗe kana, ya ɗauki wasu takalma irin nasu na sarauta Golding color ne kuma half cover ne, zura jajayen sawunshi yayi a ciki, kana ya koma gaban mirror, wani kolba turaren OudKareem mai masifar ƙamshi mai sanyi, ya fesa a duk sashin jikinsa.
Kana yasa hannunshi ya ɗauki carbinshi. Farin galashi ɗan siriri ya manna a idonshi.
Kana ya juyo da sauri zai fita, sai kuma ya tsaya cike da mamakin ganin. Haroon tsaye ya zuba mishi ido.
Ya buɗi baki zaiyi faɗa sai kuma yayi shiru jin Haroon na cewa.
"Kada kace zakayi faɗa Lamiɗo ne yace inzo in kiraka, lokaci na tafiya fa."
Bai kulashi ba kawai yayi gaba, da sauri Haroon ya bishi tare da cewa.
"Wannan baza ƙamshi haka sai kace wurin amarya zakaje, gsky kayi kyau sosai masha Allah".
Bai kula Haroon ba sabida addu'o'in da yakeyi.
Amman duk da haka saida ya bawa Haroon amsa a zuciyarshi, yake cewa.
"Akwai wani wuri da yafi cancanta da ɗan adam yayi shiga ta tsabta da kyan shiga da ƙamshi sama da masallacin ne? Innal masajida lillafa, duk duniya da babu wurin da Allah ya keɓanta yace dakinshine sai masallatai. Nan zamu gana dashi. Domin idan mu bama ganinshi ai shi yana ganin mu".
Murmushi Haroon yayi, dan Jabeer bai san mgnar da yakeyi a zuci ta fito filiba.

A haka dai suka shiga Masallaci.

Dole yau a gaggauce yayi Kudbar jumma'a dududu 15 minutes yayi yana kudbar kan halaccin mace ta kalli mijin da yakeson aurenta, kamar dai yadda yayi al-ƙawari a wancan satin.
Daga nan aka kabbarta sallah.

A can Rugar Bani kuwa.
A hankali Shatu ta ɗago kanta ta kalli Ba'ana jin tunda suka tsaya baice mata komaiba, ganin yadda ya zuba mata idone yasata, saurin yin ƙasa da kanta,
cikin sanyi muryar tace.
"Ya Ba'ana zamu tafi rana tanayi fa!".
Wani dogon numfashi ya ja ya sauƙe da ƙarfi, kana a hankali ya ƙara matsowa kusa da ita da sauri tayi baya cikin tsoro, hannunshi ya ɗaga mata alamun karta gudu, kai ta jujjuya tare da ƙara matsawa cikin rawan murya tace.
"Ba kyau ina tsoro".
Kanshi ya jingina da jikin bishiyar gamjin da suke ƙasanta, ido a rufe yace.
"Da dai inada niyar cutar dake, da bamu kawo zuwa yau ban cutar dakeba Shatu, kadafa ki mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki kuma nake tare dake, dare da rana, kada ki mance kullum sai kinje gidanmu da dare da asuban fari kin amsowa Ummey mgninta, da har ina son cutar dake da tun wancan lokacin zan cutar dake.
To amman bani da niyar cutarki, ina sonki ne sabida Allah, da kuma gsky da zuciya ɗaya, Shatu koda zaki ƙi yarda dani a kan komai dan Allah ki yarda dani cewa ina sonki, na kuma soki a baya zan soki har gaban abadan, wlh babu ƙarya a cikin soyayyarki a zuciyata, Shatu sonki shine babban raunina a duniya.
Har yau babu wani abu dake firgitani da bani tsoro sai rasaki.
Babu wani abu na duniya daya taɓa sani zubda hawaye sai soyayyarki, dan Allah ki dena zaton dan na matso kusa dake zan cutar dake, ki amince dani in baki abinda idonki zai buɗu da gane sihiri duk ƙanƙantarshi".
A hankali take juya mishi kai cikin sanyi tace.
"Na sani Ya Ba'ana wlh na yarda da kai akan soyayyata, na sani bazaka cutar daniba, tunda baka cutar dani a bayaba, nasan kana sona, na kuma yarda da son gsky kakemin, to amman ni bana son wadannan abubuwa asirce-asircen sabida haramun ne.
A hankali ya zame jikinshi ya zauna kan jijiyan bishiyar.
Ganin haka itama tayi sauri ta zauna bisa guiwowinta ta durƙushe a ƙasa.
Cikin mamaki tace.
"Dan Allah ya Ba'ana meyasa kwanan nan duka sai kayi ta zubda hawaye a gabana, hankalina yana tashi."
Kanshi ya ɗan ɗaga ya kalli sama, a hankali yace.
"Shatu ina sonki zan kuma soki har iya numfashin na, bazan bari wani abu ya rabani da keba, in kuma akasamu wani ya zama ƙaddarar rabani dake, to shi kuwa tabbas zan rabashi da rayuwarshi, kiyi haƙuri in dai a kanki ne zan iya yin komai, na kuwa san duk duniya babu wanda yasan hanyar da za'abi a kamani ko aci galaba a kaina, sai ke ranki ke ɗaya tak ce kikasan duk wani sirrina ban saniba ko zaki iya min halacci ki sirranta min rayuwata".
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Ya Ba'ana ai rayuwa a hannun Allah take, wata ƙilma in rigaka mutuwa, kuma in dai nice in sha Allah bazan baiyana sirrinka dan a cutar da kaiba, ko ba komai kana soma kuma kace dan zaka nemo su ya Gaini ne kayi wannan tsarin gudun kada mugaye su cutar da kai, Ni na sani Ya Ba'ana waɗannan layun bazasu kareka ba, sabida ba hanyar Allah ka biba amman ni zanyi ta maka addu'a".
Ido ya zuba mata a zahiri da baɗininta gsky ta faɗi dan yaga hakan cikin ƙwayar idanunta.
A hankali ya jawo tandun duma dake rataye a kafaɗunshi, cikin sanyi yace.
"Ga ruwa kisha".
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
"Bana jin ƙishi".
Tura mata tandun yayi gabanta tare da cewa.
"Eh ba mgnin ƙishi bane, kishi dan kiji sanyi a zuciyarki naga kina kuka".
Cikin share hawayenta tace.
"Ba kai bane ka sani kukan kana ta barmin amanar sirrikanka bayan kuma shi amana rikeshi nada girma da nauyi da wuya".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Zaiyi wuya ki riƙe kenan?".
Da sauri tace.
"In sha Allah zan riƙe".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Bazaki sha bako?".
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh.
Kana ta miƙa tsaye, gaba ta ɗan yi kusa da Rafi'a, tace.
"Rafi'a mu tafi".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Rafi'a ku tsaya".
Cikin tsoronshi Rafi'a tace.
"To Ya Ba'ana".
Da sauri ya ƙara so gabansu, tare da cewa.
"Mata ɗago hannunki mu gani kinada zobene?".
Kai ta girgiza alamar a a babu.
kana ta ɗaga hannunta na dama,
Yatsarshi ya karkaɗa mata tare da cewa.
"Lalala ɗago hannun hagu mu gani".
Cikin gajiya ta ɗago hannunta, fararen tausasan zara-zaran yatsunta suka zubawa ido gaba ɗayansu.

Babu zobe ko ɗaya a yatsunta,
Murmushi yayi kana yace.
"To bari in baki zoben ziyara, koda bakya tare dani, duk lokacin da na nake kusa dake kawai zakiga zoben a yatsunki".
Da sauri ta buɗe baki da nufin cewa a a.
Kawai sai tayi shiru ganin wani irin zoben azurfa mai masifar ƙyalli da sheƙi sai ɗauke ido yakeyi.
Ta juyo zata ce mishi a a Ya cire sai kuma tayi shiru ganin ya ɓace daga gabansu.
Yatsunta tasa da nufin cire zoben da sauri ta barshi jin tamkar yatsunta zasu tsinke.
Rafi'a kam tuni tayi gaba, haka yasa itama tabi bayanta.

Suna zuwa bakin titin suka samu motar zuwa cikin Ɓadamaya.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa,
Bayan an idar da salla, kamar kullum Lamiɗo ya gaggaisa da mutane, talakawan garinshi.
Shi kuwa Jabeer dashi da tawagarsa duk sun nufi cikin gida.
Sabida Galadima nata ce mishi su tafi cikin gida su fara shirin tafiya.

Haka yasa duk suka nufi cikin gidan masarauta.
A nan babban farfajiyar suka ɗan tsaya.
Ido Jabeer ya ɗan zubawa jerin motocin da a ƙalla sun kai ashirin da biyar zuwa talatin an bisa alamu anyi manyan baƙi ne ko kuma za'ayi fita mai mahimmanci.

Cikin suka wuce a falo suka samu Umaymah, Hajia Mama, Aunty Juwairiyya, da Ummi, duk suna zaune suna ɗan hira.
Hibba kuwa tana kitchen.
Chapter 82 · 0% Book details