← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 142

Sashe 9

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yake taku, har zuwa dinnin area, a hankali ya ɗan juyo, jin an jamishi kujerar.
Jamil kenan.
Zama yayi bisa kujerar, kana, ya miƙawa Jamil jakar system ɗin nashi.
Amsa yayi ya rataya a kafaɗarshi,
sannan ya matso gab kusa da ɗan uwan nashi,
baƙin Tea ya haɗa mishi da zuma sai bredy wanda shima da zuma a jikinshi ,
wanda yasan iya abinda zai ci ya sha kenan duk da tarin. Abinci da hadiman Aunty Juwairiyya, suke kawowa dominshi ga kuma na Hadiman Hajia Mama, wanda duk Umminshi Jakadiyace ke kawosu, domin ita tana shiga har cikin falonshi ɗakin konciyarshi ne dai bata shiga, amman falo ukun nan duk tana shigarsu da kitchin da sauran ɗakunan sashin.
Suna zama babu jimawa, wayar Jamil ta fara tsuwa, da sauri ya ɗauka tare da karawa a kunne,
sai kuma yayi zuru-zuru da idanu ganin yadda Hammanshi ya tsareshi da fitinannun idanunshi masu sa hanjin cikinsu kaɗawa, cikin yin ƙasa da murya yace.
"My love Sheykh yana kusa".
Ya ƙarishe mgnar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Sheykh kauda idonshi yayi yaci gaba da zuƙan tea ɗin a hankali a hankali.
Shi kuwa Jamil cin abinci yai haninƙan kana.
Shi kuwa Sheykh ido kawai yake zubawa ƙanin nashi bai tashiba har saida yaga ɗan uwan nashi ya gama cin abincin.

Sannan suka jero suka fito falo,
A can bakin ƙofar shigowa babban falon suka samu sarkin ƙofa da kuma hadimai na jere a wurin suna hangosu duk suka rusuna har ƙasa har suna haɗa baki wurin cewa.
"Takawarka lfy ɗan Babban Yaya jikan mai martaba sarkin Nuruddeen jika ga mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Malam ɗan Malam Habibullah jinin Limamen Saudia malamai magada annabawa, jika ga ƙabilar da tafi ko wacce ƙabilar duniya d...".
Hannun shi biyu ya ɗaga musu alamar amsawa gaisuwar da sukayi mishi, da kuma dakatar dasu da kirarin da sukeyin.
Kana yaci gaba da taku Jamil na biye dashi a baya, Sarkin ƙofane yayi saurin rusunawa tare da cewa.
"Hajia Mama ta turo jakadiya a sanar maka cewa tana buƙatar ganinka".
Kanshi ya gyaɗa kana yaci gaba da tafiya,

Gefen dama ya nufa, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali hadiman dake tsaron wannan ƙofar suka fara rusunawa tare da bashi hanya da gaidashi.

Tafe suke har cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi.

Wasu ƴan yarane guda biyu duka mata,
Suna ganinsu suka ruga a guje jikin Sheykh Jabeer suka faɗa tare da cewa.
"Sabahul khair Uncle MJ".
Sunkuyowa yayi ya ɗan shafa kansu tare da cewa.
"Sabahul noor ya Habittey".
murmushi sukayi kana suka sakeshi suka isa gaban Jamil sunkuyowa yayi ya ɗauki ƙaramar bayan sun gaidashi ne babbar ta juya da gudu tana cewa.
"Ummi ga Uncle MJ".
tsayawa tayi tare da kamo hannun wata kekyawar mace matashiya yar duma-duma, tayi shiga irin ta larabawa, kamo hanunta tayi suka fito falon.

Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Barka da safiya GARKUWAN FULANI, GARKUWAN ahlin Sitti".
Fuska ya ɗan sake still bawai yayi murmushi bane, a hankali yace.
"Barka da safiya".

"Barka dai Sheykh Dr Garkuwa".

Babbar rigarshi ya ɗan gyara tare da cewa.
"Ya jikin Ya Jafar?".
Kai ta ɗan ranƙwafar tare da yin rau-rau da idanunta murya na rawa tace.
"Jiya kwana yayi baiyi bacciba, Sheykh, hankalina yana tashi, sabida duk randa baiyi bacciba, to kwana yake karatu yanayi yana kuka, kukan da yakeyi ɗin ne yake sashi zazzaɓi da ciwon kai, gashi ba cikin zuciyarsa yake karatunba ya wuni karatu a baiyane ya kwana karatu a baiyane babu bacci".
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da nufar kofar wani ɗaki.
Jamil da Juwairiyya na biye dashi a baya.

Suna shiga cikin ɗakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ƙal mai tarin tsabta wanda yake tsananin kama da Jamil duk da duk suna kama da juna amman Jalaluddin yafi kama da Jabeer, Jamil kuma yafi kama da Jafar.
Zaune yake bisa sallaya, ya jingina kanshi da jikin gado, karatun al'ƙur'ani yakeyi cikin nitsuwa da da cikar tajwid, babu ɓata ko na ɗigo, yana karatun ne hawaye na kwaranya daga kwayar idanunshi,
A hankali Sheykh Jabir yasa Hannu ya kamo hannun ɗan uwan nashi,
A hankali Ya Jafar ya buɗe idanunshi ganin mutumin da shi kaɗai ke sashi yin abu yayi ko ya hanashi ya hanune ya sashi gyara zama still yana karatu.
A tausashe Sheykh Jabir ya ɗan ranƙwafar da kanshi cikin salon tausayawa da muryar larabawa yace.
"Sadakallahul Azeeeeeem".
Jin hakane yasa wannan bawan Allah'n ya ɗago tafin hannunshi addu'o'in ya, fara karantawa kusan tsawon 3 minute sannan suka shafa a tare,
Cikin wani zafi da ƙuna Sheykh Jabeer ya taune lips ɗin shi na ƙasa hannunshin yasa ya kamo na Ya Jafar ɗin,
ba musu ya miƙar dashi,
kan gadonshi ya zaunar dashi,
A hankali ya juyo ya kalli Juwairiyya cikin sanyi yace.
"Yaci abinci kuwa?".
A hankali tace,
"Tunda asuba daya dawo masallaci na bashi yaci abinci, kuma yanzuma na bashi ya ɗan ci".
Kanshi ya rausayar kana yace.
"Maganin shi fa kin bashi".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Eh na bashi maganin yasha".
Jin hakane yasa Sheykh ya kamo hannun kekyawan Yayan nashi ya kontar dashi bisa gadon blanket yaja ya rufe mishi rabin jikinshi a hankali yace.
"Ya Jafar kayi bacci, kaji jikinka zafi".
Shiru bai kulashiba sai dai, ya lumshe idonshi.

A hankali ya juyo ya kalli Matar ɗan uwan nashi kuma ƴar kawunsu yayan Mamansu yace.
"Juwairiyya Nagode".
Hawayen dake zubo mata ta sharce tare da kamo yaranta ta ruggumesu,
Jamil kuwa tuni yaketa zubda hawaye.
Cikin rawan murya Juwairiyya tace.
"Sheykh ka dena gode min nimafa Ya Jafar ɗan uwanane kuma mijinane, uban ƴaƴana, to in ban kula dashiba da waye zan kula a duniya?."
Kanshi ya kauda kana ya juya ya nufi hanyar fita a ranshi yanajin ko sai yaushe manyan burukan rayuwar da fatanshi da addu'o'in shi zasu ƙarɓu yana ganin daraja da girman Juwairiyya domin tayi musu tsantsar halacci ta zauna da ɗan uwanshi a matsayin majanuni, a haka suke tafiya yana zancen zuciya.
Jamil na biye dashi a baya.

A haka suka fito, suna tafe hadimansu na biye dasu a baya.
A hankali ya ɗan juyo ya kalli Jamil da yasan yanada rauni dan Jamil yanada tausayin ɗan uwanshi duk da yanada shekiyanci amman yanada rauni a kansu abu kaɗan ke sashi kuka,
Sashin dake tsakanin sashin su Jamil dana Ya Jafar suka wuce wanda nanne sashin Sheykh, sashin su Jamil ɗin suka shiga.
Kai tsaye suka wuce har cikin bedroom.
Tsaye suka sameshi yana taje suman kanshi mai yawa ga wondo iya ƙugu duk rabin boxes ɗinshi a woje ga wondon da rabin jiki duk woje waishi kirezi ko? da alamun fita zaiyi.
"Meya hanaka zuwa masallacin jumma'a da wuri jiya?
Waɗannan kolaben barasar na waye ne?".
Sheykh ne ya jero mishi tambaya biyu a lokaci guda,
A hankali Jalal ya juyo cikin shakku da shayi da kwarjin Hamma nasu ke sasu ji yace.
"Mamace ta aikeni, jiya shiyasa na dawo a ƙurerren lokaci.
Kolaben barasar kuma nasu Ashid ne, na kwace ne lokacin da suka saya, dan karsu sha".
Kanshi ya gyaɗa dan ya gamsu ya kuma yarda dan yasan duk rintsi ƙanennshi basa mishi ƙarya.
Cikin faɗa yace.
"Ka kula da salla, ka tsaida ita kan lokacinta, kasan irin abokan da zakayi yawo dasu, ka tabbatar kaikeyi nasara akan juya halaiyarsu daga mummuna i zuwa kekkyawa. Shiyasa ban hanaka mu'amala da suba, domin manzon Allah yace.
"Mutun ɗaya ya shiryu ta dalilinka, tarin ladan yafi a baka tarin jajayen raƙumi.
Kada ka bari suyi nasarar juya rayuwarka daga kekkyawan i zuwa mummunan.

Kanshi ya gyaɗa cikin ladabi yace.
"In sha Allah".
Daga nan suka juya baki ɗayansu,
Kai tsaye sashin Hajia Mama suka wuce.
Inda hadimanta sukayi musu iso,
Har cikin bedroom ɗinta suka shiga,
A bakin gado suka sameta, zaune, yayinda baiyawarta Mansura keyi mata tausa.
Murmushi tayi tare da kallonsu yadda suke a jere, koda maƙiyinsu ne sai sun burgeshi sun bashi sha'awa yayi fatan inama da ƴaƴansa ne.
Kan dantsatsetsen shimfiɗar kilisa mai kyau da zanen tsuntsuwar ɗawisu, suka zauna,
Cikin kula tace.
"GARKUWAN FULANI, Jamil, Jalal, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin, Sheykh da Jamil suka amsa,
Jalal kuwa shiru yayi,
Ita kuwa Hajia Mama murmushi tayi tare da cewa.
"Babanmu mai Al'farma Sarkin Musulmai Jalaluddin meya farune naga fuskarka a haɗe?".
Kanshi ya girgiza alamar.
"Babu".
Shi kuwa Sheykh ido kawai ya zuba kan wayarshi,
Jamil ne ya ɗan gyara zama, tare da cewa.
"Mama Abba fa".
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
"Abinda yasani nemanku kenan, Abbanku ya tafi Abuja jiya da dare, yanzu kuma Gimbiya Samira zatabi bayanshi".
Shiru Sheykh yayi a ranshi yake jinjina al'amarin mahaifinsu.
Babusu a cikin dukkan sabgogin rayuwarsa komai nashi saidai suji a bakin Hajia Mama ko kuma a jaridu ko gidajen Radio ceɗi meɗinshi da amaryarshi Gimbiya Samira ƴar sarkin Nokan ce ita kuwa mijinta shine rayuwarta babu ruwanta da sabgar kowa.
Sam Abba bai shaƙu dasuba da wuya ka ganshi zaune dasu yana hira dasu kamar uba da ƴaƴan shi.
Saɓanin Maimartaba ko meye zaiyi Sheykh zai sani shine mutumin da yake shawara dashi akan duk abinda ya shafi addini.
Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa.
"Allah ya dawo dashi lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu,
Cikin kula yace.
"Hajia Mama Affan fa sai yaushe zai dawo?."

"Next month?". Ta bashi amsa a gajarce.

A gogon hannunshi ya ɗan kalla kana a hankali ya miƙe tare da cewa.
"Zan wuce Hospital shugaban ɗaliban makarantar ya kirani cewa sunada mara lafiyar da take buƙatar kulawar gaggawa".

Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
"A dawo lfy".
Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Daga nan kai tsaye FADA suka nufa.
Inda sarkin fada yayi musu iso zuwa ga Maimartaba kakansu.

Suna shiga suka samu fada na cike da dattawa karsu Waziri, Matawalle, Galadima, Wambai, Ɗan isa, ɗanm' buram, sairkin Dogarai sarkin Gida, da kuma Duba gari, kana, sai kuma hadiman dake tsaye bayan sarki sunayi mishi fifitar sarauta da maficin fiffigen Ɗawisu.
Chapter 9 · 0% Book details