← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 142

Sashe 86

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai.
Tuni mutane sun cika sunyi maƙil ko ina ya cika da bani adam.
Kiɗe-kiɗen da bushe-bushen sarewa da al'gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.

Ba'ana da tun jiya yake cikin ɗakin dodon tsafinsu Bonon.
Jin al'gaita Shaɗi ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna.
Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga ɗakin sirri dan a dafashi da kyau.

Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.

Lamiɗo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ƙasaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida Lamiɗo da tawagarsa.
Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba ɗayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi.
Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa.
Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi.
Allah ya sani baya son ganin ko ƙasar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer ɗin tare da cewa.
"Yaro ya ƙarfin jikin naka".
Ba tare daya ɗago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala.
A hankali yace.
"Alhamdulillah".
Gaba ɗayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ƙoshin lfy.
Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako ɗaya tak.
Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace.
"Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi".
Idonshi ya ɗan ɗago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace.
"Amin ya Allah".
Bukar ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
"Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka".
A daƙile Jabeer yace.
"Inuwa tace".
Galadima ne ya ɗan kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna.
Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su Arɗo bani suka koma wurin zamansu.
Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba'ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi.
Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron.
Juyi ya farayi da ihu da ɗaga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji.
"Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ƙasar nan, zan koma ƙasar Cameroon nida ƙasar nan sai dai ziyara,
Dan ba'a yin jarumai biyu a gari ɗaya kamar yadda ba'a sarakuna biyu a gari ɗaya."
Wani irin ihu da shewa gaba ɗaya mutanen suka ruɗe dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba'ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi.

Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace.
"Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira."
Kai ya gyaɗa mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al'farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips ɗinshi ke ɗan motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi.
Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska Lamiɗo yace.
"Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu."
Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buɗe idonshi.
Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye.
Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer.
Muryar Lamiɗo yaji yana kuma cewa.
"Jabeer DAN ALLAH KA TASHI".
Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali.
Cikin jin daɗi Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron.
A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu.
Al'kyabbar shi ya ɗan gyara mahaɗinta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaɗa duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al'gaita kana da kaɗe-kaɗen.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al'kyabbar shi.
Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace.
"Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raɗaɗin marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaɗi da kashedi na ba!".
Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya,
cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa.
"Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za'a dakaba".
Ba'ana kuwa wani murmushi jin daɗi yayi sabida yasan yin duka da ƙatuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ƙarfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba.
(Allah sarki Ba'ana bai san zafin hannun Sheykh bane.
Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu.
Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa.
Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi.
Hannun yasa ya amshi bulalar.
Kana ya gyara al'kyabbar jikinshi.
Shi kuwa ba'ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buɗa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙugunshi, ya buɗa ƙwanjinshi da kyau.

Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin.
Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane.
Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi.
Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani.
Yasani in sha Allah daga kanshi baza'a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan ɓarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ƴan uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin ɗaya fushinsa na ranar ya dawo.
Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaɗan, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana ɗagata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya ɗaura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba'ana ita a tsakiyar bayanshi.

Gaba ɗaya hankali da idon kowa bisa fuskar ba'ana yake.
Shi kuwa ba'ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.

Arɗo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba'ana babu ƙaƙƙautawa.

Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiɗa mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah.
Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras.
A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaɗunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ƙebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin.
Fargabane ya fara dukan ƙirazan dattawan Fulani, yayinda ƙabilar ɓachama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba'ana suna ƙara mishi ƙarsashi.
Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi.
Cikin sauri Arɗo Bani ya juyo ya kalli Lamiɗo dake zaune.
Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin Shaɗi kuwa murmushi ma yakeyi.
Chapter 86 · 0% Book details