← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 142

Sashe 30

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali wayar Sheykh Jabeer ta fara bada wani sauti mai masifar sanyi da daɗin sauraro, sautin gwauraye yake da kukan sassanyan tsuntsaye.
da sauri ya zaro wayar a al'jihun tattausan al'kyabbar tasa.
Ganin sunan Maimartaba Nuruddeen ne, ya sashi sakin wata sassanyan ajiyan, cikin ladab ya kalli Sitti, kana a hankali ya kalli Sheykh Abdulkareem, cikin sanyi da nitsuwa yace.
"Mai martaba Nuruddee ke kirana, bisa alamu da babbar mgna domin baya kirana haka banza".
Murmushi dottijon yayi, domin ya fahimci hanyar fecewa, Sheykh yake nema, hakan yasa ya mishi izinin tafiya.
Cikin sauri Sitti ta yunƙuro da niyar yin mgna, sai kuma tayi shiru, sabida nuni da tayi shirun da mahaifinta yayi mata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya yunƙara, ya miƙe ya nufi hanyar fita bayan yayi musu, su huta gajiya.

Kai tsaye Side ɗinsu ya wuce.
Yana shiga kai tsaye bedroom ya wuce, gyara al'kyabbar jikinshi yayi kana, ya zauna bisa wata tattausar doguwar kujera.

A nan ƙasar kuma, cikin faɗar masarautar maiartaba Sarki Nuruddeen.

Bayan Jamil ya fita, wurin da yayiwa su Bappa Masauki,
kai tsaye, sashin kakanin nashi ya nufa.
Bayan an mishi isone, ya shiga, ya gaisa da kakan nashi kana ya ƙara da cewa.
"Mai martaba, akwai baƙi ma buƙatar kulawarka, suna tsumayinka".
Murmushi mai cike da kamala farin dottijon bafulatanin yayi, cikin ratsin sarauta yace.
"Yau ka zama, sarkin fada kenan, kaine mai yiwa baƙi iso ko?, ko dai matane baƙin dan nasan ta nan kafi ƙarfi". Ya ƙarishe mgnar da yanayin tuhuma.

Kanshi ya ɗan shafa, kana a hankali ya girgiza kansa tare da cewa.
"A,a mazane dattawan Fulanin dajine,".
Ido ya ɗan zuba mishi kana yace.
"Kaje kace a kula dasu, gani nan zuwa yanzu".
Kanshi ya ɗan rusunar tare da cewa.
"Nasa an basu dukkan kulawar da zasu, buƙata, zuwa yanzu sunfi buƙatar ganinka fiye da komai".
Kai ya ɗan jinjina alamar to.
Yunƙurawa yayi tare da cewa.
"A fito lfy".

"Allah yasa".

"Amin Amin". Yace kana ya fita.

Shi kuwa Sarkin ya fara shirin, fitowa fada.

A can sashin Sheykh Jalal ne, zaune da Ya Jafar, Aunty Juwairiyya na gefenshi.
karatu yakeyi kamar koda yaushe, tun jiya yaƙi barin sashin Sheykh, koda aka kira Sheykh Jabeer video call, ya ganshi sai yayi ta kuka.
Wannan abun shiya ƙara tada hankali Sheykh Jabeer.

Yana yawan, bin Jalal, wanda mutane ke zaton ko dan tsananin kamannin da Jalaluddin keyi da Sheykh Jabeer ɗinne yasa, yake ganin kamar shine, to sai dai sam Jalal baya iya mu'amalantar Babban yayan nasu, kamar yadda Sheykh keyi har yake sama mishi nitsuwa, sai dai shima yana iya yinshi.

Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya cika mata idanu. A duniya bata da babbar matsala sama da larurar mijinta.
Ita kuwa Mama, gefenshi ta zauna, cikin sanyi ta kalli, Jalal da fuskarshi ke murtuƙe kamar ko yaushe,
cikin baiyanar damuwa tace.
"Ya za'ayi ya samu gamsuwa da kulawarka, a yadda kake haɗe fuskarnan tamkar wanda aka sanarwar labarin mutuwar uwarshi, ba haka Sheykh ke mushiba, yana kula dashi, da tausayawa da sakin fuska tunda yasan larurar haukace dashi, amman kai ko yaushe kana nan kamar boss".
Sai ta kuma kalli Jakadiyarsu Kana, ta kalli Jamil dake waya da alamun da budurwarshi yake mgna, hararanshi tayi tare da cewa.
"A haka kuke samawa kanku tabon nunawa a rayuwarku, shi wannan ya zama, mahaukaci, shi Jalal ya zama tantiri ɗan shaye-shaye, kai baka da aiki sai bin matan banza. Kuna samin ciwo a raina, shima kanshi Sheykh duniya ta zata fara zargin cewa mazinacine shiyasa yaƙi yin aure ya zauna, sinƙitin fakitin. Shi kuwa Affan in banda shashanci da tarin ƙuruciya babu abinda yasa a gaba.
Ya kukeso inyi, ya kuke son mahaifinku yayi? Yana da yaya maza har ku shida, amman ku biyar manyan duk kun zama, ababe masu taɓo a idon duniya, ya za'ayi yayi mararin gadar mulki a hannun mahaifinshi, tunda yasan shi bashi da masu gadarsa, a kusa,ku duba, Imran da yake uwarsa ta tambaɗaku, ta nesan taku da mahaifinku, sai ta kusanta ɗanta da mahaifin naku.
Shiyasa mahaifinku keta ƙin amsar sarautar har sai randa Imran ya mallaki hankalinshi, ku kuwa kun zama ababen kyarata. Yaya zanyi da raina.
Shiru sukayi gaba ɗayansu,
Shi kuwa Ya Jafar sai ƙara sautin karatun yayi. Yanayi yana zubda hawaye.

Shi kuwa Jalal, shiru yayi yana riƙe da hannun Jafar ɗin.
Jamil kuwa katse kiran yayi.
Affan kuma wanda dama tare suka shigo, fuska ya ɗan kele, cikin irin matsayin da ƴan auta kedashi a wurin iyayensu yace.
"Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaɗamu, ya za'ayi keda kanki ki rinƙa suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamɓaɗe mukeba,
Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki ɗan uwanmu nefa".
Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace.
"Ɗan uba dai ba ɗan uwaba".
A tare suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya.

A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa ɗinne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu.
Shiru mutanen fadar sukayi baki ɗayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ƙare zancensa da cewa.
"Babban tashin hankalinmu, kullum ɗauki ɗaɗɗayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu.
Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu."

Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa.
Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin.
Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi.
Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace.
"A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa.
Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!".
Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa.
"An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki."
Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu.

Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu,
cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace.
"Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa,
Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake."
Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu.
Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe,
Da sauri ya rusana ya koma gefen.
Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa.
"Imrana, kiramin Sheykh Jabeer."
Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi.
Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu.

Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi.

Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa.
"Wata ƙil baya kusa da wayar."
Kai ya jinjina mishi tare da cewa.
"A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira".
Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa.
Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala.

Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.

Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.

Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa,
cikin tarin girmamawa yace.
"Barka da hantsi, Hamma Jabeer".
A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru.
Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace.
"Afwan Sheykh Assalamu alaikum ".
Murya can ƙasa yace.
"Wa alaikassalam".
Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko.
"Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?".
A taƙaice yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Imrana yace.
"Masha Allah, ga Lamiɗo".
"Na'am". Yace a takaice.
Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi.
A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace.
"Assalamu alaikum".
Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu.
Kana, ya ɗoro da cewa.
"Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace.
"In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah.
hakan bazai kuma faruwa ba.

Da haka sukayi sallama.

A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.

Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu.
Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum.
Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.
Chapter 30 · 0% Book details