← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 142

Sashe 105

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bappa da yanzu ya iso daga rakiyar da yayiwa Rafi'a ne, yayi murmushi tare da cewa.
"Bani wayar nan".
A hankali cikin girmamawa ta miƙa mishi wayar.
Shi kuwa amsa yayi tare da karawa a kunne.
jin muryar bappa yanayi mata sallama ne yasata jin sabbin hawaye masu masifar ɗumi, sabida tausayinshi.
Duk da tsufanshi mugayen ƙabilar ɓachama basu barshiba, sun kashe mishi babban ɗan shi.
Kana sun tafi da uku, sun barshi cikin zulumin suna raye ne ko sun mutu? A ina suke? Me akayi musu? Me sukeyi? Sannan itama data rage anyi mata wani irin bahagon auren da yafi kama da na mulkin mallaka.
Muryarsace ta katse mata mgnar zuci da takeyi da cewa.
"Shatu kina Lfy ko?".
Murya na rawa tace.
"Lfy lau Bappa, amman bana jin daɗin gidan, ina kewarku, ya jikin Ummey na? Ya lbrinsu su Ya Gaini an samu wani lbrin ko har yanzu shiru? Ya Ba'ana bai muku komai bako? Ya tafi ne ko yana nan?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Shatu wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki'.
Tana kuka tace.
"Duka".
Cikin hikima da jinƙai irin na iyaye yace.
"To sai kinyi shiru kin dena kuka".
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Na bari".
Taku biyu yayi zuwa uku kana yace mata.
"Ba'ana bai mana komaiba! Ya gudu ya bar ƙasar ma baki ɗaya! Jikin Ummey ki da sauƙi sosai! Su ya Giɗi munata addu'a in Sha Allah, in Allah ya yarda zasu baiyana garemu da izinin ubangiji.
Kafuran nan kuma mun rigada mun karya ƙarfi su yanzu bazasu sake samun damar cutar da muba, in Sha Allah munfi ƙarfi su."
Sai kuma ya ɗan tsagaita jin, tana murmushi mai ɗan sauti alamun jin daɗi,
a hankali yaci gaba da cewa.
"Rafi'a tazo, nayi mata bayanin komai, kuma in ta dawo zata zo, in an barta zata shigo".
Da sauri tace.
"Zan gayawa Ummi ta sanarwa sarkin ƙofa in tazo a barta ta shigo".
Cikin danne ainihin tarin ƙunar watsewar gidanshi yace.
"Yauwa to haka zakiyi.
Sannan in sunƙi yarda kada ki damu.
Umarnine gareki, kibi dukkan umarnin mijinki, kiyi mishi biyayya a cikin dukkan lamuranshi nasan bazai saki mugun abuba, kada ki saɓawa umarninshi.
Kada kiyi komai saida amincewarsa.
Ki kasance mai kula da lamuran rayuwarsa kada ki bar wani abun cutarwa tare dashi.
Yanzu shine gatanki. Shine madadin Giɗi, Ganin, Seyo, Lado, ƙannenshi mata ki kallesu tamkar Junainah, mahaifiyarshi ki kalleta kamar Ummeynki, yan uwan mahaifiyarshi ki kallesu kamar yadda kike kallon innarku, yanzu sune ƴan uwanki.
Domin naki basa kusa Ki zama GARKUWAR sa".
Shiru yayi jin kuka na son kubce mishi.
Ita kuwa tuni hawaye na kwaranya daga cikin manyan idanunta.
Cikin sanyi yace.
"Gobe zamu tafi, lardinmu, zamu koma can na wani lokaci".
Wani irin tsananin razana da tsoro ta zaro ido tare da cewa.
"Bappa zaku tafi Kardi kuma!? Ni ku barni a nan ba kowa nawa!?".
Cikin sanyi yace.
"Zamu dawo Shatu. Donke zamu dawo.
Dole muje, in sanarwa iyayen innarku abinda ya faru da ita da yaranta.
In kuma gayawa yan uwana halin da nake ciki a kan ɓatan yayunki, bayan salla zamu dawo. Can zamuyi azumi. Bakiga yanzu a nan ko tinkiya ba'a bar manaba".
Cikin gamsuwa da zancen Bappa ta ɗan danne shessheƙan kuka tare da cewa.
"Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy. Amman Bappa ku barmin Junainah mana, a kawo min ita mana in samu iƴar uwa kusa dani".
Cikin tausasamata zuciya yace.
"Kada ki damu, su nan bazasu barki da maraiciba.
Sai mun dawo zan kawo miki Junainah da kaina".
Kit kiran ya ƙatse sabida kuɗin sun ƙare.
Hibba da tun ɗazu ta shigo tana gefenta ne,
ta ɗan kalleta cikin sanyi tace.
"Aunty Shatu, meyasa kikace bakya jin daɗin zama a gidan nan? Munayi miki wani abune?".
Cikin zubda hawaye ta jujjuya mata kai.
Hibba bazata fahimci halin da take ciki ba, bazata gane matsalar rayuwarta ba.
Ita kuwa Hibba cikin sanyi tace.
"Aunty Shatu nima ƙanwarki ce, duk abinda zakisa Junainah tayi miki nima kisani zan miki kinji ko".
Cikin share hawayenta tace.
"To Hibba ngd".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yauwa kuma Umaymah ta aika Ya Jamil ya sayo miki sabuwar waya iPhone".
Cikin sanyi da son tsaida hawayenta tace.
"Ngd".

Haka yammacin ranar ta yishi a bedroom ɗin ta.
Sai Hibba dake ɗebe mata kewa ne.
Da Umaymah taga basu fito bane itama taje.

Washe Gari yau Jumma'a, kuma yaune ta cika sati ɗaya cib a gida.
Kuma tunda yazo gidan sau uku taga Sheykh Jabeer, tun randa ya wucesu, suna batun abinci bata sake ganinshi ba, koda a gilme ne.
Yanzu ta saba da Umaymah Sosai hakama Ummi
Ita da Hibba kuwa shaƙuwa ta fara ƙarfi a tsakaninsu.
Tana jin Hibba kamar Junainah.
Jamil da Jalal Haroon suna ɗan zama asha hira dasu.
Yau ne kuma Haroon zai tafi Leddi julɓe, sabida yayi masifar kewan Jannart ɗin shi, wacce taƙe ƙanwace ga Aunty Juwairiyya, kuma ƙawance ga Ibrahim.

Ƙarfe ɗaya dai-dai, Sheykh Jabeer, ne tsaye gaban dreesing mirror yana fesa turare bayan ya gama shirin jummarsa tsab.
Yau shigar baƙar Al'kebbar da farar jallabiya yayi.
Yayi wani irin kyau mai cike da sheƙi.
Kusan a tare suka jero da Haroon wanda yake cikin shigar ƙananan kaya.

Su kuwa suna falon suna, zaune.

Jamil da Jalal da Ya Jafar kuwa suna tsaye alamun fitowar Sheykh suke jira.

A hankali Shatu ta ɗan ɗago kanta jin wani irin masifeffen ƙamshi mai daɗin shaƙa.

Da sauri ta janye ƙwayar idanunta,
Sabida idonta da suka faɗa cikin ƙwayar idanunshi.
Wanda shi kuwa Jalal yake kallo ganin wani shegen wondo wai shi crezi ne ko meye ne oho, duk yana ɓuɓɓule har kana iya ganin farar fatar cinyarsa.
ga saɓulellen wonɗo ga kafurin aski.
fuskarshi ya tsuke tare da jan gajeren tsaki wanda shiyasa Jalal juyawa, ya nufi hanyar fita yana cewa.
"To Ni banifa da manyan kayan nan, yanzu bari inje in duba ko inada jallabiya sai in saka a kai zan biyoku daga baya."
Da ido suka bishi. Haroon da Jamil kuwa murmushi sukayi.
A haka suka fita suka tafi. Har sunje bakin ƙofar fita ba tare da ya juyoba yace.
"Umaymah ku tashi lokacin salla yayi". Ya ƙarishe mgnar suna fita
To tace.

Kana suma su Ummi suka nufi ɗakinsu.
Aunty Juwairiyya kuma ta wuce Side ɗinta.

Ita kuwa Shatu da Hibba suka tafi ɗalinta.
Hibba ce ta fara shiga tayi al'wala.
Sannan itama Shatu ta shiga.

Tana fitowa daga bathroom ɗin tayi wani irin....!

Uhummmmmm tuni mun gama shimfiɗan lbrin GARKUWA yanzu dai muna cikene dumu-dumu .

By
*GARKUWAR FULANI*
Ta kamo hannun Jalal da ya miƙe tsaye da nufin yarfa mata mari.

Cikin wani irin masifeffen tsana, Hajia Mama takalli Shatu.
Kana da sauri ta juya ta nufi hanyar fita.
Sheykh da tunda ya fito yake tsaye tamkar an dashi ne,
yayi saurin bin bayanta tare da cewa.
"Hajia Mama! Mama!! Mama dan Allah kiyi haƙuri, kizo karki fita Please Mama karki fita, babu wata halitta da zata miki iyaka da sashina, in kin tafi kenan kinbi umarninta."
Cikin tashin hankali yake waɗannan kalaman yana mai binta a baya.

Jamil kuwa miƙewa tsaye yayi ya zubawa Shatu idanu tamkar zasu faɗo ƙasa.

Aunty Juwairiyya kuwa, wani irin kallo mai sarƙafe da ma'anoni takeyiwa Shatu.

Ya Jafar kuwa wani irin kallo mai surke da murmushin jin daɗi yakeyiwa Aysha.

Ummi kuwa tuni jikinta rawa yakeyi da abinda ya faru.

Imran, Ya Hashim, kuwa ido suka zubawa sarautar Allah.
Hibba kuwa kuka takeyi tare da riƙo hannun Shatu tana ja tare da cewa.
"Aunty Aysha ki bari, Mamace fa! Kizo mu tafi ɗaki".
Tanayi tana jan hannun Shatu da ƙarfin tsiya, dole yasa Shatu ta bita a baya.

Umaymah kuwa wani irin tashin hankali da tafasan zuciyane ya dirar mata lokaci ɗaya.
Da wani irin kallo tabi bayan Aysha dashi.

Duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali.
Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Sun daɗe a haka, da kyar dai
Cikin wani irin tafasan zuciya ta saki hannun Jalal.
Tare da komawa ta zauna.
Da yatsa ta nuna musu hanyar fita daga falon. Murya a hargitse tace.
"Kul kada ka sake tunanin gigin ɗaga kayi nufin taɓa lfyar Aysha, bana so kul.
Maza Ku tafi masallaci".
Sai lokacin suka jiyo sautin muryar Jabeer yana Hudba.
Wanda daga jin muryarsa kasan yana cikin baƙin ciki.

Wani irin numfarfashi Jalal ya sabke tare da yin koffa kana ya juya ya nufi hanyar fita shi matsalarsa meyasa Umaymah na mgn Aysha na mgn Umaymah na hanata abu tanayi.
Haka su Jamil da su Imran da ya Hashim da Ya Jafar suka fita.

Ita kuwa Aunty Juwairiyya wani irin tashi tayi ta fita ta nufi Side ɗin ta.

Ya zama Ummi da Umaymah ne kaɗai suka rage a falon.

Shiru sukayi tamkar ruwa ya cin yesu.
"Uhuhhmmmm". Umaymah ta fesar da wani zazzafan numfashi mai ɗumi.
Hakama Ummi tagwayen numfarfashi masu nauyi ta sauƙe.
Kallon juna sukayi, cikin shiga al'hini wannan al'amari cikin tsoro da karaya Umaymah tace.
"Toh wai meye hakan? Meke faruwa ne? Me hakan yake nufi? Kaina ya kulle. Wani zagon kasan kuma aka shirya tsakanin Shatu da Hajia Mama ko dai dama da zagon ƙasan ne?.
Wake saƙa gadar zare, muna na bi ta kai ya rubta da mu".
Wani numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.
"Tabbas akwai babban al'amarin dake faruwa wanda bamu saniba Ni tsorona ɗaya kada a juya ƙoƙwalwar yar mutane."

Shiru sukayi cikin ta'ajjudin al'amarin. A hankali suka miƙe a tare suka nufi ɗakinsu jin har an idar da sallan a masallacin.
Al'wala sukayi kana sukayi salla daga bisani suka, fara tattauna wani abu na sirrin masarautar Joɗa.

A cikin ɗakin Shatu kuwa, tunda suka shiga ta kwanta bisa gado.
Bacci tayi bacci, hakama Hibba.
Sai ƙarfe uku dai-dai Shatu ta tashi.
Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta miƙe ta shiga bathroom.
Wonka tayi tare da al'wala.
Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah.

Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan.
Chapter 105 · 0% Book details