← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 142

Sashe 10

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farin dattijo bafulatani, mai cikar haiba.
Yana cikin manyan kaya na sarakai, wanda al'kyabbarsa kaɗai ta kai kuɗin mallakar wani gidan,
A gabanshi suka zauna gaba ɗayansu uku,
A hankali Sheykh yasa tafin hannunshi kan rumfar sawun kakan nashi da suke kan wani tim-tim mai girma da masifar taushi.
taɓa sawun kakan nashi yayi tare da cewa.
"Barka da hantsi Maimartaba, ya sawun naka?".
Duk maganar nan da yayita a hankali yake yinta ko Jamil da Jalal dake gefenshi basujiba.
Shi kuwa Maimartaba hannunshi ya ɗaura kan tsakiyar kan Sheykh wanda tun kafin ya zauna ya tura hulanshi ya koma baya, dafa tsakiyar kanshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi,
dan su sai yanzu suka haɗu dashi tunda gari ya waye,
Tsaɓanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma ɗakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taɓawa.

Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi.

Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa.
Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta,
Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al'kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita.

Cikin tarin so da ƙaunar Jazlaan ɗin nata take kallon su,
Murmushi tayi tare da cewa.
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam".

Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata.
Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa.
"Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa'azin ka da kayi kan falala da ni'imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure.
Sai najima wa'azin kamar da kanka kakeyi.
Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar Joɗa".
Jalal ne ya miƙe tare da cewa.
"Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi".
Haratanshi tayi tare da cewa.
"Tafi daga nan mai ƙugu kamar buzuzu hegiyar masifa".
Hararanta yayi kana ya juya ya fita.
Ita kuwa Gimbiya Aminatu.
Jamil ta kalla wanda shima ya miƙe yabi bayan Jalal.

Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa.
"Maganinki ya kare koda saura?."
Da sauri tace.
"Yauwa magani ya ƙare a kawo min wani".
To yace kana ya mike ya fita.

Daga bakin harabar sashin kakar tasu,
Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau.
Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi.

Da sauri Ado drevernshi ya buɗe mushi ƙofar wata mota mai ɗan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma'a-jumma'a yake hawanta,
wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai sheƙi takeyi,
yana shiga sauran fadawanshi suka yi yunƙurin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya.

Da sauri ya ɗaga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace.
"Kkku ba bari ba'a bukatar rakiya".
Da sauri suka ɗan rusuna tare da haɗa baki wurin cewa.
"Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh".
Amin Amin yace a taƙaice kana ya shiga motar, sarkin ƙofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi.

Suna fita kai tsaye Babbar jami'ar dake cikin babban birnin Ɓadamaya suka nufa.

A can cikin makarantar kuwa,
Kasan cewar duk ɗaliban jami'ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba ɗaya harabar asibitin dake cikin jama'ar cika da taron tsala-tsalan ƴan mata ƴaƴan manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ƙwarewarsa.

A hankali wasu ƴan mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka ɗayar bata da lfy dan ɗayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya.

Cikin tausayawa ɗayar ta kalli wacce ta riƙewa hannun a hankali tace.
"Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh ɗin kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ƙa'idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaɗan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba.
Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa,
kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun".

A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara niƙab ɗin dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta
wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda yaƙinin Ba'ana ne dan mutunne mai masifar baƙin kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaɗi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu.
Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace.
"Rafi'a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata ɓalle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ƙaraso".
Jin haka yasa Rafi'a cewa.
"Zaki iya tahowa ke ɗaya?".
Kanta ta gyaɗa mata a hankali.
Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital ɗin da sauri.

Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta cikin farfajiyar.
Bayan Ado ya dai-dai ta parking ne a cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Jabeer a samanta.
Ado ne ya fito da sauri ya buɗewa, Sheykh marfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito.
Cikin nitsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin.
Kasan cewar ta gabas ya fito Aysha kuwa ta yamma ta fito sai ya zama suna fuskantar juna.
Yayinda sai sun haɗu wuri ɗaya zasuyi kwana sun fuskanci kudu inda nanne mashigar cikin asibitin.

A hankali suke takowa suna fuskantar juna.
Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku.
Ita kuwa Aysha, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da mararta keyi.
Kanta a sunkuye take tafiya, hakan yasa bata san da mutunba a gabanta.

Da sauri Sheykh ya tsaya sabida wani irin bugawa da ƙirjinsa ya fara. Ganin ta tunkaroshi gadan-gadan, kuma daga yanayin tafiyarta tamkar zata faɗi ƙasa.
Ganin tayi wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta da takeji tamkar caccakarsa akeyi da allura.

Gefe ya ɗan tsaya yana kallon ikon Allah, ita kuwa GARKUWA rumtse idanunta tayi da karfi, wata fitinenniyar zuface ke tsastsafowa tako ina,
a hankali ta fara buɗe idanunta jin kartan da mararta keyi ɗin yana ɗan lafawa,
a hankali ta zubawa kyawawan sawunshi idanu, cikin sauri ta ɗago kanta, ganinta tsaye gab kusa da namijin da bata saniba ne yasata ja da baya da sauri tare da miƙe tsawonta cikin firgici murya na ɗan rawa tace.
"I'm very sorry".
Bai kulata ba, sai kauda kanshi da yayi gefe.
Ita kuwa Garkuwa cikin sanyi tace.
"Dan Allah kayi haƙuri".
Kai ya ɗan gyaɗa mata alamar Uhumm.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
"Uhumm kaima Doctor Sheykh ɗin kazo ganin ne?".
Da mamaki ya ɗan kalleta da gefen idonshi, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan jin muryarta a sanyaye taci gaba da cewa.
"Muyi sauri mu shiga ance yanada shegiyar ƙasaita da isa, wai ko sarkine yake dubawa in dai lokacin salla yayi tashi yakeyi ya fita".
Cikin tarin mmki ya ɗan waro kyawan idanunshi tare da cewa.
"Umh".
Ita kuwa Garkuwa, hannu tasa ta matse mararta tare da cewa.
"Muyi sauri mu shiga, kaga kuwa kayi sa'a kayi shigar mutunci dan ance shi baya son ganin musulmi da lalatacciyar shiga, ancema in mace tayi shigar banza baya dubata, kaji shishshigin mutunfa ko meye ruwansa da rayuwar wasu ai kowa yayi mai kyau dan kansa ko?".
Rolling Ball eyes nashi yayi tare da gyaɗa mata kanshi.
Kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya.
Ita kuwa Garkuwa cikin yin ƙasa da murya tace.
"Uhum shidama akace shine shugaban tuzuran ƙasar nan, yana zaune baiyi aureba, ai zama ba aurema ba kyau tunda dai yanada damar yi ko?".
Ɗan tsagaita takunshi yayi tare da cewa.
"Hummh".
A hankali ta bishi a baya cikin yanayin muryar mara lfy tace.
"Dan Allah ka tsaya in rigaka shiga kar yace sai ya dubaka kafin ya dubani".
Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin.
Da sauri Garkuwa ta zazzaro idanunta baki ɗaya, tare da dafe ƙirjinta ganin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa.
"Barka da hantsi Sheykh".
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da tamfatsetsen Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.

Ita kuwa Garkuwa gaba ɗaya tsorone ya rufeta,
Gefen Rafi'a taje ta zauna wanda a take kuma mararta taci gaba da murɗawa da kartawa.

Da ƙarfi ta damƙi hannun Rafi'a.
Cikin tausayawa Rafi'a tace.
"Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za'a kiraki, dan na nemi al'farman sauran sun yarda Khadija Nasir Shugaba ce aka shigar, ƴar gwamnan, ba lfy".
Kai kawai ta iya gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi.

Shi kuwa Sheykh yana shiga Office dinshi, ya fara aikin daya kawoshi cikin ikon Allah kuwa Khadija ta samu sauƙi tunda ya dubata aka bata magunguna.

Mutun biyar ya duba, na shida kuwa, Aysha ce.

Koda aka kira sunanta jiki a mace ta miƙe ta nufi inda take ganin ana shiga.
Nurse namiji na gabanta.
A haka suka shiga,
Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba.
Chapter 10 · 0% Book details