← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 142

Sashe 73

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Sarkin Shaɗi ya miƙa Abba wani butan duma.
Sannan ya amshi borgon.
Shi kuwa Lamiɗo Haroon ya kalla tare da cewa.
"Cire mishi wannan rigar".
Da sauri Haroon yace to kana ya fara kiciniyar cirewa mishi jallabiyar.
Duk da yana galabaice saida ya ɗan ja tsaki tare da ture hannun Haroon cikin muryar dake baiyana a wahalce yake yace.
"Bana so ku barmin rigata".
Hannunshi Abba ya buge tare da cewa.
"Bakinka bazai mutu bako".
Shiru yayi yana gani Haroon ya cire mishi rigar
cikin murmushin da ganin jarumta da ƙarfin hali irin na Jabeer Galadima yace.
"Cire wannan ta cikinma".
Ba musu ya bari Haroon ya cire mishi rigar,
Wani irin zaro ido Haroon yayi gani duk jikinshi yayi shatin zanen irin manyan kunama nan".
Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa murmushi sukayi tare da haɗa baki wurin cewa.
"Uhum dafin ya gama fita, cikin jininshi."
Abba kuwa hannun ya haɗa ya miƙa wa Lamiɗo dake mishi alamun zai zuba mishi abu a hannun.
Wani haɗin mgnin ya zuba mishi cikin tafin hannunshi.
Murzawa yayi kana, ya shafa a duk jikin Jabeer.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe idonshi.
sabida wani irin sanyin da yaji yana ratsashi har cikin ƙasusuwan jikinshi.
Tuni wani bacci mai fitinenne daɗi ya kwasheshi.

Nan suka gama yi mishi komai.
Kana suka fita,
Dr Aliyu kuwa da Ya Hashim suka shigo bisa umarni Lamiɗo.

Drip and injections Dr Aliyu ya ɗaura mishi tare dasa ruwan alluran a cikin ƙarin ruwan da akeyi mishi.

Ganin sun gama yi mishi komai ne, suka fita suka tafi.
Suka bar Haroon kaɗai. Dan in ruwan ya ƙare ya cire mishi.

A falo kuwa Ya Hashim nayi musu bayanin ya samu bacci jikin da sauƙin duk sai suka tashi suka nufi masallaci.
Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya aka bari a wurin.
Sum jin shiru ba motsin Haroon yasa suka tafi sashin Juwairiyya dan bawa hadimanta umarnin shiga kitchen.

Bayan awa ɗaya kuwa ruwan ya ƙare ya cire mishi.
Ganin yana bacci ne yasa ya shiga wonka.

A can cikin gidan kuwa. Sashin Gimbiya Saudatu zaune take a bisa bakin gadonta ita da Laminu ɗan ta na biyu video da yayi a Rugar Bani na zabgar Jabeer yake nuna mata, cike da tsantsar jin daɗi, sai dariyar mugunta sukeyi.
Babban ɗan ta Ya Hashim ne, zaune can gefensu, ya zuba musu ido, yana nazartansu, to sukuma me sukeji a zuƙatansu, akan Jabeer da sauran ƴan uwansa shin duk wannan ƙiyeyyar ta mecece".
Muryar Baba Nasiru suka jiyo a falon yana sallama.
Da sauri Gimbiya Saudatu ta miƙa tsaye tare da kamo hannun Laminu tace.
"Zo taho muje gacan ƙaramin Babanku".
Da sauri suka nufi hanyar fita, wani irin kallo yayiwa Ya Hashim tare da jan tsaki cikin faɗa tace.
"Banza mara zuciya, wanda bai san masoyansa da maƙiyansa, ai dai duk abinda nakeyi a kankane".
Tana faɗin hakan suka fice.
Jiki a mace yabi bayansu, Allah ya sani baya son cutar da Jabeer da sukeyi.
A falon ya samesu zaune harda Baba Bashiru sunata sheƙa dariyar mugunta.
Gefe can ya zauna ya zuba musu ido. Bayan sun ɗan tsagaita dariyar ne,
Baba Nasira ya nisa tare da cewa.
"Allah kenan maji roƙon bawa, gashi ya amsa min addu'o'in da nai a safiyar yau ɗin nan,
Yadda na wuni da baƙin ciki, shi kuma zai kwana da azaba".
Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
"Ai Ni nafi kowa farin cikin wannan dukan Kawo wuƙa da akayi wa wannan hegen yaro mai jajayen kunnu, yaro sai hegen baki da rashin tsoro duk barazanar da akeyi mishi baya kashe bakinsa.
Musamman ni kam ina mgna kafinma in sauƙe numfashin ya bani amsa ga shegen azanci. Ɗan is abun buga cincim yau dai babu wannan bakin ai".
Cikin dariyar ƙeta Laminu yace.
"Ai wlh Umma ni so nayi a kashe hege a can, mu binneshi a waccar ƙaramar Rugar mu dawo salum salum abinmu".
Cikin murtuke fuska Baba Basiru ya kallesu tare da cewa.
"Ai Ni yau ko mutuwa yayi ban huce baƙin cikin dana shaƙa ba lokacin da naga ya fito ɗakin sirri da Lamiɗo har yanzu in na tuna zuciyata bugawa takeyi, to wai ma meye hakan ke nufi.
Da farin ɗan uwanmu da aka bawa Galadima ya rasu dare ɗaya, ana biyu aka bawa wancan hegen yaro mai nisan kwana Jafar ɗin sarautar.
Wannan abu shi yafi komai tada mana hankali, tunda dama duk cikinmu yaran Lamiɗo babu wanda ya ba koda sarautar fadanci ce sai Yaya Muhammad, to kuma dan ya rasu sai a maida sarautar kam jikoki a tsallake ƴaƴan duka."
Cikin tafasar zuciya Laminu yace.
"Yo waya ma sani ko sune suka kashe mana Babanmu dan mulkin ya koma hannunsu, ku kuma kuka barsu".
Da sauri Baba Nasiru yace.
"Muka barsu kuma, ai Allah ne zai barshi ba mu in bamu ɗauki mataki ba, Allah ya nuna ikonaa yanzu shi Jafar ɗin kallon me akeyi mishi?".
Da sauri Gimbiya Saudatu tace.
"Mahaukaci tuburan".
Dariya sukayi kana cikin rashin gamsuwa Laminu yace.
"To kuma duk da haka ai ba'a dawo da sarautar kanmu ba sai, aka bawa ɗan tsohon sarkin wannan bappan naku mai farin gemu.
Bayan nan kuwa duk bawa kowa mulkin komai ba, dan sakacinku an ɗauki mulkin Garkuwa an bashi."
Cikin sanyi Ya Hashim ya harari ƙanin nashi tare da cewa.
"Laminu kafa ji tsoron Allah ka tsarkake zuciyarka, ka raba kanka da wannan zalumci da kafurar zuciya".
Cikin zafi Gimbiya Saudatu tace.
"Rufe min baki, samodaran banza sako tumaki ɓallo jakai,".
Cikin sanyi yace.
"Umma badake nakeyi ba da".
Cikin mgnar in-ina Baba Nasiru yace.
"Tafi daga nan damu kakeyi mana, ka fake da Laminu, maza tashi ka bamu wuri".
Miƙewa yayi ya fita ya bar musu wurin ya nufi sashinsa wurin iyalanshi.

Su kuwa nan sukaci gaba da sabgogin gabansu.
Nan Gimbiya Saudatu ke cewa.
"Sai gobe da sassafe zanje in salon hegen balaraben nan".
Dariya Laminu yayi tare da cewa.
"Yau da yaga haza, yaga zai zanu sai cewa yayi, wai shi ba bafulatani bane, a kirashi dama duk ƙabilar da akaga dama".
Playing video yayi ya miƙa wa su Baba Basiru tare da cewa.
"Jaridar safi ta gobe da safe da wannan labarin zai fito a shafin forko nako wanne kamfanin jarida,
Kana wannan abun shine hirar da BBC Hausa da kanshi zasuyi karin kumallo dashi. Sai wannan lbri da video da hotuna sun bazu tako ina, dan ina jirane sai jaridu sun fidda shi kafin in watsashi kafafen yaɗa labarai na duniyar gizo-gizo".
Cikin tsananin jin daɗi suka jinjina wa basirar Laminu.

A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa, kekyawar tsohuwar bafullatana ƴar kimanin shekaru 61 sosai hankalin ta ya tashi jin labarin abinda ya samu jikanta mafi soyuwa a gareta. Cikin rawan jiki ta miƙe tare da juyawa zata nufi Side ɗin ta.
Da sauri Lamiɗo yayi gyaran muryar dake mata nunin ta zauna ta nitsu.
Cikin tashin hankali ta koma ta zauna tare da cewa.
"Allah Rane zanje in duba halin da yake cikine".
Cikin ƙasaita da bada umarni yace.
"Koma ki zauna ki nitsu kin ga magriba ta ƙara to. Bawai zan hanaki zuwa bane, ki bari ayi sallan magriba da isha'i sai ki aika Jakadiya ta dubo miki in idonshi biyu sai kije".
Ba don ta soba ta amince da hakan.

Hajia Mama kuwa, tana jin lbrin abinda ya faru daga bakin Abba, kai tsaye daga sashinsa sashin Jabeer ɗin ta nufa.
A falo ta samu Haroon kadai zaune cikin shigar kakanan kaya. Cikin tashin hankali da kiɗima da firgici ta nufi hanyar side ɗin. Jabeer ɗin ido na zubda hawaye.
Da sauri Haroon ya miƙa tsaye cikin sanyi yace.
"Mama ya samu bacci ne, kuma Dr Aliyu yace kada a tadashi, jikin da sauƙi ma sosai ki kontar da hankalinki".
Ina hankalinta bai konta da hakanba, saima ƙara kutsa kai cikin falon side ɗin shi takeyi.
Cikin sanyi ta tsaya jin Haroon na ce mata.
"Dan Allah Mama kiyi haƙuri, Allah kuwa jikin da sauƙin, Abba da Lamiɗo da kansu suka kula dashi, yanzu haka bacci yakeyi."
Cikin tashin hankali murya na rawa tace.
"Haroon hankali na ya tashi sosai, ina tsoron kada a cutar min dashi kamar yadda akayiwa Jafar."
Hannunta ya kamo kana yaja suka dawo falo, cikin sanyi yace.
"In Sha Allah babu wani abinda zai sameshi, in Allah ya yarda an gama samun nasara a kansu, yanzu warakace ke kusantosu, in sha Allah duk sarƙaƙiyan dake sarƙafe cikin masarautarku da mutanen cikinta zai worwore, za kuma ayi walƙiya kowa zai ga kowa!".
Wani irin lumshe ido tayi tare da cewa.
"Allah yasa haka".
Cikin kontar mata da hankali yace.
"Amin Amin. Umaymah ma tace tana nan tafe".
Cikin tarin mamaki da baiyana tsantsar jin daɗin ta tace.
"Alhamdulillah kai naji daɗin wannan mgnar ko ba komai in tazo ai zan samu wacce zan tattauna damuwar raina, sabida hirar waya bata wadatar wa".
Murmushi yayi tare da nuna mata hanyar fita cikin tsokana yace.
"Wato kun san ɗan naku ragone shiyasa duk kuka tashi hankulanku."
Cikin share hawayenta tace.
"Haroon yayanka nefa".
Tura baki yayi tare da cewa.
"To naji Hajia Mama je kiyi salla lokacin salla yayi, kinji an fara kiran salla".
Da haka ta fita.

Shi kuwa Haroon a hankali ya nufi cikin ɗakin, kamar yadda yabar Ya Jafar zaune a tsakiyar gado yasa Jabeer a gaba, yana karatu tare da gyara mishi rufuwar shi.
Haka ya sameshi yanzuma,
Kuma har zuwa yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba.
Kana ganin fuskarshi zaka hango zazzafan so da ƙanan da tausayin ƙanin nashi cikin ƙwayar idonshi.
A hankali Haroon ya matsosu.
Cikin sanyi yakai hannunshi ya kamo hannun Ya Jafar ɗin.
Kanshi ya ɗago ya zuba mishi ido.
Murya cike da rauni Haroon yace.
"Ya Jafar tashi kazo muje masallaci lokacin salla yayi. Muje muyi salla muyiwa Sheykh Jabeer Addu'o'in samun lfy".
Kanshi ya gyaɗa sabida in dai abu na ibadane to bai kasance jiɓeɓɓe a kanshi ba.
Sunkuyo wa, yayi ya sumɓaci goshin Jabeer kana, ya sauƙo kan gadon.
ƙofar Bathroom Haroon ya nuna mishi da yatsa.
Shiga yayi bayan ya fitone, shima Haroon ya shiga ya sabunta al'wala kana, suka fita.
Chapter 73 · 0% Book details