← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 142

Sashe 72

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can cikin fadar masarautar Joɗa kuwa.
Jin jiri na ɗibanshi ga duhu dake rufe mishi ganine ya sashi, tafiya a hankali tare da dafa jikin gini.
A haka har ya isa bakin Jakuzin,
A hankali ya zare al'kyabbar jikinshi, ya wurgar dashi can gefe,
kana ya tura ƙofar ya Jakuzin ya shiga,
tsayuwa yayi tsakiyarshi, hannun na rawa ya buɗe shawan ruwan ɗumi.
Wani irin numfarfashi wahala ya sauke lokacin da yaji ruwan ɗumi yana ratsa raɗi-raɗin azabobbun bulalin da yasha.
Wasu irin hawaye masu masifar zafine yaji suna tsastsafo mishi cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi, sai dai basu kai ga damar samun zobowa ba.
Wani irin tsuma duk illahirin sashin jikinshi ya fara,
zafin ruwan yakeji har cikin ƙoƙon ranshi,
wani irin karkarwa haƙoranshi sukeyi har suna dukan juna, kat-kat.
Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe idanunshi a hankali, ruwan dake gangarowa daga jikinshi yana bin ƙasa in da zai gangara yake kallo,
sabida zakace jinine ba ruwaba,
Sabida yana wonke mishi jinin jikinshi.
Haka ya tsaya a ƙasan ruwan ɗumin har saida yaga jinin ya daina zuba kamar da fari.
Sannan yasa hannunshi ya ɗauki daddaɗan sabulun wankan shi, ya fara murza sabulun taki wani sashi na jikinsa, wani irin wahaltaccen ƙara yayi lokacin da sabulun ya ratsa inda ya farfashe a jikinsa, cikin rauni yace.
"Wayyo Allah na! Wayyo Mamey na zan mutu, zafi zai kasheni tun kafin cikar burina."
Ci gaba yayi da murza sabulun tare daci gaba da cewa.
"Wayyo Umaymah wayyo Ummi".
Sai kuma ya taune lips ɗinshi kana ya rumtse idanunshi yayi ta murza sabulun tako ina yanayi ruwan ɗumi na dukanshi.
A haka yayi wonka ya wonke duk wani jini dake jikinshi yayi fes.
Al'wala yayi, kana ya fito cikin Glass ɗin sannan ya ɗauki wanni tattausan baby towel fari ƙal ya ɗaura a ƙirjinshi ya sauƙo har zuwa guiwansa.
Hannunshi yasa ya murza farin boxes dake jikinsa wanda ɗazu yake jiƙe da jini yanzu kuma yayi fari tas.
Murza boxes ɗin yayi har ƙasa, kana ya ɗaurashi kan al'kyabbar jikinshi da ya cire,
Cikin Woshing mashine yasasu,
Kana ya fara yin taku a hankali ya iso gaban drower'n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin.
Wani tattausan gajeren wondo fari tas mai ratsin sky blue ya saka, gajeren wondon yazo mishi har guiwarsa, kuma mai ɗan faɗine,
Wata tattaunawar riga mai guntun hannu wacce itama farace da ratsin Sky blue, ya saka, kana ya zaro wata ɓakar tattausar jallabiya doguwa har ƙasa tazo mishi daya zurata,
Wani hulan taɓa kaji Hadisi ya kifa kan suman kanshi dake da ɗan damshin ruwan ɗumin.

A hankali yake taku sabida zuwa yanzu wani fitinenne zazzafan zazzaɓi yakeji.
Jiki na rawa ya fito, bisa sallayarshi dake shimfiɗe a wata ƴar kusurwa yaje ya hau.
Yana hawa kan sallayar ya fuskanci gabas, yaji zuciyarshi tayi wasai, baya tuna komai, baya kuma jin ciwon komai a jiki da zuciyarshi sabida kushi'i da tawakkali da kyutata ibada baya jin komai sai hasken farin cikin ibada.
Kabbara ya tada tare da niyar sallan la'asar daya mannata bisa laruri ya makarar dashi.

A falonshi kuwa, hankalin Haroon ya tashi yana nan tsaye bakin ƙofa yana ta magiyar ya buɗe mishi,
bai saniba shi yana can har cikin bathroom ɗin shi.
Yana nan tsaye, mai Martaba Lamiɗo da Galadima suka iso tare da Sarkin Shaɗi.
Cikin sanyi yacewa Lamiɗo.
"Ya shiga ciki kuma ya rufe ƙodar ta ciki, inata kiranshi baya amsawa.

Murmushi Lamiɗo yayi kana, yacewa Galadima.
"Muje".
Kusan a tare suka fito falon.
Suka zauna, kana ya kira Abba, yace yazo yasa ɗanshi ya buɗe musu ƙofar.

Jin hakane yasa Abba tahowa da sauri.

A can babban falon kuma. Cikin damuwa Jamil ya labartawa Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya abinda ya faru.
Ga mamakinsu sai sukaga Jakadiyarsu tayi wani ƙayataccen dariya cikin sakekkiyar murya tace.
"Alhamdulillah wannan shine abinda muka daɗe muna jira tsowon shekaru da dama.
Kuma jinyarsa abune mai sauƙin".
Cikin ruɗani Jalal yace.
"Ummi kuka daɗe kuna jira kuma?".
Kai ta jinjina mishi, kana ta miƙe ta nufi kitchin dan harhaɗa aikin da akasata.

A nan Abba yazo ya samesu.
Jalal na ganinshi ya kauda kanshi.
Hakama Jamil Imran kuma bayanshi yabi suka nufi side ɗin Jabeer ɗin.

A falo ya samu iyayen nashi,
Cikin girmamawa ya rusuna yayi Lamiɗo Barka da yammaci kana ya matso kusa da baƙin ƙofar Bedroom ɗin Jabeer cikin ɗaga sauti yace.
"Muhammad! Muhammad Jabeer! Jabeer!! Jabeeey!!! Ka taso maza kazo ka buɗe min ƙofar nan ina jiran ka".

Jabeer kuma da yanzu yake raka'ar ƙarshe, sam hankalinshi baya ga jin kiran Abbanshi domin a yanzu yana gaban Ubangijinmu ne.

Haroon kuwa wayar dake kunnenshi ya gyara riƙewa cikin shaƙiyancinsa yace.
"Uhumm Umaymah ke dai kicewa Sarki Jalaluddin da Sarki Abubakar baban Daddy na, suyiwa masarauta Joɗo gudumowar suturu. Domin yau dai ran ƴan maza ya ɓaci, nasan sai ya yayyage kab wani abu mai yaguwa a masarautarsu".
Cikin wani irin farin cikin wannan labarin da Umaymah taji tayi kekkyawan dariya tare da cewa.
"Haroon yayan naka kakeyiwa tsiyako?".
Cikin tura baki yace.
"Allah ko Umaymah kecema kike sawa Jabeer yana rainani wai yayana".
Da sauri tace.
"To ba yayanka ɗin bane?".
Cikin yamutsa fuska yace.
"Yayan kwana arba'in, shiyasa yake min kallon kobo biyu da sisi, sabida yana jin kuna ce mishi yayana, wani lokacin har cemin yaro yakeyi dan tsabar son girma da manyance, Ni mamaki da yake bani kawai sai in zuba mishi ido in naga yana min faɗa kamar wani ɗan cikinsa".
Murmushi Umaymah tayi kana, tace.
"Gobe zuwa jibi in sha Allah ina nan zuwa Masarauta Joɗo, sabida zanzo in lallashi ɗana nasan yayi zazzafan fushi tunda yaƙi kula Dr Aliyu ma".
Daga nan sukayi sallama.

Shi kuwa Sheykh Jabeer saida ya isar da sallameshi yayi addu'o'in shi
Kafin ya tashi a hankali ya nufi bakin ƙofar sabida zuwa yanzu zanan bulalin sunyi tsami ga zazzaɓi daya mishi rubdugu.
A hankali ya murɗa key ɗin ƙofar ya buɗe ta, kana ya juya ya koma kan gadonshi, sabida rawa da jikinshi keyi na zazzafan zazzaɓi da wahala.

Yana konciya ya lumshe idonshi tare da fara karanta Suratul Khaf kasancewar yau yammacin jumma'a ne.

Su kuwa a falo suna jin sautin buɗe ƙofar, suka zubawa ƙofar ido ganin shiru bai fitobane yasa.

Galadima da Haroon suka nufi cikin ɗakin.
Jim kaɗan da shigarsu Galadima ya fito da sauri ya kira sarkin Shaɗi, da Lamiɗo kana da Abba.

A tare suka nufi cikin ɗakin, suna shiga Haroon ya fito.
Babban Falon ya koma ya nufa yana kiran Jakadiyarsu da sunan da suke kiranta.
"Ummi! Ummi!!".
Da sauri ta fito kitchen ɗin riƙe da filas da kofuna, sai kuma wani ɗan kwarya mai kyau ruwan ciki na tururi.

Da sauri ta miƙa mishi tare da cewa.
"Yauwa Haroona gashi kai musu da sauri".
To yace kana ya amsa ya juya ya koma, can cikin ɗakin Jabeer ɗin.

Zaune suke gaba ɗayansu, shi kuma yana konce ya duƙunƙune cikin wani jibgegen blanket mai masifar kyau da taushi.
Sai karkarwa yakeyi tamkar mazari,
Cikin sanyi Lamiɗo ya ɗan janye borgon tare da cewa.
"Jabeer!".
Duk da azaban zafin da yake ciki, bai hanashi buɗe idonshi ba, wani irin mugun kallo ya watsawa Lamiɗo,
murmushi sukayi baki ɗayansu kana cikin lallami Galadima yasa hannunshi ya kamo nashi cikin sanyi yace.
"Jabeer tashi ko? Tashi kasha mgni".
A kufule yace.
"Bazan shaba ku barni in mutu tunda hakan shine fatanku".
Da sauri Abba ya kauda kai tare da yin wani faffaɗan murmushi kana, ya juyo ya kalleshi cikin bada umarni yace.
"Muhammad tashi. Maza tashi kasha mgni".
Kanshi ya ɗan gyaɗa kana a hankali ya fara yunƙirin tashi zaune.
Ganin hakane Haroon yayi saurin taimaka mishi ya tashi zaune.
Idonshi ya rumtse sabida ji yake kamar har cikin ƙasusuwan jikinshi ake tsikara da bakin allurai gashi duk inda hudar gashi yake a jikinsa sai ya ɗan tasa kamar wurin da cinaka ya ciza.
Cikin tarin kula da wani mashahurin farin ciki, Lamiɗo da kanshi ya amshi haɗin maganin da sarkin Shaɗi yayi mishi a wani ma dai-dai cin kofi.

Hannunshi yasa ya amshi kofin kana ya kaishi bakinshi,
fuska ya kwaɓe sabida gafin mgnin da yaji a jikinshi.
Cikin bada umarni Abba yace.
"Ka shanye duka".
Ido ya rumtse kana ya kafa kanshi ya shanye shi tas.
Miƙa musu kofin yayi, kana ya amshi wani kofin da Abbansu ke miƙa mishi,
Shima shanye shi yayi tas.
Yana miƙa wa Lamiɗo kofin.
Ya fara wani irin gyatsa mai ƙarfi, gyatsan a jere a jere.
Cikin sanyi Haroon yace.
"Sanno my broz".
Ina babu halin amsawa dan gyatsan ya tsananta, wani irin zufane ya keto mishi daga tsakiyar kai har kan babbar yatsarshi.
Wani irin murɗane ya fara ɗibanshi tamkar zai tsinke mishi ƴaƴan hanji.
Cikin wani irin zabura ya fara wani irin yunƙiri.
Sai gashi yanata kela wani irin baƙin amai akan tattausan blanket ɗin nan.
Murmushi Sarkin Shaɗi yayi tare da kallon aman da kyau kana ya juya ya kalli Lamiɗo da Abba yace.
"Da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, ga nan dafin yake amayarwa."
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Uhumm kaji mugun banza ko".
Shi kuwa Abba ido ya zubawa Jabeer ganin yadda yaketa kela amai, fuskarshi nan tayi jazir, jijiyar kan goshinsa nan ta tashi ta miƙe samɓal.
Haroon kuwa tallafeshi yayi yanata ce mishi sannu.

Sai dai yayi kusan 30 minutes yana kwara amai kafin ya koma ya jingina da jikin Haroon yanata wasu irin zafafan numfarfashi tare da lumshe idonsa.
Da sauri Lamiɗo yasa hannunshi ya tattare blanket ɗin ba tare da aman ya ɓata ko maiba.
Ya dunƙuleshi ya miƙa wa sarkin Shaɗi.
Chapter 72 · 0% Book details