← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 142

Sashe 62

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin mugun kallo ta watsa musu, kana cikin zafi da azalzalar zuciya da jin tarin tsanarsu ta gyara zama tare da cewa.
"Naji yau an ganka ka fito ɗakin sirri na masarautar Joɗa kaida mai martaba Lamiɗo, me hakan yake nufi?".
Ba tare da ta gama rufe bakintaba yace mata.
"Ina ɗakin sirrin masarautar Joɗa akace miki na fito, ba ɗakin sirrin masarautar kuba na fito?".
Cikin kufula tace.
"Itama ɗin wannan masarautar ai tamuce, tunda ƴaƴanane manyan jikokin sarkin Nuruddeen, kuma babansune Galadima, shine kuka kasheshi, aka bawa wancan majanunin yayan naki mulkin Galadiman, to yanzuma kuma ɗan tsurfa da tsiri uwar me kukayi a cikin ɗakin sirrin? Me ya gaya maka? Me kuke shiryawa?".
Still harshenta ma bai gama komawa zaune ba ya jefa mata amsa.
"Ɗakin sirri mgnar sirri, tunda shi jakin daya kai miki rahoton, bai sanar miki me muka tattaunaba, Ni sai in miki jagora zuwa wurin Lamiɗo ki samu ki ganshi yanzu sai ki tambayeshi me yace min me mukayi, tunda kinsan in bani nai miki isoba sai ki kai sati nan gaba baki samu damar ganinshi ba".
Ya ƙarishe mgnar yana tsareta da fitinennun idanunshi wanda babu tsoro a cikinsu.
Cikin kufula tace.
"Ba girin-girin ba tayi mai, ta yaro kyau take bata ƙarko".
Amsa ya kuma bata.
"Surkin nakine yaron? Mutumin daya haifa miki miji, kika aura har kika haifi yayan da kike son su gajeshi, shine yaron? To asheko masarautar duk yarace, ke mulkarta, tunda nasan ko tsohonki bai kai, Lamiɗo ba".
Ohoho ina wuta ta faɗa ciki, cikin kausasa murya tace.
"Ina mai umurtarka da kada ka kuskura ka amshi wani mulkin daya wuce Garkuwa".
Cikin taɓe fuska yace.
"Anƙi bin umarnin naki".
Wani irin Murmushi mai baiyana jin daɗi da tarin Mamaki Haroon da Jamil sukayi.
Jalal da kanshi yau Hamma Jabeer ɗinsu ya shayar dashi tarin mamaki, ashe shi nashi ƙarfin halin da ake gani wasane, ga Jarumin da jarumtarsa ta girgiza, zuciyar Jalal. Dan harga Allah shi dai ya sani bazai taɓa iya yiwa Gimbiya Saudatu abinda Haammanshi keyi mata yanzuba, ashe dama haka yake, da kafiya da bada amsa tun kafin ta huta. Muryar Gimbiya Saudatu ce ta kuma katse mishi tunani.
"Yanzu bakinka ke iya furta ka haka,, yaro zakaci kan uwark".. da sauri ta zaro mishi ido jin yace mata.
"Kul kada ki ƙarasa, in kuwa kikayi gangancin ƙarasawa, zan". Katseshi tayi da cewa.
"Zakayi me? Gaya min isshe ɗan fitsara me zakayi".
Jalal ne ya amshi zancen da cewa.
"Zan datse miki harshe, kika kuma zagar mana uwa".
Cikin tsananin tsana ta watsawa Jalal harara tare da cewa.
"Zaka aikata! Babu musu! Menene ɗan giya bazai iya yiba, menene, ɗan iska ɗan daba bazaiyiba, banza ɗan sara suka, gwada datse min harshen ka gani, in akwai wanda zai rage da harshe a zuriyar uwarku".
Jabeer ne ya ɗan taune leɓenshi tare da kaɗa mata yatsa kana yace.
"Kulfa, ki raba kanki da zagin mace mai daraja".
Cikin isa da ƙasaita tayi wani irin dariya, kana ta miƙe tsaye, gabansu ta ɗan matso kana cikin izaya tace.
"Eh daraja ko? Uhummm lallai kam, aifa sai dai mace mai daraja."
Sai kuma ta ɗan ja da baya kana tace.
"Mace mai daraja ko mai zunubi, ai dai kun fara ganin sakayyar Allah tun a duniya, waya san metayiwa ubangiji, y...."
Juwairiyya ce, tasaki wani irin ƙara da yasa duk sukayi shiru.
Ita kuwa ta faɗi kasa a sume alamun makaranta sun dawo.
Ganin haka yasa Jakadiyarsu tayi kanta da gudu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
"Haka dai. Duk a haka zaku ƙare, mulki kuwa sai dai ku ga anayi, GARKUWAN da aka bakanma, zakaga me zai sameka dashi".
Tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar fita Hadimanta na biye da ita a baya.
Shi kuwa Sheykh Jabeer murya ya ɗan ɗaga a hankali yadda zata iya jinshi yace.
"Babu abinda zai sameni face dama Allah ya ƙaddara zai sameni, domin baki isa ki cutar daniba".
Cikin harshen fillanci tace.
"A laran ai, zaka gani ai".
Bai kulataba.
Ita kuma fita tayi.

Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido.
Haroon kuwa cikin rudu da ɗaure war kai yake mgnar zuci.
shin wai wannan wacce iriyar fitinenneyar masarautace, mai cike da tsarƙaƙiya, yanzuma dama a irin wannan yanayin Jabeer ke rayuwa da ƙannenshi da yayanshi da mahaifanshi.
To meyasa, bazasu bar musu masarautarba, tunda shi Jabeer bama son wannan mulke-mulken yakeba.
Sassanyan zazzaƙar Muryar Sheykh Jabeer ne ta katse mushi nazari, jin yana rere karatun Alqur'ani cikin nitsuwa yake, karanta fatiha.
Bayan ya kai ƙarshenta ya kuma yi bisimilla, ya fara Suratul Baqra, wanda yakeyi da ɗan ƙarfi, tare da fuskantar inda Juwairiyya ke kwance,
Yanayin karatun cike da taƙawa da kekyawan tajwid, shiyasa in ya fidda wani harafin kamarsu Khah sai kaji har ƙasan wurin yana amsa amon sautin."
A hankali Juwairiyya ta fara buɗe idanunta, tana mai bin karatun da takejin,
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Jakadiyarsu tace.
"Alhamdulillah Jabeer ta farfaɗo".
Ta faɗi hakane sabida tasan duk sansa Juwairiyya ta faɗin in dai zai mata Rugyag rufe idonshi yakeyi.
Jin Jakadiyarsu tace ta farfaɗo ne, tasashi, yin hamandala tare da cewa, Jakadiyarsu ta meda Juwairiyya Side ɗin ta, kana ya kalli Jalal tare da cewa.
"Jalaluddin kaje, ka kula da Ya Jafar, ka bashi abinci kana ka shirya shi, shirin zuwa sallan jumma'a kaima kaje ka shirya."
To sukace kana duk suka fita. har sunje bakin ƙofar fira yace.
"Jalaluddin kasa kayan mutunci".
Cikin sanyi yace.
"To". Sannan suka fita.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli, Jamil, tare da cewa.
"Ka gyara mana bedroom."
Yana jin haka ya miƙe ya nufi bedroom ɗin.
Shi kuwa Haroon ido ya zuwa Jabeer, sabida gaba ɗaya muryarshi ta tabbatar musu, yana cikin tsananin ɓacin rai, kai Haroon ya jinjina ganin Jabeer yasa hannu ya janye hiramin dake kanshi, ya taune lips ɗinshi, kana ya rufe idanunshi, cikin ƙarfi yasa hannunshi ya fara jan bakin hiramin , da yake sabo fil janshi yakeyi alamun zai yagashi.
Shiru Haroon yayi baiyi yunƙurin hanashi ba, domin dama yasan za'a rina, sabida shi Jabeer wannan itace babbar alamar tsananin ɓacin ransa, muddin fushinsa ya hauhawa to, yakan yayyaga abu da karfi.
Fass haka Haroon yaji sautin, yagewar sabon hiramin nan.
Shi kuwa Jabeer idonshi ya ƙara rumtsewa yanayi mai ci gaba da fatattaka hiramin.
Murmushi Haroon yayi cikin tare da fara ɗaukar shi video.
Yanayi dan tsokana.

A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan,
Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ƙenƙesa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau.
A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin zaƙuwa tace.
"Yakura, muje, side ɗinshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba."
Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da miƙewa tace.
"Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi".
Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer ɗin.

Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ƙofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.

A falon suka samesu, zaune.
Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa.
Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi.
Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa.
"Barka da fitowa Hajia Mama".
Da sauri ta ƙarasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna,
cikin tarin kula tace.
"Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?".
"Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taɓa minshi? Waya taɓo ɗan lelen Umaymah'nshi Da Sitti'nshi?".
Cikin lumshe ido Haroon yace.
"To Hajia Mama wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki, ta ƴar uwarki ko ta ɗan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya damƙi ƴar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ƙwatar kanshi".
Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana,
ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi ɗanye,
wani irin sonshi da ƙaunarshi takeji, jiki da zuciyarta,
Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ƙawanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu ɗaya, yayi baƙi sitib dashi ya konta lib sai sheƙi yakeyi, jajayen laɓɓan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.
Chapter 62 · 0% Book details