← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 142

Sashe 114

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dogon numfashi Junaidu yaja tare da cewa.
"Adda Shatu, ashe mun samu nasara, an kora mana mugun babarbarenen nan,".
Uhum tace a taƙaice.
Shi kuwa Junaidu cigaba da mgna yayi.
"Adda Shatu Ya Salmanu ba lfy, yazo dubamu da jiki shima an kamashi gado.
Shi yake cemin wai su Bappa sun tafi Lardi. Ayyah Adda Shatu yanzu sai yaushe zasu dawo? Kina mgna dasu ne?".
Cikin dariya tace.
"Faɗi gsky dai Junainah kake son tambaya dai. Junaidu.
Suna lfy ina mgna dasu. Sai bayan salla zasu dawo."
Da sauri yace.
"Dan Allah Adda Shatu turo min number su".
To tace tare da gyara konciyarta.
Nan dai suka ɗan yi hira, kana sukayi sallama.
Sannan ta tura mushi number su ɗin.

Suna gamawa ta kira Number Bappa.
Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga.
Cikin jin daɗin jin muryarshi tace.
"Ina kwana Bappa na".

"Lfy lau Alhamdulillah Shatu ya Azumi, da baƙon wuri".
Cikin sanyi tace.
"Alhamdulillah, Bappa yaushe zaku dawo".
Dariya yayi mai ɗan sauti kana yace.
"Bayan salla".
Cikin lumshe ido hawaye na zuba tace.
"Bappa ina jin kewarku, bani da kowa nawa kusa dani.
In na tuno su ya Giɗi hankalina na tashi Bappa inyi ta kuka babu mai sanin irin ciwon da nakeji a raina".
Cikin sanyi yace.
"Kwantar da hankalinki Shatu, su Ya Giɗi suna raye, sai dai suna cikin mawuyacin hali, suna buƙatar addu'o'in ki musamman a cikin wannan mata mai alfarma, na sanki bakya wasa da riƙo da ibada, amman ki ƙara kan yadda kike, in sha Allah wata rana zasu dawo garemu, cikin sauƙaƙƙiyar hanya, addu'a itace abinda suke so, shiyasa na gaya miki abinda Allah ya nuna min a mafarki a kansu".
Cikin sassanyan kuka murya can ƙasa tace.
"Zanyi Bappa zan ƙara zan dage, kuma zan roƙi a tayamu addu'o'in a masallatai da wurin tabsir."
Cikin jin daɗi yace.
"Yauwa Shatu na, ki kwantar da hankalinki, ki zauna lfy da mutanen da kike tare dasu, kiyiwa mijinki biyayya, kiyiwa mayanshi biyayya bana son musu in babba ya gaya miki abu matukar bai saɓawa shariyar musulunci ba."
Cikin sanyi tace.
"To". Da sauri yace mata ga Junainah".
Cikin jin daɗi tace.
"To a bata waya".
Tsalle Junainah tayi tare da cewa.
"Adda Shatu, kizo Lardi garin da daɗi kullum sai an gasa mana zabbi ko Tattabaru, insha nono da zuma inci naman insha zuma, inci su inabi sai na ƙoshi".
Cikin so da ƙauna da shaƙuwar ta da yarinyar tace.
"Allah sarki Junnu ke ko kewata bakiyi bako?".
Dariya tayi tare da cewa.
"Nayi kewarku mana harda Ya Junaidu ma nayi kewarshki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na bashi number ku, zai kira ku gaisa".
Tsalle tayi tare da nufar ɗakin Ummey.
Ita kuwa Shatu cikin dariya tace.
"Azuminki nawa".
Da sauri tace.
"Azumi na ɗaya ranan nayi rabi daga safe zuwa azahar jiya kuma na ƙarisa rabin daga azahar zuwa mangriba".
Wani irin dariya ne ya rufe Shatu dariya takeyi sosai.
Kewa da bege da son ƙanwar tata ya rufeta.
Da Sauri ta tsagaita da dariyar jin Junainah na cewa.
"Adda Shatu Bappa yayi aure an samo mana wata Inna mai kirki".
Cikin mamaki tace.
"Ke Junnu ƙarya ba kyau fa".
Da sauri tace.
"To ga Ummey ki tambayeta kiji".
Ajiyan zuciya ta sauƙe jin muryar Ummey cikin sanyi da jin daɗi tace.
"Ina kwana Ummey na ya gida, ya Junnuna nayi kewarku, Ummey wai da gaske Bappa yayi aure".
Murmushi mai faɗi Ummey tayi tare da cewa.
"To duk Alhamdulillah muna lfy eh Bappa yayi aure an bashi ƙanwar innarku, Indo kin santa ai ita take bin innarku, Bata taɓa haihuwa ba, to ashe mijinta ya rasu.
Shine yanzu aka aura mishi ita. Kuma tanada hankali kamar innarku".
Cikin sanyin jiki tace.
"Eh na san Umma Indo tanada kirki, to Allah ya baku zaman lfy yasa kuyi irin zaman da kukayi da Inna".
Amin Amin tace kana tai mata nasiha Sannan sukayi sallama.

Daga nan ta miƙa ta nufi ɗaki dan yin salla.

Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Ummi da Saratu da tun ɗazu tana nan.
Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai.

Kafin shida ta cikama sun gama komai.

Yanzu in sun zo buɗa baki ita da Ummi da Hibba tsakiyar falon suke dawowa.
Jalal, Jamil, Imran, Sulaiman, kuma su zauna a dinning table.

Ya Jafar kuwa wani lokacin har can falon Sheykh zai wuce suyi buɗa baki a tare.
Kana su tafi masallacin.

Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari.
A wurin al'ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta.

Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur.
Cikin kula Ummi ta kalleta tare da cewa.
"Ɗauko kwanu kan nashi".
Kanta ta ɗan juyo ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ai bai dawo yaci ba ko?".
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
"Baya cin ƙosai, kuma kinga doyan ma jiya baiciba, ya gaji dasu ne, ki ɗauko a juyewa su Saratu shi ki ɗan haɗa mishi wani abu kafin ya dawo".
Cikin ɗan kauda kai tace.
"Ummi ai ƙoshi yake shiyasa bazai ciba, a barshi kawai in yaji yunwar yacima wani bai saniba, ai yunwa ba Umaymah bace ko ke bare zaku lallaɓashi".
Dariya Ummi tayi kana kuma ta haɗe fuska tare da cewa.
"Je kiyi abinda nace ko".
To tace ganin kamar ran Ummi ya ɓaci.

Bayan ta dawo da kwanukan ne,
Suka bawa Saratu ta juye, kana ta harhaɗa wonke-wonken ta fara.

Ita kuwa Shatu cikin yin miƙa tace.
"Ummi me zan dafa mishin?".
Juyawa tayi tana haura wurin da Fridge yake tare da ce mata.
"Duk abinda kika iya kika san ba mai nauyi bane".

Kanta ta gyaɗa tare da cewa.
"To".
Cikin ranta tace.
"Bari inyi Special Arish, in yaga dama yaci in yaso ya bari, mutun sai zaɓe-zaɓe kamar mai ciki.
Dankali ta ɗan ɗebo da Nama, kwai, tumatur, kabeji, Bama, maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita.

Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi.
Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al'basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan.

Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi.
Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan.
Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al'basa. bisa wata a ɗan tukunta.
Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe.
kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin.
saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al'basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu.
Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma.
Kana tasa Maggi da al'basa da Bama ta gauraya kana
Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka.
Kanta ta jujjuya tare da cewa.
"Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo".
Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa
"Yaushe ya dawo?"
Plate ta ɗauko tare da cewa.
"Tun ɗazu".
Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma.
Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace,
Ya akayi kika san ya dawo".
Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba.
Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe.
Ta shiryashi yayi kyau sosai.
Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi.
Kana tasa spoon da Fork a cikin tray'n data ajiye plate ɗin.
Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki.
Sannan turashi gefe.
Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi.
Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi.
Amsa Ummi tayi tare da cewa.
"Ɗauki ki kai mishi to".
To tace tare da ɗaukan tray'n ta fita.

A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito,
Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi.

Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv.

Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi.
Kana ta juya a hankali ta fita.

Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci.
Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa.
Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki.
Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo.
Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC'n zatayi.

Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al'wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi.
Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima.
Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu.

Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray'n abincin sahur ɗin shi.
Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi.
Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi.
Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area.

Washe gari da safe yau Jumma'a kuma, yaune azumi na shida.
Chapter 114 · 0% Book details