← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 142

Sashe 51

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Can cikin tsunƙurun dajin kuwa.
Ba'ana ne zaune cikin taron matasan ƙabilar ɓachama da a ƙalla sun kai goma, cikin kausasa murya da bada umarni yace.
"Zanyi fito ɗaya zuwa uku, cikin daƙiƙu 10 shanayen Malam Liman da Alhaji Haro da wasu. Zasu baiyana, a nan.
Suna zuwa ku jasu ku fuskanci gabas, ta ƙasar Jihar Gombe zaku ratsa, kana ku nufi ƙasar chadi daga can."
Shiru ya ɗanyi tare da zuba musu idanu, wani irin azzalumi murmushi yayi cikin barbarci ya kalli biyu dake kusa dashi wanda ƴan ƙanwar Bukar ne su barebari ne, cikin izaya yace.
"Kada ku kauda ido akan ko wacce gonar makiyayin da zaku wuce ta gabanshi, ku shiga gonakin manoma, kuyi kiwo a ciki.
Idan manoman suna cikin gonakin in sun muku mgna ku kashesu, sannan ku gudu da dabbobin yankin wurin".
Cikin barbarci ɗaya daga cikin su yace.
"Ba'ana, tsayuwa kiwon bazai ja mana tsaikoba, har cekiyar ya riskemu ba tare da munyi nisa ba".
Murmushi yayi mai cike da fajirci sumar kanshi ya shafa tare da cewa.
"Ba'akana Ku kiwaci duk gonakin manoma, hakanne zai jawo faɗa tsakanin MAKIYAYA da manoman, daga haka saiku gudu, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin su mutanen duniya sun ɗauka duk wanda suka gani da dabobbi yana kiwo, BAFULATANI NE, sam mutane sun kasa ganewa cewa ba sai Fulani kaɗai ke kiwoba, kaga mun tada faɗa mun kwashi dabobbinsu, mun kashesu mun gudu, kuma in sunje kai korafinsu ga hukuma a kamasu ko a korasu ko azagesu, ace suke haddasa faɗa tsakaninsu da manoma, sun zama ƴan ta'adda a idon duniya. Mun kwashe dukiyoyinsu".
Dariya sukayi baki ɗayansu, kana suka sara mishi, juyawa yayi, ya fuskanci gabas kana ya durƙusa, ya zuba guiwowinsa duka biyu a ƙasa, yatsarsa manuniya ta hannun hagu ya kafa a ƙasa, kana yatsarsa ta hannun dama kuma, ya toshe kunnenshi na dama, da ƙarfi ya rufe idanunshi kana, ya tsuke bakinsa ya rinƙa zuro iskar wata zazzafar fito mai bala'in sauti.
Su kuwa sauran duk rufe ido sukayi dan jin fiton sukeyi tamkar zai fasa musu dodon kunne.

Shi kuwa Ya Lado yana cikin kiwonshi kawai yaga gaba ɗaya, shanun sun juya sun fuskanci gabas, kana sun ɗaɗɗaga kunnuwansu sama, daga baya kuwa sunata karkaɗa binɗinsu.
Cikin mamaki yake ratso tsakiyarsu.
Dan in makiyayi yaga dabbobi suna haka yasan akwai abun da suka gani, ko mutun ko iska, ko maciji ko dai wani abu na daban to sukanyi wannan alamar dan sanar da makiyayinsu.
So ganin hakane yasa Lado ya ƙara kutso kai cikinsu.

Su kuwa dabbobin gaba ɗaya fiton da Ba'ana yake hurawane ya cika musu kunne, ai fa a take suka nausa a guje suka fuskanci gabas, da wani irin masifeffen gudu.
Shanu da dawakai na gaba tumaki da awaki na baya hatta belbelun dake cikinsu, suna kiwo binsu sukayi.
Cikin ƙarfi Ya Lado yayi wani irin ihun wanda dashi suke kiran dabbobinsu, amman ina basu juyoba.

Da gudu ya fara binsu kana yana ihun neman taimako a wurin sauran makiyayan su.

Amman da yake gudun dabba dana mutun ba ɗaya ba,
Sun mishi nisa mai tarin yawa, hakanan shi kuma yayiwa sauran makiyayan dake biyoshi a guje su kawomishi agaji ya musu nisa.
A haka suka rinƙa gudu,
waɗannan mutun huɗun dake laɓene suka fito suka, tareshi ba zato ba tsammani kawai yaji an burma mishi wuƙa juyowan da zaiyi kuma yaji an kuma burma mishi wuƙaƙe a tako ina na jikinsa.
A nan take ya faɗi babu rai.

Su kuwa nan sukabi shanun da gudu.

Koda sauran makiyayan suka iso inda gawar Ya Lado take.
Hankalinsu yayi masifar tashi.
Tabbas sun san babu masuyi musu wannan aikin sai ɓachama.
Ko hanƙo kurar dabbobin basayi.
Hankalinsu yayi mummunan tashi ganin gawar Lado, ga kuma tashin hankali da firgici rashin ganin su Gaini da Giɗi da Seyo Manunu da Sale.
Junaidu ne yayi sauri ya kira mahaifinsu Ahaji Horo a waya ya sanar mishi halin da ake ciki.

Wannan mummunan labari yayi matukar firgita al'ummar Rugar Bani hankalin kowa ya tashi.

Hankali Bappa kuwa in yayi dubu to ya tashi,
kuka cur-cur yakeyi da idanunshi.

Junainah kam kuka da ihu harda burbuwa takeyi tana cewa.
"Wayyo Ya Lado, Bappa ku nemo min Ya Gaini na da ya Seyo".
Sai ta kuma faɗa jikin Ummey daketa kuka tamkar ranta zai fita,
cikin kukan take cewa.
"Ummey kicewa Bappa suje su nemo min Ya Giɗi na, kada su bari a kasheshi kamar yadda aka kashe Ya Hashimu da Ya Isa, da kuma Yaya Lado".
Babu mai iya bata amsa a cikin wannan gida.
Duk da tarin maƙota da suka cika gidan.
suna zagaye da Inna wacce, take sume tunda taji yaranta Rai uku babusu babu dalilinsu su ko gawarsu ba'a ganiba ga kuma mutuwar Lado wanda shine yasata, sumewa.
Faɗin tashin hankali da mutanen Rugar Kikan ke ciki bazai taɓa misaltuwa ba.
Saidai ƙunane wanda duk mai imani zai iya ƙiyastashi a ranshi.

A cikin garin kuwa tuni Arɗo Yabani yasa anyi shela anyi taron gaggawa, kowa ya shirya za'a shiga daji neman su Gaini, ko Allah zaisa a samosu.

Haka matasa kusufa-kusufa suka rinƙa kusa kai cikin daji suna ratsa tsaununka da kozozzabai.

Bappa kuwa da Arɗo Yabani da Ahaji Haro, da Ahaji Umaru ne da sauran dattawan rugarsu dana kewaye, gawar Lado suka ɗauko suka dawo gida da ita da sauran shanayensu gaba ɗaya matasa kuma suka bazama nemansu Gaini.

Su kuwa sauran matasa majiya karfi daji suka rinƙa ratsawa.
Amman babu koda kurar dabbobin nan, bare alamun su Gaini illa iyaka dai takalmansu da suka tsinto.

A Rugar Bani kuwa, hankali na matukar tashe, Bappa ya tasa gawar Lado a gaba wacce sunyi mata wonka sun kimtsata cikin sutura kamar yadda shariya ta tanadar.
Kuka mai tsananin cin raine ya kwabcewa Bappa, yana ruggume da gawar.
Inna ma da yanzu ta farfaɗo da kukan ta farfaɗo, kuka takeyi tamkar ranta zai bar gangan jikinta.
Hakama sauran matan maƙota.
Hiden da Binto ma kuka sukeyi sosai a gidajensu sabida ɓacewar samarin su.

Dattawan ne sukayi ta bawa Bappa haƙuri da tausan zuciyarshi.
Ganin dare yayine yasa akace dole a bar gawar tayi kwanan keso.

Su Sule, Iro, Ado, Junaidu, Madu, Ari, Sani, Ibi, ja'eh, Ori, Binbi, dama sauran samari majiya karfi kuma kab sun cikin daji.

Haka suka kwana a can. Suna tafiya suna nema, kafin gari ya waye, wasu sun isa har jihar taraba, wasu Gombe, wasu har bauchi, wasu har cikin iware da mutun biyu na taraba,
Wasu sun nausa da nisa, sabida in dai tafiyace bata taɓa bawa bafulatani tsoroba domin anyi ittifaƙin duk ƙabilun duniya babu ƙabilar da takai ƙabilar fulani saurin tafiya da jumurin doguwar tafiyar ƙafaba, bayan laraban da.

Washe gari Litinin.
ɗin, sauran dattawan garin suka sallaci Ya Lado, kana suka zauna amsar gaisuwa.
Suna kuma jin labarin inda yaransuke.
Ganin sunata wahalar tafiya ba lbrine yasa.
Bappa yace su dowo. Domin wanna abu addu'ace mgninshi.
Sannan kuma wannan karon bazasu saurari masarautar Numan ba , gangami zasuyi su kai kukansu, ga masarautar Joɗa, wanda a cikinta ne GARKUWAN FULANIN ƙasar Nigeria gaba ɗaya yake.
Da fari Arɗo Yabani bai gamsu da hakanba saida Bappa yayi mishi bayanin.
Dolefa suna da buƙatar hukama mai tsarki ta shiga tsakaninsu da ƙabilun Ɓachamawa nan, kana dole mgnar ta isa ga babbar masarautarsu, wacce za'a miƙa mgnar ga Ƙungiyar *TABITAL POOLAKU, DA KUMA ƘUNGIYAR.*
*MIYETTI ALLAHA*
Wannan dalilin ne yasa Ardo Yabani ya umarci gaba ɗaya matasan da suka bazama neman su Gaini su juyo su dawo gida.
Haka kuwa akayi kafin yamma sai gasu duk sun daddawo domin.
Wasu da yawa motoci suka shigo.

Bayan sallan ishane suka zauna zaman mitin domin sun gama shirya komai gobe dai kai tsaye masarautar Joɗa zasu wuce.

Bayan sun gama tattauna yadda abun yake suka tsaida zance kan cewa dattawansune zasuje.
Daga nan Duk suka tashi taron kowa ya koma gidanshi da tarin al'hini a zuƙatansu.

A can cikin birnin Ɓadamaya kuwa cikin makarantar su Aysha.
Chapter 51 · 0% Book details