Sashe 91
Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
By
*GARKUWAR FULANI*Ido Laminu ya rumtse da ƙarfi.
Ganin Sheykh Jabeer yayi wani irin tsayuwa na ingarman, jarumin namiji nitsuwa da kamala, sai lips ɗinshi dake motsawa a hankali yana ambaton Allah.
Shi kuwa Ba'ana cikin tsantsar mugunta, ƙeda, da zalumci ya ɗago bulalar nan da azaban karfi ya zabgawa mishi ita a inda ya zabga ta forko.
Wanda yasa gaba ɗaya mutanen wurin suka rumtse idanunsu.
Especially Lamiɗo da tawagarsa,
Shi kuwa Sheykh Jabeer, zuciyarshi ta rigada ta gama tafasa, idonshi baya ganin komai sai wani irin azabebben duhu, kunnuwanshi basa jin komai sai sautin muryar mahaifinshi da kuwa Umaymah. Da suke bashi umarnin cewa dole yayiwa Lamiɗo mubaya'a.
Wani irin azaba mai girgiza ran mutun a jikinsa yakeji yana sukarshi har cikin ƙahon zuciyarshi, sai dai duk wani sihiri na jikin bulalar duk baya tasiri a jikinsa illa dai dafin kuna min kam tabbas yana jinsu.
Barmuji wanda shine al'ƙalin gasar kuma mai irga bulalin.
Da sauri ya rumtse idanunshi lokacin da Ba'ana ya tsulawa Jabeer bulala ta biyar waccee, a take jini ya fara tsastsafo duk inda ta konta.
Arɗo Bani kuwa da Bappa da Alhaji Haro da Alhaji Umaru, da Sarkin aska, da sauran dattawan garin da kewayensa wani irin fargaba ne da taraddadi mai firgitarwa suke ciki.
Gaba ɗaya bakunamsu addu'o'in ne a ciki.
Laminu kuwa tuni yanata ɗaukar duk abinda ke faruwa a ƴar ƙaramar na'ura sa. Yanayi yana dariyar farin ciki.
Jalal kuwa da sauri ya rumtse idanunshi kana ya koma baya.
Jamil kuwa cur-cur yake zubda hawaye ganin yadda jini ke tsastsafo wa, a tsakiyar bayan Hammansun.
Haroon da kanshi tsoro ya rufeshi, yaji ranshi ya fara zargin anya kuwa bada biyu aka haɗa wannan gasarba.
Muryar Barmuji ce ta cika wurin gaba ɗaya da alamun tsananin tausayawa yace.
"Goma!".
Alamar anyi mishi bulala ta goma kenan.
Shi kuwa Sheykh Jabeer Idonshi a buɗe suke, sai dai basa ganin komai sai duhu na tsantsar baƙin cikin abinda sashi yayi cikin bainal nasi a sashi tsayuwa da ɗan kampai,
Idanun nashi suna buɗe ras.
Launin su kuma ya sauya daga farin zaiba, zuwa jazir tamkar wanda maciji ya watsa dafi a cikinsu.
Gaba ɗaya fararen faratun yatsun hannunshi sun rine sunyi jazir tamkar wanda aka ƙunsawa jan lalle.
Ji yakeyi tamkar tsikarinshi akeyi da bakin allurai.
Tabbas duk da bai san dafin kunama ko macijiba, ya gane cewa akwai gubar dafin wani abu a jikin bulalin da ake tsula mishi tamkar za'a zare ranshi dasu.
duk ta inda hudar gashi yake a jikin shi, ji yakeyi tamkar ana soka mishi ƙarin kunamai.
Bukar kuwa, wani irin murmushin farin ciki yakeyi, ji yakeyi kamar ya fito ya taka rawa dan farin cikin ganin halin da jikan Sarki ke ciki.
Muryar na rawa Barmuji yaci ga da irge.
"Goma sha ɗaya! Sha biyu! sha uku! sha huɗu! sha biyar!!!."
Cikin sauri Haroon ya iso inda suke, hankali a tashe ya kamo hannun Barmuji cikin sanyi yace.
"Kai kasheshi zakuyi ne? Bulalin har nawa ne za'ayi?".
Cikin rawan murya Barmuji yace.
"In sha Allah bazai mutuba, bulali Hamsin za'ayi a ƙa'idar gasar, ba abinda zai sameshi tunda har gashi ya juri bulali 15 wanda a tarihin gasar Ba'ana babu wanda ya taɓa jurar koda bulala biyar ne".
Da ƙarfi Hashim ya zaro ido tare da cewa.
"50 wannan ai zalumci ne".
Da sauri Galadima ya miƙa ya nufi tsakiyar taron ganin Jalal ya nufi inda suke gadan-gadan bisa dukkan alamu kamo hannun ɗan uwan nashi zaiyi yaja su tafi.
Da sauri Galadima ya kama hannunshi cikin ɗaga murya yace.
"Kai Jalaluddin ina zakaje?".
Cikin faɗa yace.
"Zan ja ɗan uwana mu tafi, in ku bakwa sonshi bakwa da buƙatar shi, mu muna sonshi munada buƙatar shi, a rayuwarmu domin mu dai shine farin cikinmu, shine silar zamanmu cikin masarautarku, da tuni kun koramu tamkar karnuka, shine kuka haɗa Deel a kashe mana shi, to kuji ku sani zamu bar muku masarautarku in dai ganinmu ne bakwa tson yi."
Cikin faɗa Galadima yaja hannunshi yaje ya ajiyeshi gaban Lamiɗo.
Yana mai jin tausayin yaran.
Da ƙarfi Barmuji yace.
"Ashirin da biyar! Ashirin da shida!".
Zuwa wannan lokacin gaba ɗaya jikin Al'Sheykh Jabeer Habeebullah yayi ruɗu-ruɗu. Tuni farin boxes dake jikinshi ya cika da jinin dake gangarowa ta bayansa da cikinsa, inda bulalin suke taɓawa duka.
Babbar yatsarshi ta ƙafar damanshi da yatsun hannunshi kawai yake motsawa, wanda suke nuna alamun yana nan da rai daram da kuma haiyacinsa.
Bayan wannan babu abinda yake motsawa a jikinshi,
Cake ƙasar garin yakeyi da yatsar kafar tashi.
yatsun hannunshi kuma, motsasu yake yana tasbihi dasu, wanda shima cikin zuciyarshi yake ambaton Allah dayi mishi kirari da kyawawan sunayenshi.
Zafin da yakeji a jikinshi tabbas ya wuce zaton mai zato.
Taune lips ɗinshi na ƙasa yayi da fararen haƙoranshi tamkar zai hudasu, sai dai har cikin ƙashin haƙoran nashi yake jin azabar dafin dake cikin wadannan bulalin masu masifar siddabaru, sai dai babu wani siddabaru da yayi tasiri a kanshi ko a jikinsa domin shi Allah ya riƙe, Ba'ana kuwa tsafi ya riƙe.
Wannan gasace tsakanin gsky da ƙarya, bawai gasar caɗi bane kamar yadda mutanen wurin ke kallo.
Haka yasa duk da safin wannan bulalin sam basu kai zafin da yakeji a ranshi na sashi ya tsaya gaban dubban al'ummar garin da ɗan guntun wonɗo a jikinshi ba.
Allah ya sani shi mai kunya ne, kuma shi mai suturce kanshine, shida kanshi yana jin kunyar kanshi da kanshi.
Baya zama haka ko a ɗaki sabida yana tuna in mafa ya kaɗaice yana tare da Raƙib da Atib Mala'iku makusantan ɗan adam, wanda in ka bar tsiraicinka ma su kauda ido sukeyi daga gareka.
Shiyasa shima yake kauda ido daga kan kanshima bare wani.
Allah ya sani babu wani abu da aka taɓa yi mishi a duniya ya ƙona mishi rai sama da wannan abun.
Tabbas da an barshi hakama, yafi jin zafin hakan sama da waɗanan bulalin.
A ranshi yake wani irin kuka mai cin rai yana mgnar zuciya.
"Anci min zarafi an wulaƙantani an tozarta ni a gaban waɗan mutanen da wasun cikinsu zindigan kafuraine. An barni tamkar mara kima da galihu, wannan shine iya maƙurar zalumcin da akayiwa rayuwata a karo na biyu".
Sam baya jin zuciyarshi tanada raunin da zai iya zubda hawaye kan bulalin nan shiyasa ko zafinsu bai zame mishi abin zubda hawaye ko ihu da bakiba ko gudu ko wani motsi.
Zuwa yanzu hankalin kafuran ƙabilar ɓachama ya yi masifar tashi domin wannan shine karo na forko a rayuwar tarihin Ba'ana da ya zana mutun bulalin shaɗi har talatin da takwas baiyi ihuba bai zubda hawayeba, bai sumaba, bai faɗi ba, bai guduba.
Kai wannan abun yayi tsamari wannan wanne irin mutum ne, anya kuwa mutun ne ko al'jan.
Ya Salmanu kuwa, cikin tsanani kuka cur-cur da hawayenshi sabida yasan azabar da Sheykh Jabeer yakeji.
Juyawa yayi ya fuskanci gabas, sujjada yayi tare da fashewa da wani masifeffen kuka mai cike da rauni murya na rawa yake cewa.
"Ya Haiyu ya ƙaiyum, ya ziljalali wal ikram. Ya Allah ka ƙarawa wannan bawa naka dauriya da jarumta, ya Allah ka bashi ikon jure wannan azabar, ya ubangiji ka sanyaya mishi masifun dake jikin waɗanan bulalin, ya ubangijin taliƙai ka hana wannan mugun mushirkin bawa naka samun nasara, ya Allah ka kare musulminka kan wannan kafurin matsafin da baya salla".
Kuka sosai ne yaci ƙarfin Ya Salmanu.
Bappa ma wani irin raunine ya rufeshi tabbas kowa zaiyi tunanin Jabeer yana jin azabar duniya.
Sai dai kasan cewarsa Jarumin namiji haka yasa babu wata alama da ya nuna na yana jin zafi ko ciwo.
Sosai kuwa hakan ya tada hankalin kafuran.
Lamido da Galadima kuwa kallon juna sukayi tare da yin murmushi irin nasu na manyan fada, murmushi ne mai manufofi.
Jalal kam kife kansa yayi a cinyar Lamiɗo ya saki kuka mai sauti.
Haroon ma hawaye yakeyi zuwa yanzu.
Hankalin duk tawagar Lamiɗo yayi masifar tashi, ganin yadda wani irin azabebben zufa ya tsinkowa Jabeer tun daga tsakiyar kanshi, zufar nan take gangarowa har kan jikinshi gaba ɗaya, saida ya jiƙe yayi jilak tamkar an kwaza mishi ruwa bokati ɗaya.
Wani irin karkarwa jikin shi, ya farayi yana tsuma yana ɓari, gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi.
wanda duk fulanin wurin suka fahimci cewa tabbas.
Zai iya cinye gasar zai kuma iya faɗuwa.
Shi kuwa Sheykh Jabeer daga can cikin naman jikinshi yake jin jikinshi na rawa tamkar mazari.
Zuciyarshi kuwa wani irin duka takeyi, wanda muddin kana kusa dashi zakaji yadda take bada sautin harbawa.