← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 142

Sashe 104

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan duk sun zaunane, Ummi, ta miƙe da nufin saka musu abincin.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta miƙe tare da cewa.
"A a Ummi ki huta bari in saka mana".
Foodflaks ɗin dake kusa da ita ta ture tare da jawo wanda suka shigo dasu.
Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Ya kika ture wancan?".
Baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
"Uhummm wai fa Gimbiya Saudatu ce, ta turowa amarya abinci dan salon munafurci".
Wani irin kallon ƙasa-ƙasa Shatu tayi mata tare da zuwa abincin data buɗe ido, cikin mgnar zuciya take cewa.
"Uhumm wai zata cewa wata muna fuka, muguwa Itan ko meye sunanta!?".
Sai kuma ta kalli Umaymah jin tana cewa Juwairiyya.
"Ni zubo min na gidan Hajia Mama naga tuƙeƙƙen tuwone da biyar zogale".
To Aunty Juwairiyya tace kana ta zuba mata.
da sauri Shatu ta ɗan kalli Umaymah lokacin da aka saka mata mal-malan tuwon farar ɗanyar shinkafa,
tare da miyar a side sup.

Sai kuma ta juyo ta kalli Hibba da Ummi da tuni sun ja plate ɗin da Aunty Juwairiyya ta saka musu. Couscous and vegetables sup, mai ɗan karen kyau da ƙamshi.

Da sauri ta jujjuya kanta lokacin da Aunty Juwairiyya ta turo mata na plate ɗin gabanta, cikin sanyi tace.
"La da baki saminba". Da mamaki Umaymah tace.
"Sabida me?". Sunkuyar da kanta tayi tana tunanin.
suma ta yaya zata hanasu cin abincin. jin Ummi ta kuma mata tambayar da Umaymah tayi matane yasa ta ɗan kallesu.
Ta buɗe baki zatayi mgnar kenan.
Sheykh ya shigo da sallama, a bakisa.
kusan a tare, suka amsa masa.
A fakaice ya ɗan kalli Aunty Juwairiyya kana yace.
"Kije ki bawa Ya Jafar mgninshi".
To tace tare da miƙewa da sauri ta fita.
Ita kuwa Shatu, wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauƙe.
Kana tasa hannunta ta ture plate ɗin gaban Umaymah tare da jawo na gaban Ummi da Hibba,
Ido suka zuba mata cike da mamaki.
Ita kuwa cikin sanyi ta kallesu tare da cewa.
"Dan Allah kada kuci wannan abincin.
Kuci wancan ne".
Jabeer dake ƙoƙarin shigewa falonshi ne, a ranshi yace.
"Uhumm lallai kam wannan abun wato itace ma zata zaɓa musu abinda zasuci".

Hibba kuwa da sauri tace.
"Aunty Shatu abincin gidan Gimbiya Saudatu fa kike cewa muci."
Ganin kallon mamaki da tuhuma da Umaymah da Ummi keyi matane yasata yin ƙasa da kanta cikin jin tausayinsu a ranta tace.
"To in bazaku cishiba, Umaymah bari ni in shiga kitchen nida Hibba yanzu zan girka muku duk abinda kukeso".
Ko inda suke Sheykh Jabeer da yanzu ya fito zai wuce baiba, yacewa Umaymah.
"Zan fita".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya, ya bada Sa'a".
Amin Amin yace, hakama Ummi tai mishi addu'a.

Ita kuwa Shatu kanta na sunkuye,
Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin nazartan yanayin ta, da yin tunani hakafa ɗazuma taƙi shan madarar Barka da shigowa masarautar Joɗa da Hajia Mama ta bata,
ta kuma amshi tuppar da Gimbiya Saudatu ta bata,
yanzu kuma tace kada suci abinci Juwairiyya.
Wannan abun shi yafi komai tsayawa Umaymah a rai.
Yaya daga shigowarta zata kasabto wasu hasashen a ƙwaƙwalensu.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Hibba sa mana abincin Gimbiya Saudatu, muci".
Jin hajane yasa Shatu jawo Foodflaks ɗin ta fara saka musu.
Ita kuwa Hibba ta kwashe plate ɗin da Juwairiyya tasa musu ta kaisu kitchen.

Nan sukaci abincin kowa da abinda ke ransa.

Ita Shatu bataci na kirki bama.
Sabida ta lura da kallon da Umaymah keyi mata kamar da tuhuma.

Suna gamawa suka tattare wurin ita da Hibba.
tuni su Umaymah kuwa suna falon.

Suna gamawa suka fito falo.
da sauri ta kamo hannun Hibba suka wuce falonta har bedroom ɗinta.

Suna shiga Haroon, Jamil, suka shigo.
Shigarsu ba jimawa Jalal ma ya shigo.
Nan sukayi ta hira.
to ganin yanzu ta shigane yasa Umaymah bata kirata dan tazo taga ƙannen mijin mataba.

Suko. Suna cin abinci suka fita sabida kiran sallan la'asar,
daga nan kuma basu kuma shigowa falonba sai kusa goma na dare kafin nan kuwa tuni Shatu da Hibba sunyi bacci ma.

Washe gari ranar Laraba, da safe.
Aunty Juwairiyya ta shirya musu breakfast kamar yadda ta saba, koda su Umaymah basa nan, abincin Sheykh a sashinta yake duk da ma, yakan iya wata biyar baisa abincin nata a bakinshi ba.
sai dai Ummi Jakadiyarsu ta ɗan dafa mishi irin ababen da yafi so yaci lokuta da dama kuma na rayuwarshi da Lamiɗo yake cin abinci a Side ɗin kakarsa Gimbiya Aminatu shiyasa bai fiye cin wanda ake kawowa sashinsa ba.
Jalal Jamil Ummin suke cin wannan abincin.
To sashin Hajia Mama kullum za'a kawo Side ɗin shi.
Hakama gidan Barrister Kamal da Dr Aliyu yawanci suma sunasa ana kawo mishi.
kana gidan Baba Nasiru ma,
yawanci ana kawowa.
Especially kamar yanzu da su Umaymah ke nan.

To yauma haka abin yake tako ina an kawo musu breakfast, na maraba da zuwan amarya.

Koda suka zauna cin abinci.
Kamar jiya da dare, haka yauma Shatu ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya cikin hikima tace.
"Aunty Juwairiyya asaka mana na gidan Gimbiya Aminatu".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Wato kema irin mijin nakine, kuna son girkin Gimbiya, kunsan nata yafi naku na zamani daɗi da lfy".
Murmushi Shatu tayi cikin jin sanyi da daɗin basu fahimci manufarta ba.

Sun fara ci kenan.
Jalal Jamil suka shigo.

Dama Haroon, Ya Jafar, oga Sheykh Jabeer suna falonshi.
can Ummi ta kai musu nasu karin.

Cikin murmushin Umaymah tace.
"Yauwa Jalal kuzo nan, kuga Aunty Amaryankun."
Matsowa gefenta Jalal yayi tare da kallon Shatu a fakaice kana yace.
"Uhumm aini na santa, taje ta tasa min ɗan uwa gaba har cikin Office dinshi tana mishi ihu a kai".
Cikin sauri ta ɗan kalleshi tabbas ta ganeshi ta kuma tunashi Umaymah ta ɗan kalla tare da cewa.
"Sherri ne, Umaymah ni banyi ihuba".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh ai ba ihun kukaba, shi da mijin naki duk bauɗaɗɗun mutanene, da zaran kin ɗan yi musu mgna da murya a sama to cewa sukeyi, wai kayi musu ihu".
Ya ƙarishe mgnar yana kallon corridor fitowa falonshi.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Ga baki ga tsoro".
Aunty Juwairiyya ce ta nuna musu wurin zama tare da fara zuba musu abincin.
Ita kuwa Shatu murmushi kawai ta ɗan yi, sai taji hawaye na neman cika mata ido.
Zamansu hakan ya tuna mata yayunta, ko ina suke? Wani hali suke ciki? Ko ya jikin Ummeynta? Ya Junainah keyi da kewarsu.
Ba ya Lado, Babu Ya Gaini, Babu Ya Seyo, babu Ya Giɗi, sannan nima an kawoni nan an cusani cikin wani irin bahagon gida mai wuyar ganewa".
A hankali tasa tafin hannunta tana share hawayenta cikin hikima.
Ɗan juyowa tayi ta kalli. Umaymah dake cemata.
"Shatu, ga Jalal da Jamil tagwaye ne, sune ƙannen Sheykh Jabeer da suke binshi
yanada wasu ƙannen Affan baya ƙasar.
Sai Imran ɗan amaryar Hajia Mama mom.
sai kuma yayunsu mata, kin san su ai ko? Rumaisa da Rumana".
A hankali ta gyaɗa kai alamar eh.
Ita kuwa Umaymah su Jalal ta kalla tare da cewa.
"Ga Auntyn ku, matar Hammanku".
Jamil ne ya ɗan yi dariya tare da cewa.
"Allah ya ɗaiyiba".
Murmushi sukayi tare da cewa.
"Amin Amin."

Nan dai sukaci sukasha kana suka dawo falon.

Kamar jiya haka yauma suka wuni.

Umaymah da Ummi na yawan yi mata dukkan bayanin komai na Side ɗinta.

Washe gari ranar. Al'hamis, da yamma taja Hibba suka koma falonta.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Yauwa Hibba sammin wayarki.
Wallahi na nemi tawa har na gaji ban ganiba tun a Side ɗin Gimbiya Aminatu".
Da sauri Hibba tace.
"Dama kinada wayane? Kuma ya ɓata baki faɗawa Umaymah".
Da sauri ta jawo hannun Hibba tare da cewa.
"Ina zakije?."
"Zanje in gayawa Umaymah mana".
Ta bata amsa tana cire code ɗin wayarta-ta tare da miƙa matashi, da sauri tace.
"A a ki bari ke dai bani aron taki bari in kira Bappa na".
Ajiye mata wayar tayi bisa cinyarta kana ta wuce ta fita.
Ita kuwa Shatu, da ido ta rakata, jin tana ta rabkawa Umaymah Kira tun kafin ta fita.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare dasa hannun ta ɗauki wayar.

Jujjuya wayar tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta.
Number Bappa ta saka, kana kirashi.
tare da kara wayar a kunne mugu ɗaya ana biyu, aka amsa kiran.
Wani irin murmushi tayi jin muryar Junainah tana cewa.
"Bappa! Bappa ga wayarka ana kiranka".
Da sauri tace.
"Ƙanwaliya".
Cikin wani irin mamaki da jin daɗin Junainah tace.
"Laaaaah Adda Shatu, kece? Ina kike? Adda Rafi'a tazo jiya wai tana neman wayarki baya shiga, Bappa yace mata ai anyi miki aure, taita kuka tace to ya batun karatunki,
Bappa ma ya nemi number ki baya shiga.
Ina kika ajiye wayar ne to Adda Shatu".
Cikin sanyi tace.
"Wayar ta ɓata ne Junainah".
Cikin tura baki tace.
"To mijinki ya saya miki mana".
Ido ta lumshe tare da cewa.
"Ina Ummey na? Ya jikinta?".
Cikin sauri tace.
"Ummey tana na Kitchen, yanzu jikinta da sauƙi tana mgna kaɗan-kaɗan, ko ɗazuma itace tace.
"Bappa ya kira mata ke!."
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah, kai mata wayar".
Da sauri ya juya ta nufi kitchen tana cewa.
"Ummey! Ummey ga Adda Shatuna".
Da sauri Ummey ta fito, ta amshi wayar.
Cikin murya mai cike da sanyi tace.
"Aysha na!".
"Wasu zafafan hawayene, suka zubo mata,
Cikin rawan murya tace.
"Na'am Ummey na! Ya jikinki?".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Jiki da sauƙi, Shatu yaushe zaki zo?".
Chapter 104 · 0% Book details