← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 142

Sashe 77

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wani murmushi tayi mai cike da taraddadi da al'hini da nazarin yadda zataga bayan wannan yaron mai bakin tsiya.
Jaridar gabanta ta miƙa mishi.
Kanshi ya girgiza tare da kaɗa mata yatsarshi manuniya cikin rashin tsoro da ƙasaita yace.
"Ba kifa kai matsayin da zaki nuna min wani abin da idanuna basu rigaya sun ganiba ko basu san dashiba domin ke a makance kike rayuwarki, Ni kuwa nan da kike gani idona buɗe suke ras.
Ita wannan itace tayi bayanin abinda ya faru na gsky a Rugar itace tai bayanin cewa bulalin shaɗi akayi min bana Haddiba to sai me kuma!?".
Shiru sukayi gaba ɗayansu.
Kowa da abinda yake nazarta a ranshi sai bugawar da zuciyoyinsu keyi.
Buɗa al'kyabbar jikinshi yayi tare da kuma haɗe ta cikin fillanci yace.
"In kun gama ihun ku ficemin daga Side ɗina Dan ba haɗamu akayi ba. Kuma ku sani (MOH ALLAH WUJI FURƊATA)."
Yana faɗin haka ya juya ya nufi falonshi.

Ita kam Gimbiya Saudatu ta cika tayi maƙil.
Baba Nasiru da Baba Basiru kuwa,
A kufule suma suka fita.
Haroon kuwa ido ya zuba musu.
Barrister Kamal kuwa murmushi yayi mai tarin ma'anoni kana shima ya fita Sulaiman na biye dashi.

A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici tace
"Banza kawai me tsoron zuci me dan ya matso kusa dakaii ka wani firgita ka razana har ɓari jikinka keyi ka miƙa mishi jaridar, da zamu iya kaita a tallata".
Wani irin wawan ajiyan zuciya Laminu yayi tare da cewa.
"Uhummmm Umma kenan wato, fa duk wannan kumfar bakin da kikeyi abinda yasa kike yinta da jin daɗin yinta, dan wancan Jabeer ɗin bai taɓa kifa miki bari bane shiyasa.
Wallahi Allah da ya taɓa marinki da waɗannan hannayenshi da kike ganin taushinsu kamar na jarirai shakka babu, wlh suma zakiyi sai an yayyafa miki ruwa".
Cikin kufula Baba Basiru yace.
"Kai tafi daga nan banza mai zuciyar mata, ji abinda kake cewa kan mari ɗaya tak daya taɓa yi maka".
Wani irin kallo Laminu yayi musu kab lokacin da suka shiga falon Gimbiya Saudatu.
Cikin rumtse idonshi sabida tuno marin da Jabeer ya kifa mishi randa yayi gangancin zai zageshi.
Da sauri ya buɗe idanunshi cikin kara yace.
"Yesss sabida baku ya shararawa mari ɗayanba shiyasa.
Kuna sanefa mari ɗayan da yayi min. A take kunnena ya rinƙa zubda jinin da Ni dai har yau bansan ta inda ya ɓulɓuloba, wlh Allah lokacin daya mareni kusan suma nayi, har yau in na tuno marin sai inji kunnena yayi gummmmm".
Cikin zafi Gimbiya Saudatu ta yunƙuro zata surfawa ɗan nata masifa, sai ta kuma komawa ta zauna jin Baba Nasiru na cewa.
"Uhummm Dafa gskyar Laminu, in dai Jabeer ya ɗauki hannun mahaifinshi to tabbas, suna da zafin hannu mai ban tsoro,
In dai ya gado hannun Ya Habibullah to fa duk abinda suka mara wlh in dai dabbace sai dai a matso mata da wuƙa, in kuwa mutum ne to, tabbas zai sha azaba mai raraɗi.
In jifa ne ma sukayi ma basa saɓawa saiti sai sun samu abin harinsu, in kuma tsuntsune ko ƙananan halittu tofa in suka harba sai lahira."
Sai kuma ya ɗan tsaya ya kallesu cikin dakiya yace.
"Munada buƙatar sabon shiri, akanshi, zamuyi mgnin bakinshin nan da baya mutuwa".
Cikin takaici Gimbiya Saudatu tace.
"A duk cikin ababen da ake dangantawa dasu babu, abinda yafi cimin rai kamar meda, zoo ɗin masarautar sade ɗin Jabeer.
Wlh duk sanda najiyo kukan Ɗawisun Masarautar da sauran tsuntsaye nakiji kamar in je in samisu shinkafar tsuntsaye suci su mace kab ɗinsu kowa ma ya huta."
Barrister Kamal dne dake,
Jinsu ta window ɗin falon.
Ya jinjina kai tare da jan hannun Sulaiman suka tafi yana mai cewa.
"Uhum naku burin dai baza taɓa cikaba in sha Allah".
Su kuwa nan sukaci gaba da tattaunawa yadda shirunsu a kanshi zai kaya.

Jakadiyarsu kuwa saida taga fitansu ta sauƙe ajiyan zuciya.
Jafar kuwa saida yaga Barrister Kamal ya fita kafin jikinsa ya dena rawa da karkarwa.

Shi kuwa Haroon da sauri yabi bayan Jabeer cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
"Wato kai bakinka bazai mutu bako."
Cikin kufula ya juyo ya kalli Haroon jin ya yace mishi irin
Abinda kullum Abba yake cemishi.
A hatsale yace.
"Eh bakina bazai mutuba ba kuma zan bar ko wanne taƙadirinba, duk wanda yace dani tak zai samu amsa dai-dai da zancensa.
Wannan zarerriyar matarfa ta kiyayeni, kadafa ta fusatani, tam!".
Ya ƙarishe mgnar da taune lips ɗinshi.
Cikin sanyi Haroon yace.
"Nifa tsorona ɗaya Jabeer kada su cutar da kai, so dan Allah duk abinda zasuyi maka kosu Jalal da ya Jafar kada ka tanka musu.
Yanzu wannan sharrin ya zamuyi dashi?".
Wani irin kallo yayiwa Haroon cikin sauƙe numfashin yace.
"Tuni na magance ta, na saye jaridun, tun kafin a fiddasu, shima dan ya ɗauka ne tun kafin inji inje wurin.
Kuma gashi shima a hannun yanzu sai dai su nemo wani sharrin. Kuma batun basu amsa, da sun gane sun dena sako Mahaifiyata a duk abinda zasuyi min da Ni dai ko kallo basu isheni ba."
Cikin sauƙe numfashin Haroon yace.
"To Alhamdulillah Allah ya kare gaba".
Amin yace tare da zama bisa kujerarshi ta musamman wacce take kyautace ga Sheikh Abdulkarim. Tab ɗin shi ya ɗauka ya fara wasu yan dube-duben.

Anan falonshi suka zauna, shida Haroon.
Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace.
"Yauwa Gimbiyar Lamiɗo kizo kiyiwa wannan jikan naki faɗa".
Murmushi tayi mai ƙayatarwa,
a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi.
A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna,
cikin sanyi ya kalleta.
Ita kuwa cikin kulawa tace.
"Jabeer, ya jikin naka".
Cikin harshen fillanci yace.
"Da sauƙi".
Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace.
"Yaci wani abu kuwa?".
Da sauri yace mata ehh.
Cikin kula tace.
"Me yaci!?."
Murmushi yayi cikin tsokana yace.
"To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa".
Dariya ta ɗan yi tare da cewa.
"Taso kuzo kaci abinci".
Kanshi ya girgiza mata tare da cewa.
"Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina.
In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka".
Murmushi tayi tare da cewa
"To naji taso muje kaci wani abun".
Dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima suka shigo.
Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.

Bayan sun zauna ne Lamiɗo yace.
"Ya ƙarfin jikin?".
Rai a ɓace yace.
"Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani".
Murmushi Lamiɗo yayi cikin tsokana yace.
"To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?".
A hatsale yace.
"Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin."
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama".
Da sauri ya ɗago kanshi daga kallon Tab ɗinshi ya zuba musu tare da nuna kanshi.
Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace.
"Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin.
Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba."
Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaɗarshi tare da cewa.
"A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah".
Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru.
Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.

Bayan sun tafine.
Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya ɗanci abinci.

Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.

A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa.
Saida akayi sallan la'asar kafin suka isa sashin, Jabeer.
Sosai suka nuna mishi kulawa da gata,
Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole.
Hajia Mama kuwa daɗi kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.

Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.

Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.

Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.

A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.

Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu
Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.

Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma.

Yau kwana biyar da faruwan abun.
Sosai jikinshi yayi ras.

Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.

Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba'ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.

Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani.
Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.

Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin.

Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.
Chapter 77 · 0% Book details