← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 142

Sashe 142

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ganin yadda hannunta yaketa karkarwane yasa ya tayata tura ƙasar saida suka gyara komai fes kamar ba fasawan ganganci akayiba.
Kana ta miƙe tare dasa hannun hagunta ta riƙo na damanta tana cewa.
"Shima Yah Sheykh dole zaiji wani abu a jikinshi duk inada yake".
Sai kuma tayi shiru tare da rumtse idanunta tace.
"Wash hannuna".
Cikin sauri Ummi tace.
"Sannu hannun ya gaji ko".
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.

Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.

Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.

Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al'ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina".
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
"Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba."

Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
"Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Allah ya miki al'barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba".
Amin Amin tace kana ya katse kiran.

A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin...!

By
*GARKUWAR FULANI*
Chapter 142 · 0% Book details