← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 142

Sashe 117

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin turo baki ta harari gefen fuskarshi, kana ta ɗan rusuno a hankali ta zauna.
Bakin kujerar dake bayanta.
Cikin muryar ƙunƙuni tace.
"Bacci nakeji".
Bai kulata ba, sai ma gyara zamanshi da yayi ya nuna mata plate ɗin gabanshi.
"Cikin cinna bikin sama tace.
"Bana gane kurmanci".
Juyowa yayi ya watsa mata narkakkun idanunshi da bata iya gano meke cikinsu cikin nata.
Karon forko kenan data ga zahirin yadda kalar ƙwayan idonshi suke, sosai kwarjinshi da haibarshi ya danne tsiwarta, a hankali ta matso kusa da inda yake.
Rusunawa tayi har ƙasa a hankali ta buɗe plate ɗin data shirya mishi Chechen balls da ganyen Fork ta ajiyeyi mishi gefen plate ɗin kana tasa hannun zata ɗauki flaks alamun zata samunshi tea a cup ɗin.
Yatsarshi manuniya ya ɗan ɗaga tare da kaɗa mata ƴatsar alamun bai sataba.
Yamutsa fuska tayi tare da turo baki cikin yin ƙasa da murya can cikin maƙoshinta tace.
"Karkaci ma in kaga dama".
Ta gefen idonshi ya kalleta ba tare da ya juyoba yana kallon yadda takeyin mamul-mamul da lips ɗinta,
Gyara zamanshi yayi tare dasa hannun ya ɗan ɗauki Fork ɗin Chechen ball ya ɗan soka
kana ya ɗago alamun zai kai bakinshi sai kuma ya maida cokalin ya ajiye.
Ɗago kanshi yayi ya zuba mata ido na 3 second kana ya nuna mata idonshi tare da lumshesu alamun ta rufe idonta tako gane abinda yake nufi.
Cikin gunaguni tace.
"Nifa zan tafi bacci nakeji, ba sai na rufe idona a nanba zan tafi kaci abinci k".
Shiru tayi ganin kallo da yake mata da mayun idanunshi.
tura bakin tayi tare da sunkuyar da kai kana ta murguɗa bakin.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, numfashin ya ɗan fesar kana a hankali ya muskuta ya gyara zamanshi, kaikaicewa ya ɗan yi yasa hannunshi cikin al'jihun jallabiyarsa. rafan dubu-dubu sabbi dal-dal ya fito dasu guda shida.
Miƙo mata su yayi.
Hannunta ta miƙo a hankali ta amshi kuɗin.
Gyara zamanshi ya kumayi kana yasa yatsunshi biyu ya jawo ɗaya plate ɗin ya rufe ɗayan.
Tsuke fuskarsa yayi da kyau tare da kafeta da ido cikin kakkausar murya yace.
"Yau zanyi tafiya daga yanzu, zuwa ƙarfe biyu. Duk inda naje inada lbrin gidan nan duk abinda zakiyi zan sani, duk motsin masarautar Joɗa.
Saboda haka ki kiyayi kanki da yiwa mutane tijara,
Bana son fitsara da rashin sanin darajar manya, ki tsaya matsayinki, bana son shishshigi cikin al',amuram rayuwata.
Ki kuma kiyayi murguɗa wannan bakin fitsarar in ba hakaba wata rana in kin murguɗa minshi bazai dawo dai-dai ba haka zai zauna a murguɗe a karkace, Allah ya nuna miki matsayi da darajar miji."
Ƙasa tayi da kanta tare da cewa.
"Kuɗin na meye ne".
A daƙile yace.
"Na yagawa ne, kije ki yaga ki zubdasu".
Kallonshi ta ɗan yi ganin hankalinshi baya kantane, ta miƙe tsaya ta juya ta fita.
Shi kuwa bayanta yabi da wani irin kallo.

Sosai yaci Chechen balls ɗin dan yayi daɗi sosai, kuma gashi rabanshi da abinci tun jiya iwar hakan, dan haka yaci iya abinda zai iya ci, kana ya miƙe yaje yayi wonka ya fara shiryawa.

Ita kuwa Shatu tana fitowa a falo ta samesu gaba ɗayansu harda Ya Jafar da Aunty Juwairiyya da kuma. Su Jalal da Hajia Mama.
ganin hakane yasa ta ɗan juya ta nufi falonta bedroom ta wuce taje ta ajiye kuɗin sannan ta fito.
Gefen Ummi ta zauna kusa da Hibba suka ɗan fara hira da Hibba ko inda Mama take bata kallaba.

Can ya fito cikin shigarsa ta yau da kullum.

Da sauri Jalal ya miƙe ya amshi ƴar Kekkyawar jaka ta maza dake hannunshi.

Dai-dai lokacin kuma Ya Hashim ya shigo tare da cewa.
"Sheykh mu tafi lokacin yana ƙurewa".
To yace kana ya kalli Ummi, Mama, Aunty Juwairiyya, Hibba, yace.
"To zamu tafi".
Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa.
"Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy".
Amin Amin sukace.
Ƙwayar idanunshi ya ɗan juya ya kalli inda take ba tare da kowa ya gane ya kalletanba, kana suka juya suka tafi nan su Jalal Jamil duk suka fito dan sune zasu kaisu Airport.

Daga nan suka tafi sha biyu dai-dai jirginsu ya tashi a international airport Ɓadamaya.

Sai kusa ƙarfe ɗaya su Jalal suka dawo,
Sosai suka mamakin wannan karon Ya Jafar bai ce zaibi Sheykh ba.

Haka dai rayuwa tai-ta juyawa sa'a da wuni yau azumi ashirin ne aka kai wanda bahaushe ke cewa an gama goma na wuya za'a shiga na ɗokin salla.
Tunda Sheykh ya tafi baiyi mgnar da kowaba a cikinsu har yau kwanansa biyar.

Yana can ƙasa mai tsarki ibada tayi daɗi baya tuna kowa baya tuna komai sai kusanci yake nema da yardar mahalinsa.
Ko bacci Allah ya yaye mishi sai yayi baccin awa ɗaya zuwa biyu a wuni daga wannan kuma ya gamsu.

Kullum a a masallaci yake kwana.
In gari ya waye sai yayi walahanshi yayi karatun awa biyu, sai ya tafi gidan ƙanan Sitti dake nan Madina wanda shidasu Baba Kamal duk nan suka sauƙa.
to a nanne zai ɗan yi bacci.

To yau kuma shine daren da za'a fara tuhajjudi kuma sannan yaune suka baro Madina suka iso makka.
Kai tsaye gidansu Sitti suka wuce.
Nan suka samu itama Sitti da ahlinta sun iso, Umaymah ma da Haroon yau suka iso.
Kana Ibrahim ma da ahlinshin sun iso daga ƙasar Cairo sosai Sheykh Jabeer yaji daɗin hakan.
Yau ɗin kuma
Yana ɗaya daga cikin dararen da ake tsammanin laylatul Ƙadir.

Kasan cewar babbar zuriya yake.
Sheykh Jabeer Ali, ɗane ga Sheykh Ali jikan Sheykh Abdulkareem kenan,
Wanda sunanshi aka sawa Jabeer.
Yana matuƙar son Jabeer sosai.
Hakan yasa tare suke shiga harami tare suke fitowa.

A nan gida Kautal kuwa hada-hadan jama'ar musulmai na tafiya bisa tsarin addinin musilunci kowa na shirin salla da kuma tarban wannan kwanaki goma na ƙarshe.

Yau miyar shuwaka sukayi da tuwo.
Suna gama kimtsa komai ne suka dawo falo.
Tv suka kunna suna kallo, suna ɗan hira.
Gyara zama Ummi tayi tare da cewa.
"Lallai yau in munyi garaje zamu makara".
Da sauri Shatu tace.
"In sha Allah bazamu makara ba, wannan uban bindigar da kukace in lokacin sallan Tuhajjudi yayi zava bugata ai zata tashemu".
Hibba ce ta ɗan gyara kwanciyar ta, tare da cewa.
"Kalli lokacin shabiyu saura yanzuma za'a fara, Ummi kai mana Tashar Saudi".
Ta ƙarshe mgnar tana kallon Ummi da Rimote ke hannunta.
To Ummi tace kana ta. Juya musu tashar.
Inda suka samu tuni sun fara sallan Tuhajjudi.
Inda ake nuna harami kai tsaye.
Shiru sukayi suna kallon yadda haramin ya cika yayi maƙil da al'ummar Annabi.
Kab an nitsu bakajin komai sai sautin muryar limamin dake karatun al'ƙur'ani cikin zazzaƙar murya mai daɗin sauraro.
Koda aka tafi ruku'u gaba ɗaya a tare aka sunkuya hakan yasa abin yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali.
Sun jeru tamkar zanen fefeyi.
Hakama da suka tafi sujjada.
Musamman da yake cameran ɗaukar sama akayi.
Suna ɗagowa kuma aka juya cameran ya fuskanci limamin da sauran mamu na sahun forko wanda duk manyan malamai ne.

Cikin wani irin kallo Hibba ta miƙa da ƙarfi tare da...!Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond da yayiwa wurin labule.
Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ƙafar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya.
A hankali ta ɗago ƙafarta tare da take step ɗin forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba ɗaya sam ganinta baya gaba.
Cikin rashin sa'a kafar ta tsallake step ɗin forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ƙafar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba.
Wani ƙara mai ɗan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran taji ta ina ɗin ta zai karye.
Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faɗi gib a kan stpes ɗin kanta ya bugi dandamalin sama.

A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice,
Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray'n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau.
Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne,
ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu'o'in buɗa baki.
Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki.

Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa.
"Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse".
Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa.
Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa.
saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi.
Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray'n gefe.

Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma.
Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta.
Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam.
Chapter 117 · 0% Book details