← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 142

Sashe 92

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hankalin Ba'ana yayi ƙololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba'in da biyar.
Baiyi ɗaya daga cikin ababen da zai hanashi cin gasar ba.
Ganin hakane ya juya a fusashe, bulalin hannunshin ya wurgar kana ya sunkuyo kam ranɗar bulalin tsafinshi, bulali biyar ya zaro, ya haɗa su ya damƙesu cikin hannunshi.
Cikin azaban ƙarfi ya ɗagosu ya yarfawa Jabeer su a tsakiyar kanshi.
Wani irin azabane ya ziyarci ƙoƙon ranshi, wanda hakan yasa yaji wani irin fitsarin azaba yana cika mishi mara.
Jinine ya tsinko ta kafaɗunshi, yana bin cikinshi,
bai gama jin azabar waɗannan ba ya kuma zarma mishi su a cinyoyinshi.
Da sauri Arɗo Bani ya miƙa tsaye daga sujjadar da yayi jin ihun mutane, suna cewa.
"Ka karya dokar gasa ba'a haɗa bulali biyuma bare biyar kasheshi zakayine.
Cikin wani irin isa ta jarumta da jinin sarauta Sheykh ya buɗe kwayar jajayen idanunshi,
Barmuji da yayi kansu da nufin kama hannun Ba'ana ne,
Ya ɗagawa hannunsa alamun daka dakatarwa alamun ya tsaya kada ya iso ya bar Ba'ana yayi komai ba komai.
Cikin tsananin mamaki duk al'ummar wurin suka zuba musu ido ganin jarumta ziraran miraran tana tsaye da sawunta.
Shi kuwa Barmuji cikin rauni yaci gaba da nufosu yana cewa.
"A a Sheykh bazan barshi ba, ai ya karya ƙaida da dokan gasa".
Ya ƙarashe mgnar yana isowa inda suke.
Cikin tsananin takaici da firgicin ganin faɗuwa a karo na forko na rayuwarshi, Ba'ana
Ya zargawa Barmuji bulalin da ƙarfi.
Wani azabebben ihu Barmuji ya narka tare da fara tsalle yana yarfa hannunshi yana zagaya wurin hawaye na shatata mishi sabida azabar da yakeji, cikin ihun azaban bulalin da aka yarfa mishi sau ɗaya, fitsari na tsiyaya a sawunshi yace.
"Arba'in da takwas!".
Ta gabanshi ya dawo ya shauɗa mishi na arba'in da tara, wanda yasa Jamil yin tsalle yazo gabanshi cikin kuka yace.
"Kasheshi zakayi ne?". Cikin tsananin azabar da yakeji ne ya buɗe jajayen idanunshi ya kalli ta inda yaji muryar Jamil.
Hannunshi yasa ya ture Jamil gefenshi.
Shi kuwa Ba'ana wani irin ihu yayi tare da buga tsalle yayi sama kana ya zabga mishi bulala ta hamsin kuma ta ƙarshe.
Wani irin dogon numfashi Jabeer yaja tare da buɗe idonshi kan fuskar Lamiɗo daya iso hango dishi-dishinsa yana nufo inda suke.
Wani irin ihu da karaji Ya Salmanu ya kurma da azaban ƙarfi,
Wanda ya haɗe ya gauraye da busar sarewa da al'gaita da dukan gamgar jami, aka saki a tare.
Wani irin sowa da ihu da hargowane ya cika illahirin gaba ɗaya Rugar Bani,
Wanda mutane fulani suketa rawan farin cikin jarumtar Jabeer,
Arɗo Bani da sauran dattawan rugar kuwa gaba ɗaya sujjadar godiya sukayi wa Ubangijinmu sarki gagara misali.
Gaba ɗaya an zagaye Sheykh Jabeer.
Wanda shi kuma ya juyawa Haroon baya alamun yasa mishi suturarsa.
Da tsananin rawan jiki.
Haroon ya wore al'kyabbar, ya zura mishi ita kan jikinshi daketa zubda jini.
Yana jin Haroon ya saka mishi Al'kyabbar ya ɗago kafaɗunshi ya gyara zaman al'kyabbar.
Jiki na rawa yasa hannunshi ya kama gefe da gefen bakin al'kyabbar ya hadesu a jikinshi ya suturce kanshi ya kare kanshi.
Barmuji na shirin kamo hannunshi yayi maza.
Ya ɗaga mishi hannunshin kana ya juya ya nufi inda motoncinsu ke jere.
Jalal da na ganin haka yayi maza yayi gabanshi.
Marfin motar ya buɗe mushi tun kafin ya iso.

Cikin taron kuwa, tuni Ba'ana da matasan ƙabilar ɓachama, sun ɗauki ranɗar bulalin tsafinshi sun nufi Bonon da tarin baƙin ci dan ganin Sheykh Jabeer bai faɗi gasarba, kuma ga mutanen fulani daketa yi musu dariya da ihun rashin nasarar su.
Hakan yasa suka tafi dan sun sani a ƙa'ida sai Jabeer yayi jinya ya worke da azabar da Ba'ana ya shayar dashi kafin ya dawo ɗaukar fansa.

Cikin taron kuwa cikin kukan rauni Arɗo bani ya rusuna gaban Lamiɗo da tawagarsa murya na rawa yace.
"Sauran ɗaukar fansar da zaiyi a duk sanda ya worke a duk sanda yaga dama, fatana kuyi shirya bulalin tarihin masarautarku, domin ramuwa akan wancan taƙadirin da baya jin koda harbin bindiga baya shigarsa.
Ina yakun farin cikin nasarar da Jabeer yayi a yau, ina kuma fatan yayi nasara a ramuwar da zaiyi a wannan kuma in yayi nasarar mu zaku taya farin ciki, ko ba komai zamu rabu da wancan taƙaɗirin."
Cikin wani irin tarin ƙuna Lamiɗo ya gyaɗa kanshi.
Kana ya juya yayi gaba Dogari na rike masa da laima ɗanzagi na cewa.
"Gyara kimtsi, a bada hanya, sarki ya barku lfy".
Waziri da Wambai Ɗan buram Ɗurɓi Da iya duk suka mara mishi baya.

Hakama Arɗo Bani da sauran dottawan wajen sukayo musu rakiya.
Sheykh Jabeer kuwa.
Yana tafe Galadima na biye dashi a baya. Haroon kuma na gefenshi.
Suna isa yasa kai ya shiga cikin motar,
kana Haroon da Hashim suka mara mishi baya, da sauri sarkin mota ya maida ƙofar ya rufe.
Kana ya buɗewa Lamiɗo motar, gefen bayansu Jabeer ya shiga, kana Galadima ya shiga kusa dashi, sannan aka rufe motar saura duk kowa ya shiga motar da yazo ciki.
Sannan duk suka rurrufe motocin.

Kana suma Fadawa da dogarai suka shiga nasu motoci biyun.
Ɗaya tayi gaba, sauran motocin suka bisu a baya, ta Lamiɗo na tsakiyarsu, kana ɗaya ta fadawan ta biyo bayan uku da ke bin bayan ta Lamiɗo.

A haka suka ja motocin a jere a jere suka bar cikin Rugar Bani.

Cikin Rugar kuwa kowa ya tafi cikin al'ajabi da farin ciki.
Da yawa gani sukeyi kamar dai Jabeer ba mutun bane.

Sauran dottawan kuwa, zama sukayi cikin fadar bayan sunyi sallan la'asar ne, Bukar yazo ya tsaya tsakiyarsu cikin rashin mutunci yace.
"Kuyi kuka da kanku akan duk abinda zai faru gaba".
Kafin ma su bashi amsa tuni ya juya ya tafi.

Su kuwa nan sukaci gaba da al'ajabi da tuanjidin Jarumtar Jabeer.

A cikin motocin kuwa, mutanen ko wacce mota da abinda kowa ke tunawa.
Wani irin azabebben gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama, sabida bin umarnin Lamiɗo wanda shi kuwa ya bada izinin gudun ne, dan ganin yadda Jabeer keta zubda jini, ga wani irin masifeffen karkarwa da jikinshi keyi.

Gudu sukeyi a 360 musamman ma da suka samu suka hau kan babban titin Shikan wanda zai sadasu da cikin babban birnin Ɓadamaya.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, wani irin karkarwa jikin shi keyi, idanunshi jinsu yakeyi tamkar zasu zazzago su faɗo ƙasa, sabida wani irin masifeffen azaba da yakeji.
Ji yakeyi tamkar ya haɗiyi zuciyarshi sabida masifar fushi da harzuƙa da zafin rai,
babban abinda ya tsananta fushinsa shine yadda yaga lokacin sallan la'asar ya gota musu,
akan shirmen banza da wofi da zalunci an hanashi yin salla kan lokacin ta.
Hannunshi yasa ya fizge rigarshi da ke hannun Haroon dake ta sa hiraminshi yana tare jinin dake zubomishi ta ƙeyanshi.
Taune lips ɗinshi yayi tare da sa hannun shi, ya kama wuyan rigar cikin ƙarfi yaja ji kakeyi,
Fasss sautin yagewar sabon saddan.

Ido suka zuba mishi gaba ɗayansu,
Ya Hashim kuwa jiki narawa ya kira Dr Aliyu wanda yake ƙanine ga mahaifinshi da kuma Abbansu Jabeer ɗin.

A can baya kuwa inda Galadima dake zaune gefen Lamiɗo ne daya bashi umarnin ya kira sarkin gida ya sanar mishi ayi tanadin jinyar Shaɗi cikin gaggawa.
Da sauri Galadima ya zaro wayarshi ya kira sarkin gida.
Cikin tashin hankali yake mgna a woya bisa alama duk da sarkin gida yake mgn.
"Ladodo, kayi maza yanzu ka sanarwa tsohon sarkin Shaɗin masarautar Joɗa yayi maza ya haɗa tsumin igiyar bulalin shaɗi, ya kaiwa Jakadiyarsu Jabeer,
A shirya duk wani abun buƙata, domin Jabeer yana zubda jini sosai."

A can masarautar kuwa Sarkin gida yana jin haka ya miƙa ya nufi, sashin kananan sarakuna kai tsaye gefen Sarkin Shaɗin ya nufa, ya sanar mishi umarnin da aka bada,
ai nan take Sarkin Shaɗin da sarkin Gida, suka shiga bayan sashin mai martaba Lamiɗo,
inda bishiyoyin tarihi dana gargajiya da magunguna suke.
Forko bishiyar Goruba suka fara sassaƙan jikinshi.
Wanda shine babban makarin dukan shaɗun.
Sai kuma suka haɗa da wasu tsirran,. Koda suka gama kai tsaye gefen Jakadiya da sauran ma biyanta suka nufa,
Nan suka bata dukkan abinda suka ɗebo, suka kuma yi mata bayani.
Kana sukace maza ta haɗa su ta dafa,
Sauran kuma sai sun dawo Lamiɗo ya shiga ɗakin sirri ya ɗebosu.

Cikin tsananin tashin hankali da rawan jiki Jakadiyarsu ta amshi magunguna, ta nufi sashin Jabeer ɗin.
Cikin gaggawa ta shige kitchin ɗin shi, ta fara harhaɗa magunguna tana dafawa.

A can cikin motar kuwa cikin tashin hankali Ya Hashim yayiwa Dr Aliyu duk bayanin abinda ya faru da halin da Jabeer ke ciki.
Ya ƙara da cewa, a shirya komai na bashi taimakon gaggawa.
Jin hakane yasa Dr Aliyu tada motar Ambulance wanda take nan cikin asibitin dake cikin makarantar nasu, tazo bakin asalin babban gate ɗin masarautar nasu.
Kana ya kira babban abokinshi Dr Sanju wanda ba indiyene wani aikine ya kawoshi ƙasar,
tuni suka iso bakin gate ɗin, cikin motar Ambulance ɗin suka shiga suka zauna tare da haɗa duk wani abu na taimakon gaggawa da za'ayi mishi.
Chapter 92 · 0% Book details