← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 142

Sashe 21

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau jumma'a ne gajeren lokacine basa kai yamma a wurin kiwo, kafin azahar suke dawowa, shiyasa yau Shatu tace da ita za'aje kiwo.
Dariya kawai sukayi mata dan sun san ba iya jurewa zatayiba amman tunda ta kafa ta tsare cewa dole zataje, sai aka barta.

Kasan cewar basu kai yamman bane yasa kuma suna tafiya da wuri.
Bayan duk an kunce dabobbin gaba ɗaya, hakama sauran makiyayan baki ɗaya, sahu- sahu shanayen keta wucewa.

Sun tafi tun shida da rabi na safe,

Kafin zuwa tara na safe sunyi nisa cikin wurin kiwonsu, inda nan kuma Aysha ta samu su Hindema sunzo kiwo, wanda su kullum dama suna zuwa.

Wani irin hadarine mai ƙarfi ya taso daga ƙasa, ganin hakane yasa, Gaini kwallawa Shatu kira wacce take can cikin ƴan uwanta mata makiyaya, jin shiru bata amsa bane ya nufi wurin da suke zaune,
Cikin kula yace.
"Aysha tashi keda Hinde dasu Mero duk ku tafi gida, kunga hadarine mai ƙarfi ke tasowa daga ƙasa da alamun za'ayi ruwa mai ƙarfi".
Cikin ƙarfin hali da son wasa cikin ruwan da taketa hari murya a sanyaye tace.
"Ba komai ya Gaini zamu jiraku ai lokacin tashi kuma ya kusa ko?".
Su Giɗi dasu Aro da sauran makiyayan ne sukace.
"Ya Gaini barsu mana ba kiwo zasuyi ba ai makiyayin shanu da tumaki baya gudun ruwa duk yawa shi".
Cikin jin daɗi sukace, eh mana,
Shi kuwa Ya Gaini murmushi kawai yayi tare da cewa.
"Shike nan yau zakusha dukan ruwa".
Murmushi sukayi sukace "Babu matsala". daga nan mazan duk suka koma wurin kula da dabobbin nasu da suka duƙufa cin koren ciyawa.

Su kuwa Shatu da Hinde a hankali sukaci gaba da tafiya, sosai tsarin wurin da yanayin shigar suturar dake jikinta yayi tsananin dacewa da ita.
Doguwar rigace irin tamu ta fulani, yadin farine, sai daga samanshi akayi mishi kolliya da zaron huɗu, mai color red white, blue, yellow, and green, wanda aka ƙawata saman rigar da kolliyar zanen ɗawisu, inda daga kafaɗunta har zuwa saman ƙirjinta, duk an shimfiɗa zaren, bisa wuyan rigar mai V.
sai kuma hannun rigar shima duk an zagayeshi da kolliyar,
Kana sai tsakiyar rigar dai-dai kan ƙugunta shima an ƙawatashi da wannan kolliyar ulu irin namu na fulanin daji,
Kana sai ƙasar rigar can itama an ƙawata da wannan zaren.

Sai dogon gashin kanta da yake zube a kafaɗunta, yayinda daga saman goshinta kuma tasa, bandana amman irin namu na fulani mai kalolin ƴaƴan tsakiya, ta zagaye kanta dashi, sai kolliyar da tayi a fuskarta irin ta asalin fulani, a goshinta zanen kan shanu tayi, shaidar cikekkiyar bafulatanace, sai kuma ƙasan lip ɗinta na ƙasa zuwa kan ɗan gemunta shi kuma taja zane da kuma yin ɗigo-ɗigo a gefenshi.
Sai wata kekkewar jakar sakan ulun mai kalolin kolliyar jikin rigarta data rataya a hannun damanta, wanda cikin jakar kuma ruwan shantane a ciki sai sassanyan kinɗirmo da goran zuma, sai ɗan sandar mu ta gado, takalman sawunta irin sau cikin nanne daku mutanen cikin birane kuke masa laƙabi da tashi kabi shanu.
Tayi masifar kyau a cikin wannan shigar tamu ta gado, kyau iya kyau farar fatarta ta baiyana tamkar balarabiya gashin girarta ya konta lib lib.

A hankali suke ɗan tattaki a cikin dogayen saunukan, da koriyar ciyawa da tayiwa ƙasanshi ƙawanya. suna ɗan tafe
Suna ɗan tsinkar ya'yan kanya da gwandar daji da suke cike da wurin Chaɓɓulle wato tsada.

Hadari kuwa sai gamgami yakeyi gabas da yamma kudu da arewa, ko ina yayi dib babu motsin komai sai nasu dana dabobbin su,
Iska ta tsaya cak koda ganye ɗaya baya kaɗawa duhu ya kareɗe illahirin yankin.

A hankali Hinde ta kalli sararin samaniya cikin tsoron ganin gaba ɗaya duniyar tayi baƙiƙƙirin ko ina yayi dib, hakanne yasata ɗan zaro ido tare da cewa.
"Kai Shatu, kalli sama, fa hadarin nan yayi duhu da yawa gsky mu tafi gida".
Da sauri ta ɗago kanta kana tasa hannunta na hagu ta ɗan kare saman goshinta kaɗan, ware idanunta tayi ta kalli sararin samaniya, wani irin azabebben firgita da tsorone ya rufeta wanda yasa ta juya da azaban ƙarfi ta ruggume Hinde dai-dai lokacin, sukaga wani irin tartsatsin azabebben igiyar...!

Dan Allah da Manzonsa in dai kin san zaki sayi littafinane ɗan ki fiddashi na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar su. Kada ki saya bana so, ki riƙe kudinki.

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 9

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*FREE PAGE*

*TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta wannan number 09097853276 DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA littafin GARKUWA, ba tare da haƙƙin kowa a kankiba. Akwai Special Group shi kuma na 1k rak, ki turoshi ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai ta WhatsApp 09097853276*

~Ga masu buƙatar kayan gyara na amare, akwai set-set masu kyau, a ƙananan robobi masu sauƙin kuɗi, akwai kuma na manyan robobi masu zafi, akwiasu dai-dai da tsarin al'jihun mai ƙarfi da mai rauni, ina araha ina hana bashi. Koda kuɗinka saida rabonka, kayan Kamfani daban dana shago.~

*Al'ummar Hausawa mazauna Saudiya wannan shafin nakune kyauta gareku, domin jiya da yau saida mai zaton babu wasu masu karanta littafi sama daku. Nasha mamaki da sanyin safiya naita cin karo da numbers ɗin ƙasa mai tsarki suna ta antayo min manyan kuɗi na ƙasa mai tsarki tun ina ƙidaya numbers ɗin +966 har dai abun yaci tura sabida yawansu, ashe daga zauren Umar Maisanyi sukayi ta antayowa gareni. Godiya mai tarin Yawa Umar maisanyi mai Tsakar gida You tube limamin tsakar gida*

Walƙiya mai tsananin haske da tartsatsi wanda saida ya haska gaba ɗaya, dajin ya zamana, har kana iya ganin inuwar dogayen bishiyoyin wurin da sukayi musu ƙawanys.
Wani irin tsoro da firgici da karkarwan ne ya bijirowa Aysha.
Cikin dauriya da sabo da ganin ire-iren irin waɗannan ababen a wurin kiwo, Hinde ta kamo hannun Shatu tare da cewa.
"Kai Aysha babu komai fa walƙiyace kawai fa kai".
Sai kuma tayi dariya tare da cewa,
"Uhum a hakan kike tunanin jurar taraddadin da muke gani cikin tsaunuka in muna kiwo".
Janye jikinta tayi daga jikin Hinde, hannun tasa ta tattare gashin kanta dake baje a kafaɗunta, tubkeshi tayi cikin, fidda numafashin tsoro take karisa addu'o'in datake tayi a bakinta, a hankali taja da baya ta jingina da jikin ƙatuwar bishiyar Gamji dake gefensu, jingina kanta tayi jikin bishiyar gamjin tana jin yadda zuciyarta ke harbawa, pat-pat da azaban ƙarfi domin tasan Hinde bata san me idonta ke shirin hango mataba,
ita kuwa Hinde, a gabanta take tsaye ya zamana sun fuskantar juna.
Su Ya Gaini kuwa sun duƙufa kiwonsu kamar dai yadda suka saba, ruwa ko iska ko zafin rana da ƙishi baya kora makiyaye daga kiwo a daji ya dawo gida.
So duk kowa yana yankin da yake bawa dabobbin tsaro, sam basuma hango su Aysha sosai.

Ita kuwa Shatu idonta dake lumshe ta fara ƙoƙarin buɗewa sabida wani irin tashi da taji tsikar jikinta nayi.
Hinde kuwa ido ta zuba mata tana ganin yadda ƙirjinta yake sama da ƙasa alamun tsananin firgita.
A hankali ta ware manyan kyawawan idanunta.
Wani ƙaton curi, dake can bayan Hinde ta zubawa ido sabida wani abu da take gani kamar hayaƙi yana fitowa ta ƙananan ƙofofin curin. Ita kuwa Hinde bata san meke wakana ba sabida, ita baya ta bawa curin, asalima yanzu kanta ta ɗaga sama tana shan ruwan dake cikin goranta.

Ita kuwa Shatu so take ta janye idanunta daga kan wannan CURIN amman sai taji ta kasa, bugun da zuciyarta keyine ya tsananta, lokaci ɗaya jikinta ya fara tsuma da karkarwa zufa mai azabar zafi ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.
Yayin da zuciyarta. Ke harba jini one litter. A Cikin ko wanne one second. Bakinta ta buɗe da nufun furta addu'o'in dake jere a zuciyarta amman sai taji ta kasa, zuru-zuru tayi da idanunta lokacin da taga wani dogon abu yana fitowa daga cikin babban ramin dake tsakiyar CURIN nan, a hankali ta ɗaga kwayar idanunta sama tana bin abin da kallo, wani irin dogon numfashi taja, ganin abun nan yana miƙewa yana yin sama, abun dogo kamar igiya sai dai kuma yanada zane kala-kala red, yellow, green, blue.
Kuma abun biyune ɗaya a sama ɗaya a ƙasa, cikin ranta take iya ammabaton sunan Allah ganin zahiri fitowar bakan Gizo daga cikin curi Allah ya nuna mata, ras zanen bakan Gizon nan yayi kama da kalolin kolliyar jikin rigarta,
Kanta ta ɗaga sama, tana bin Bakan Gizon da kwayar idanunta, tana gani har ya haura sama can ya konta a gicciye gabas da yamma kudu da arewa, kana kuma mai hasken ras yana sama mai ɗan dishi-dishin yana ƙasa. Wanda a falsafar al'ummar Duniya ake cewa suma mata da mijine, muddin kaga mai hasken in ka zuba ido zakaga mai dishi-dishin wanda akecewa, mijin shine dishi-dishin kuma shike goyo matarsa shiyasa sai ake ganin mai hasken shine a sama.
Chapter 21 · 0% Book details