← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 142

Sashe 74

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A babban falon suka samu, Aunty Juwairiyya da Jakadiyarsu suna shirya musu abinci bisa dinning table.

Cikin kula Aunty Juwairiyya ta kalli Haroon murya a sanyaye tace.
"Haroon ya jikin nashi dai?".
Ɗan tsayawa yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah gsky zama muce ya worke, sabida ya amayarda duk wani dafin dake jikin bilalin yanzu naga shatin kunaman ma duk sun ɓace a jikinshi, ya zama sai shatin bulalin".
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
"Suma nanda kwana uku in sha Allah babu tabonsu a jikinshi. Na gaya muku ai jinyar Shaɗi ba abu mai wuya bane a masarautar Joɗa, yanzu da asibiti aka kaishi, koda ko ƙasar waje za'a fiddashi a ƙalla sai anyi watanni uku ana jinyarshi, in yanada nisan kwana ya worke da kyar in kuma kwananshi sun ƙare ya cika a can. Amman yanzu yana tashi bacci zaiji sauƙin sosai".
Cikin mamaki suka zuba mata ido.
Jalal da Jamil da yanzu suka shigone suka haɗa bakin wurin cewa.
"To wai Ummiy meyasa naga kamar farin cikin, abun kikeyi keda ko ruwan sama bakya son ya taɓa lfyarmu mu bare ɗan gatanki".
Kanta ta ɗan jijjiga tare da cewa.
"Abune mai duhu shekarun ku baiyi yawan da zaku gane haskenba, su kansu magautan Jabeer duk basu san ƙarfin iko da sani da shaharar wannan masarautar akan al'adun Shaɗi bane,."
Jafar ne yayi gaba bayan ya duba agogon hannunshi ganin hakane duk suka bi bayanshi.

A can Rugar Bani kuwa, bayan anyi sallan bamgrib, anyi Isha'i.

Shatu, Rafi'a, Ummey, da kuma Bappa sai Autar gidan Junainah dake konce gefen Ummey duk sunyi shiru.
Suna jin Bappa yana basu lbrin yadda komai ya faru a wurin gasar cikin sanyi yaci gaba da cewa.
"Tabbas akwai abinda Allah yake nufi da wannan bawan, haƙƙun nasan Allah bazai bari a zalumceshi haka nan banzaba, inaji a jikina akwai wani babban al'amari mai girgiza zuƙatan mutane da zai faru a nan gaba".
Cikin sanyin murya Rafi'a tace.
"Bappa meye sunan jikan sarkin ne?".
Cikin sanyi Bappa yace.
"An faɗa amman na mance sunan".
Sallamar da wani yaro yayine ya sasu maida hankalinsu kanshi, bayan ya rusuna ya gaisa Bappa ne yace.
"Bappa ana sallama da Shatu wai tazo".
A hankali Shatu dake zubda hawaye ta juyo ta kalleshi. Bappa kuwa cikin girma yace.
"Waye ne?".
Wani irin azabebben ajiyan zuciya Shatu ta sauƙe jin yaron yace.
"...!

By
*GARKUWAR FULANI*"Ya Salmanu ne yake kirantan, yace tayi haƙuri tayi sauri ta fito."
Cikin sanyin jiki Shatu ta manna kanta jikin kafaɗar Rafi'a.
Shi kuwa Bappa, gyaran murya yayi tare da cewa yaron.
"To je kace mishi tana zuwa."
Jin haka yasa yaron ya juya ya fita.

Miƙa Bappa yayi kana ya kalli Shatu murya a sake yace.
"Shatu tashi kije, kiji dame yake nemanki".
Cikin sanyi tace.
"To". Kana a hankali ta miƙe dan cika umarnin Bappa.
Rafi'a kuwa, miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki, gyara musu wurin konciya tayi, sannan tazo ta shigar da Junainah kana ta cewa Ummey su shiga, jiki a saɓule Ummey ta miƙe suka shiga.
Bappa kuwa turakanshi ya shiga.

A can ƙofar gidan kuwa.
Bisa ɗan dakalin ƙofar gidan nasu, suka zauna.
Tunda suka zauna tayi shiru, kanta na sunkuye tana wasa da ƴan yatsunta, kana hawaye na ɗigowa kan tafin hannunta.
Shi ma Ya Salmanu shiru yayi, tamkar bazaiyi mgna ba.
Farin wata kuwa ya fito ras ya haska ko ina, alamun yau watan ya kai kwana tara ko goma.
Kanshi ya ɗan juyo ya ɗan kalleta cikin tsananin tausayawa ya fidda numfashi mai zafi tare da cewa.
"Shatu!". Shiru bata amsa mishiba sai dai ɗago kanta tayi tana kallonshi hawaye na kwaranya, wani irin murmushi yayi cikin sanyi da harshen fillanci yace.
"Bazan hanaki kukaba, Shatu, sabida koni kaina nakan zubda zafafan hawaye a duk sanda na tuna yayuna ƙannena makusantana, abo kaina da aka kashe, wanda basujiba basu ganiba.
Nakanji zuciyata na tafasa, tafasar da nakejin bazai taɓa gushewa ba sai na ɗauki fansa."
Cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu fansa kuma?".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Uhum fansar dai, tunda hukuma da gwamnatin da masarautun gargajiya basu ɗauki mataki kan abinda akeyi mana ba. To mu zamu ɗaukarwa kanmu."
A hankali tace.
"Ta yaya ɗin bayan duk an kashe matasa majiya ƙarfin. Cikin kaso goma na mutanen Rugar Bani an kashe kaso 6 huɗune suka rage. Me amfanin ramuwa, wlh da zan faɗa aji da mun bar musu garinsu kawai mu koma wani wurin".
Gyara zaman shi yayi ya fuskanceta da kyau cikin sanyi yace.
"Ko wani ɗan adam ina ya shiga dumuwa, ire iransa ke shige mishi ya magance matsalar.
Yanzu da ɗan jarida ɗaya aka kashe zakiga zakiji yadda ƙungiyoyin yan jaridu zasu magantu, sai ya zama babu wani rahoton da zasu buga sai na kashe ɗayansu da akayi.
Hakama da za'a kashe police officer ɗaya zakiji yadda hukumar zatayi ta bincike da ɗaukar mataki har sai sun gano wayene sun kuma ɗauki mataki.
Da za'a ƙona kamfani ɗaya ire irensa kamfanoni sama da dubu zasu iya shiga fadan.
Hakama in da za'a taɓa ɗan kasuwa to zakiji yadda duk yan kasuwa zasuyi ta kumfar baki.
Da za'a kashe manomi ɗaya to zakiji yadda gungun manoma zasuyi rubdugu kan mgnar.
Da za'a taɓa bafaden wata masarauta zakiji duk masarautun ƙasarnan sun amsa.

Haka abin yake. Duniyar ta zama waka sani? waya sanka? Mu kuwa Fulani bamu san kowa ba bayan Allah da Manzonsa, bamu da wani namu a siyasance.
To tunda haka abin yake, muma da wannan salon zamuyi amfani.
Muna nan munata raba goron gaiyata wa duk al'ummar fulanin makiyaya a duk inda suke a cikin duk faɗin duniyar nan, in dai sunada damar zuwa to su zo!.
Su kawo mana agaji, wlh in sha Allah da izinin ubangiji sai mun yaƙi kafuran Bonon sai mun kashe dodon tsafinsu Bonon mun hallakashi a doron ƙasa,
Shatu mun kai matakin da wallahi babu mahaluƙin da zai dakatar damu.
Sai mun kauda Shirka da waɗannan mushirkan a wannan yankin."
Ido ta rumtse wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata.
Cikin muryar dake nuna ƙunar ranta tace.
"Ya Salmanu wane mataki ake ɗauka kan neman su ya Giɗi kuma?".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Yana cikin matakin shiga cikin ƙabilar mu yaƙesu, mu kuma bincika ko sun ɓoye su Giɗi a cikin garin nasu".
Ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Allah ya taimaka".
Amin Amin.
Murmushi yayi kana yace.
"Kinji batun gasar da akayi ko da nasarar dake tinkarar rayuwarki ko?".
Cikin sanyi tace.
"Kaiya ya Salmanu ina kake da tabbacin nasara mutumin da bamu san irin fansar da zai ɗaukaba, naso ace kaine kai wannan nasarar da nafi kowa farin ciki".
Murmushi mai ciwo yayi a ranshi kana yace.
"Nan ɗin ma muna zaton farin ciki, duk da akwai tarin ƙalubale, mu dai in mun samu wani ya ci Ba'ana a gasar Shaɗi kin san yayi al'washin zai bar ƙasar nan gaba ɗaya ko?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Uhum in bai sauya salon ba dai".
Cikin jin daɗi yace.
"Ba zai sauya saloba, dole zai bar ƙasar sai dai shiri zaije ya ƙara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya'a, mun yarda su masarauta Joɗo fulani ne".
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a ɗaura aurenmu a ranar".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
"Iye yan Matana an girma, me ma za'ayi mana?".
Cikin kunya tace.
"Ban saniba".
Murmushi yayi kana yace.
"Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za'a ɗaura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba".
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.

*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL'FARMA ANNABI DA AL'ƘUR'ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH🙏🏻😭😭😭 Especially ku ƴan SPG na roƙeku da Allah🙏🏻😭😭

Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar walƙiya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ƙarfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin ɗan rawan murya yace.
"Me haka, zuwa babu sallama?".
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
"Kiyaye bakinka idan maza suna wuri."
Cikin dakiya Salmanu yace.
"Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi".
Wani irin zabura Ba'ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
"Bana so ya Ba'ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai".
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai".
Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.

Shi kuwa Ba'ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.
Chapter 74 · 0% Book details