← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 142

Sashe 138

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ƙamshin turarensa.

Idonshi ya ɗan buɗe tare da ƙanƙancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren.
Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace.
"Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin ɗan adam?".
Kallon shi ta yi tare da kwaɓe fuska kana ta ɗan tura bakinta tare da fara magana ƙasa-ƙasa can cikin maƙoshinta.
"Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba." Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buɗe idon ya zubasu kan bakinta.
Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haɗe lips ɗintaba yace.
"Kika ce kin yi yajin cin abinci?".
Ya faɗa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma ɗabi'arsa bane.
Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faɗin hakanba.
Lips ɗinsa ya ɗan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa.
"Uhmm ni ba haka na ce ba."
Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya.
Shi kuwa cikin tsareta da idon yace.
"Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!".
Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta ɗago kai ta zuba mishi ido.
Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sauƙe numfashi,
kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata.
Cikin narkekkiyar murya tace.
"Cewa na yi na ƙoshi."
Ta ƙarashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi.

"Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke".
Dariya Ummi tayi tace. "Idan zata ci sai na goyata".
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ƙasa tana nanata zancensa wai agoyata.
"Yi haƙuri ki ci abincin kin ji." ta kuma jin muryarsa a bazata.

Janyo flask ɗin yayi gabanta,
flask ɗin ta ɗan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida ɗazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data ɗumama mata.
Sama-sama a haka ta ci abincin da ɗan yawa duk da bata so cinsa ba.

Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa.

Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta ɗan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa.
"Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi".
Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil ɗauki ka kai mishi".
Ta ƙare mgnar tana ɓoye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin.
Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray'n ta miƙawa Jamil dake cewa.
"Ummi kawo dai in kai dan ke".
Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti.
ba su daɗe ba Yah Ja'afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka ɗan ci gaba da hirarsu

Haka dai sukayi wunin wannan.
Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu.

Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ƙi, sai da kanta ta kai masa.
Don Aysha tsoron zuwa ɓangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki.

Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ƙi zuwa.

Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ƙamshi yake zubawa.

A haka ya fito falonshi
breakfast ɗinsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil ɗin na ce masa ga breakfast ɗinka Hamma Jabeer.

Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. "Rabon Aiiish da side ɗinna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan". Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba.
"Uwar raki da tsoro".
Ya faɗi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije.

Bayan ya shiga asibitin ɗaki ɗaki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana duba lfyarsu wanda dama hakan al'adarsa ce kyautawa marasa lafiya, bayan ya gama da shiga ɗakunan suna binsa da addu'o'in nasara da lfy a rayuwarsa.

Ya wuce office ɗinsa don duba outpatient, lumshe ido yayi bayan ya zauna kan kujerar,
Miƙa ya ɗanyi a hankali tare da yin salati.
Gaba ɗaya yanayi shi ya sauya.
Tun jiya yake jinsa cikin wani irin matsi.
Yau kuma tunda gari ya waye yake jin wani abu na fusgarsa a hankali yake dannewa zamansa waje ɗaya ya ji abun na ƙoƙarin son bijire masa, patient ne ya shigo, ya duba sa cikin kulawa tare da ɗaukan dukkan bayanansa ya rubuta masa magani ya fice, kwantar da kansa yayi jikin kujerar haɗe da lumshe idunsa da suka ƙanƙance saboda wani irin feelings yake ji na bin sassan jikinsa a haka ya duba dukkan patient ɗin sai gab da magriba ya bar asibitin saboda hadari da ya fara haɗuwa alamar za a yi ruwan sama.

Direct masarautar Joɗa wuce.
Yana shiga cikin masarautar kai tsaye Masallaci ya wuce don yana shiga cikin farfajiyar gidan aka kira salla.

Bai fito daga masallacin ba, sai da aka yi sallan isha'i sannan ya fito ya nufi gida.

Sosai yake jin wani irin masifeffen feelings mai shegen fitina yana bibiyar sasan jikinsa gaba ɗaya, a haka ya shigo falon, su Jalal na biye dashi a baya.

Ba a falon Ummi na ɗalinta hakama Aysha.

Wuce Side ɗinsa yayi.

Su kuwa su Jalal abincindu suka ɗauka suka tafi Side ɗinsu sabida jin yayyafi ya fara sauka tare da wata iriyar sassayar iska mai sanyi daɗi mai ratsa jiki.

A Dinning area ya nufa.
cikin kasala da gajiya da yunwa ya zauna.
Abinci ya ɗan zuba kana ya fara ci yana mai matse cinyoyinsa yana mgnar zuci.
"To shi wannan me yake buƙata ne da zai hanani zaman lfy, ina dalilin da zakayi ta tashi tsaye, uwar me kakeso kayi".
Sai kuma ya ɗan sha ruwan sanyi tare daci gaba da mgnar zuci.
"To ita wannan uwar tsoron ma ni rabon da ita kwana biyu, na lura tsoron zuwa nan ɗin ma takeyi."
Mitssssss ya ɗan ja dogon tsaki tare da tafin hannunshi ya dafe kanshi.
Yau gaba daya sha'awarta ta cika shi don har sai da ya ji Jabeer ɗinshi tana harbawa da cekiyar neman aminiyarta.

A hankali ya miƙe ya bar wurin.
A kasalance sabida ua fara jin zazzaɓin nan na ƙoƙarin da yanzu kullum yake kwana dashi yana bin jikinsa, da sauri ya nemo paracetamol yasha.

Sai dai abin mamaki ba abinda yayi masa don ji yayi kamar ma ƙara ciwon aka yi jingina ya yi da kujerar yana sakin ajiyar zuciya tare da tambayar kansa meyasa ne? Meke damuna?".
Yau dare na huɗu kenan Kullum da zazzaɓi yake kwana a jikinsa, asuban fari yayi lfy, sai kuma wani daren. cikin sanyi yace.
"Ya zama dole inyiwa kaina medical checkup".
Don zazzaɓin na da zafin gaske, saboda ya fara jin ya yi loosing appatite, da ƙyar ya samu ya yi bacci don abubuwan sun haɗun masa goma da ashirin ga zazzaɓi ga azabebben Feelings mai fitinarwa.

Tun asuba ya tashi bayan zazzaɓin ya sauka, cike da kuzari da kuma tarin Feelings ya shirya ya wuce masallaci yana danne kanshi.

Yau yini akayi zurr ana tsuga ruwa kamar da bakin kwarya sai gab magriba ya ɗauke.
zuwa dare garin yayi luffff gwanin sha'awa sai iska mai sanyi da ɗan karen daɗi dake kaɗawa tare da ƙamshin ƙasa, yanayin garin yayi daɗi ko ina lib gwanin ban sha'awa da birgewa.

Bai shigo ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye side ɗinsa ya shige yana jinjina yau kwanansa uku rabon da ya sa Shatu cikin idonsa gaba ɗaya ta mai da shi dodo ta ƙi yarda su haɗu, ko abinci ne sai dai Ummi ko Jamil su kawo masa ga tsananin jarababbiyar sha'awarta da take fusgarsa yau kwana biyu, da ƙyar ya iya cin abincin yana jin alamomin bayyanar nataccen zazzaɓin da yake duk dare wanda baya jin magani ya kuma rasa meye sanadinsa ga kuma wannan mayataccen Feelings dake hanashi nitsuwa.

Zubawa sarautar Allah ido ya yi, yana jira yaga wai ko zata zo kuwa saboda yau kwana nawa rabon da su haɗu.

Wuce su da ya yi a falo suna hira ya kuma ce Ummi ta bata zam-zam ta kawo mishi yasa ya yi tunanin ko zata zo.

Shiru-shiru har goma da rabi hakan yasa ya miƙe ya fito falon ya tarar da su suna hira ita da Ummin, jikinsa sanyaye alamun zazzaɓin ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi zam-zam ɗinfa".
Juyowa Ummi tayi cikin kula tace.
"Aysha baki kai bane?".
Kanta a sunkuye tace.
"Na kai mana yana kan Dinning table ɗin ka na ajiye".
Juyowa yayi ya ɗan zuba mata ido,
sai kuma ya jinjina kai ya juya ya koma cikin falonsa .
yana lallaɓa kansa don sha'awarta na ta fusgarsa musamman sautin dariyarta da ya ji tana yi, sai da Jabeer ɗinsa ta harba da masifar ƙarfi.
Chapter 138 · 0% Book details