← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 142

Sashe 111

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A falon kuwa, gyara zama Shatu tayi tare da kallon Ummi cikin sanyi tace.
"Ummi dama mgnar da zamuyi ko!."
Sai kuma tayi shiru tana nazari, jin muryar Ummi nace mata,
"Uhum ina jinki faɗi".
Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
"Uhumm dama cewa, zanyi in ba matsala a rinƙa yin abun buɗa bakin ana kaiwa masallacin Masarautar Joɗa mana, tunda dole talakawan gari na zuwa nan sallan magriba."
Murmushi mai yelwa Ummi tayi tare da cewa.
"Allah sarki, Shatu mai tausayi, ba matsala amman ki tambayi mijinki in ya amince dai ba matsala, dama kuma ana fitar da abinci a sashin Gimbiya Aminatu, da Gimbiya Saudatu da kuma gidan Galadima, da Hajia Mama.
Da gidan Dr Aliyu da sauran duka, kuma ko Juwairiyya ma tanayi".
Murmushi ta ɗanyu tare da cewa.
"To Ummi muma ai muna son ladan wannan aikin".
Da sauri tace.
"A sosai ma kuwa. Sai dai ki sanar da maigidankin in ya yarda yanzu incewa Saratu ta ƙara hannun sosai".
cikin kwaɓe fuska tace.
"To Ummi shi wannan sarkin zirga-zirgan ina zan ganshi?".
Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace.
"Yana falonshi yanzu ya dawo, yana wucewa kina fitowa, jeki sameshi da sauri kada yayi bacci ya zama kin tadashi a bacci dan babu abinda yafi ɓata mishi rai sama da ya fara bacci a tadashi".
Cikin juya ido tace.
"Ummi to ni me zan ce mishi?".
Murmushi Ummin ta kumayi kana tace.
"Abinda kika cemin shi zaki ce mishi, tashi kije musan yadda zamu fuskanci aikin".
Ta ƙarishe mgnar tana miƙar da hannunta, a hankali ta miƙe tsaye, doguwar rigar jikinta ta gyara tare da yane mayafinshi.
Ganin ta tsaya ne yasa Ummi cewa"
"kije mana." Allah yasani badon tana son ladan aikin ciyar da marasa ƙarfi da basu abin buɗa bakiba da bazata sake zuwa tambayar abu wurin wannan kurman ganganɗinba, tun randa taje tana mishi mgnar yacewa Umaymah ta bar musu Hibba ya shareta take jin haushinsa in ta ganshi kamar ta ɗirka mishi dundu a baya.
Muryar Ummi data kuma jine yasata, juyawa, ta nufi corridor'n da zai sadata da falonshi.

A hankali take taku, tana jin sanyin tayis ɗin wurin na ratsa mata ƙafa,
sallama tayi a bakin kofar tare da kutsa kai ciki, tana mai murtuƙe fuska.
Bisa 1 str ta sameshi zaune, da alamun waya yakeyi da Umaymah.
Dan taji yana kiran sunanta.
Gefenshi ta ɗan tsaya tare da kallonshi ta wutsiyar ido.
Shi wai ko shi kaɗai ko a ɗakinshi shi ɗaya sai ya zauna da kima-kiman riguna, ganshi wata ƙil basa damunshi".
Haka taketa maganar zuci, har ya gama wayar da yakeyi bata, saniba.
shi kuwa baibi ta kantaba yaci gaba da ɗan aikin da yakeyi a wayar.
Jin shirune yasa ta ɗan kalleshi, ganin ya gama wayar da yakeyi ne yasa, cikin dakiyar murya tace.
"Uhummm dama so nake in ba matsala ko zamu rinƙa yin abin buɗa baki ana kaiwa masallacin, da kuma bawa bayi nasu daban".
Bai kulata ba, asalima yamutsa fuskarshi yayi, ya lura wannan abar bata gama iya sanin makamar mgna ba, ji yadda take mgn a kaikace.
Kamar ba ba fullatanaba, bayan anyi ittifaƙin bayan larabawa babu ƙabilar dake da luggar iya sarrafa harshe sama da Fulani.
Shiru tayi tare da tura baki kana ta ɗan murguɗashi, tare da cewa.
"Ayyah ka amince mana?".
kanshi ya sunkuyar tare da ɗaga system ɗinshi ganin biyu dai-dai ta cika.
Miƙewa tsaye yayi tare da motsa lips ɗinshi a hankali yace.
"Eh". Da sauri ta juya ta fita tana hararan bayanshi.
Shi kuwa bedroom ɗinshi ya wuce.

Rage kayan jikinshi yayi kana yasa hannunshi ya jawo pillow'nshi ya wurgar can gefe gaban gadon inda babu carpet,
a hankali ya kwanta a wurin,
Gudun kada daɗi gado yasashi yayi baccin da zai makara sallan la'asar, Yana konciya ba jimawa yayi bacci.

Ita kuwa cikin jin daɗin amincewar da yayi, tacewa Ummi.
"Ummi ya yarda yace muyi".
Miƙewa Ummi tayi tare da nufar kitchen a tare suka shiga.
Tana cewa.
"Yauwa to taho mu gayawa Saratu abinda za'ayi.

A tsaye suka sameta a tsakiyar kitchen ɗin kusa da kitchen table, tana gyara ganyen.
"Yauwa Saratu kin wonke shinkarfa masan ne?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh na wonke,kuma mafa tun ɗazu da nazo kuna kuma bacci na jiƙa wani, sai dai hannuna ya zarce yayi yawa, yanzu ina gama tsinkar ganyen zan kai markaɗen ne in na dawo an kwaɓashin sai in fara firan Arish ɗin".
Ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Mugamshin".
Babbar robar dake gefenta ta jawo tare da cewa.
"Gashi kinga yayi yawa wlh mancewa nai sai naga kamar na gidan Gimbiya Aminatu zan jiƙa shiyasa, kinga da na haɗa da wanda kika jiƙan yayi yawa sosai, ko zamu rabashi biyu".
Murmushi Shatu tayi ganin shinkafar tanada yawa, kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ba matsala hakanma yayi dama mai yawan akeso".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ga kuma ƙullun na dafa tun ɗazu har yayi sanyi, shiyasa nake sauri in kai markaɗen naga lokacin yayi nisa".
Motsowa tayi inda take tare da cewa.
"Ɗauki markaɗen ki kai bari in ƙarisa wannan aikin".
Cikin mamaki tace.
"A a bar".
Da sauri ta katseta da cewa, jeki".
To tace cikin mamakin sauƙin halinta ta ɗauki robar jiƙeƙƙiyar shinkafar da ta kai mudu biyar har ta ɗaura a kai,
Ta kuma sauke jin Shatu na cewa.
"Yauwa naga akwai murjejjiyar gyaɗa, ɗebo, da wata shinkafar kizo ga dabino da kwakwa a nan ki haɗa ki jikasasu ki tafi dasu, na kunune kafin a markaɗa wannan na masan shinma ya jiƙa sai a markaɗa miki shi.
Da sauri ta juya tayi yadda tace ɗin tanayi tana nuna mata dai-dai yadda takeso, saida ta gama kana rufe babban roban da marfinshi sannan ta ɗaura ƙaramin a kai ta tafi.

Ita kuwa Shatu matsowa tayi taci gaba da tsinkan ganyen, ita kuma Ummi freezer'n ta buɗe tare da ɗebo kayan ciki mai yawa, tazo.
Ta wonƙeshi fes, kana ta watsa al'basa mai yawa a ciki, Sannan tasa citta,kanamfari, cory tare da sauran kayan ɗanɗanon.
Gas ta kunna ta ɗaura tukunyar, sannan ta dai-dai-ta wutar.

Wani babban roba ta ɗauko kana ta nufi Store Arish ta ɗebo mai ɗan yawa tazo tana fereshi cikin ɗan injin ɗin firar lokaci ɗaya tayi nisa a fitar.
Ita kuwa Shatu tana gana gyaran ganyen ta ɗebo kayan miya tazo ta jajjagasu yadda takeso.
Kusan a tare suka gama da Ummi.
Wankeshi Ummi tayi bayan ta yishi tsillk-tsillk kana ta sashi a tukunya, tare ɗan yaryaɗa gishiri, ta rufeshi.
Ta ajiye gefe.
Ita kuwa Shatu cikin kula ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me za'ayi da ganyen?".
"Miyan da za'aci masar dashi".
To bata amsa tana komawa cikin Freezer'n fruits ta ɗebo.
Tazo tana wonkesu tare da shiryasu cikin tray mai girma, kana ta shirya wasu kuma a wani ɗan madaidaicin tray mai masifar kyau.
rufesu tayi kana taje tasasu cikin Fridge.

It's kuwa Shatu can nama ta ɗebo dai-dai misali wonƙeshi tayi tasa a tukunya tare dasa kayan ƙamshi dana ɗanɗano.
ta ɗaura a wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta ɗaura a ɗaya murhun dake gas ɗin babbane.

Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al'basa,
ya soyu yana ƙamshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ƙara wonƙe ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haɗa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.
Chapter 111 · 0% Book details