← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 142

Sashe 136

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙarishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu ɗan Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan ƴaƴan ɗakinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sauƙin abin ma ɗaya ne da suga sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata aka bashi duk da shi jikan ɗan ɗan ɗansa namiji ne".

Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaɓe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.

A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ƙasa da murya tace.
"Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana".
Kanta ta jujjuya a hankali ta buɗe baki tace.
"Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga ɗakin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?".
Ta ƙarishe mgnar wasu hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaɗa mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
"Ummi ɗakin Yan Sheykh ɗakine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al'wala wlh da badan wannan nagartar da Addu'o'in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
"Addu'a'u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar Joɗa.
Amman dan al'farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani".
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ƙasa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ƙasa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
"Ummi ku yarda dani, ku bani haɗin kai, zan tone duk abun cutarwa dake ɗakin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina buƙatar taimakon ku.
Amman kafin nan ki gayawa Umaymah in ta amince,
sai inyi aikin amman kada a gayawa Yah Sheykh dan bazai yarda ba."
Cikin tsoro ido cike da hawaye Ummi tace.
"To Shatu me zancewa Umaymah, me kika gani a ɗakin har ya firgitaki yasaki suma?".
Cikin kuka tace.
"Ummi kada ku tsaya bincike a kaina.
Ni dai ku yarda dani bazan cutar da kowaba na cikin Masarautar Joɗa sai wanda ya cutar da kanshi Ummi bamu da sauran lokaci mai tsawo fa, komai zai iya faruwa da Yah Sheykh".
Cikin tsoro da firgici Jamil yace.
"Ba matsala mun yarda dake, ni yanzu taimakon me zan miki?".
Cikin sauri ta share hawayenta tare da juyowa ta kalli shi kana tace.
"Yauwa Jamilu zaka samo mana mai saka tayis, yazo da katon ɗaya na tayis ɗin irin na bedroom ɗin Yah Sheykh sak da sak.

Sai kuma kayi ƙoƙarin mu samu ya Sheykh in ya fita ya wuni sai dare zai dawo".
Cikin sauri yace.
"Tayis da mai sawa ba matsala, batun in ya fita sai dare ya dawo kuma inaga.
Sai zuwa jibi ranar ne zaije asibitin gwamnatin Genaral Hospital.
To in yaje can wuni yakeyi wani lokacin sai dare zai dawo".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba matsala.
Ummi ke kuma ki kira mana Umaymah ki sanar mata, muyi abun da saninta."

To Ummi tace kana a wurin ta kira Umaymah tayi mata bayani.
Ba wani neman ba'asi tace.
"A barta Ummin Jabeer na amince, tayi duk abinda ya dace a kan mijinta da yayanshi da ƙannenshi dama duk wani abu nashi".

Cikin jin daɗi ta jinjina kai lokacin da take jin mgnar Umaymah.

Wani irin dogon numfashi taja mai ƙarfi sai gata ta tafi luuuh kan...!

Wasa farin girki? Shatu kadafa allura ta tono garma.

By
*GARKUWAR FULANI*GARKUWA

PAGE 25

"Da Mamaki kwallo a maƙabarta.
Wato dai haka za a cigaba da gwara kawunan mutanen. Masarautar Joɗa ana mayar da su marasa tunani?".
Gimbiya Saudatu Ta faɗa tana ya mutsa fuska don ta kasa kallon ƙwayar idon Sheykh.
Banza ya yi da ita duk da ya waiwayo ya kalleta, ya so tanka mata, amman sai ya share yaci gaba da takunshi cikin nitsuwa yana tafe yana tasbihi.
A hankali ya isa falon.

Kanshi ya ɗan juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor'n da zai sadashi da falonshi. "Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen.."
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
"Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba".
Da sauri tace.
"Zan fice ba sai ka koreni ba."
Ta ƙarashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaɗa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
"To wai ɗaga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sarƙar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta ɓace ɓat ko in ce ta yi ɓatan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ƙirƙiro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts..."
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buɗesu a hankali yace.
"Dakata, tsaya kiji."
Da sauri tace.
"Uhum ina jinka".
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
"Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahaluƙiya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar Joɗa, duk da kyautar ta yi kaɗan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ƙwarai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ƙarfin tukuicin da masararutar Joɗa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan".

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙe ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaɗan ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya ɗan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya ɗan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daɗi.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta ɗan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta ɗaga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daɗi Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin ɗiyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daɗi sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ƴata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ƴaƴan Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daɗin da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daɗi tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.
Chapter 136 · 0% Book details