← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 71

Sashe 70

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ya fara kasa-kasa ya fita na raka shi da harara sannan na tashi ina ta mita na shiga bayin nima,sai da na kwashe shanya na sannan nayi alwalan na fito na shimfida abin sallah na fara sallah ta cikin natsuwa.
..

Ban tashi akan sallayan ba sai da nayi sallahn Isha'i da shafa'i da wutiri sannan na shiga wanka,ban wani jima ba kasancewan yace zamu fita,koda na fito ban tsaya dogon kwalliya ba kawai mai na shafa sai powder da kwalli sai wet lips dana gogawa lebe na duk da haka ba karamin kyau nayi ba.parking d'in gashi na nayi na saka ribon na daure su ya koma kaman a cuci maza.

Tashi nayi daga nan zuwa wardrobe ina duba kayan da zan saka, akan wani Turkish gown light blue ido na ya tsaya ba wata-wata na fito dashi ya sha stones work tun daga sama har kasa na saka kayan nayi rolling da gyalen, gaban mirrna dawo na fara shafa humra na mai dad'in kanshi sai gashi nan ya shigo bakin shi dauke da sallama.

Numfashi na kusan tsayawa yayi na wucin gadi kamin ya dawo daidai ina tasbihi ma Allah da yayi wannan kyakyawan haliita da nake gani a gaba na,sosai yayi wani mahaukacin kyau cikin sabon shiga na wani yadi mai taushin gaske d'inkin half jampa kan shi babu hula sai gashinsa daya gyara sai sheki yake.wani abin mamaki kaman hadin baki shima yadin nashi light blue ne sai kamshi yake zubawa.

Ashe shima ta wajan shi abin haka yake dan ba karamin kyau na mishi.ba da kyar ya samu ya tattaro kuzarin sa yace" muje ko"

Tashi kawai nayi nazo zan wuce naji Yana" ba dai a haka zaki fita ba?" Kallon jikina nayi ina neman makusa amma ban gani a raina ina mitan shi komai sai yayiwa mutane iyayi.

"Pls wear ur hijab,tayaya zamu fita a haka mutane su kalle min ke" yace min a d'an kausashe, juyawa kawai nayi zuwa gaban wardrobe na jawo wani hijab ba tare da nasan wani kala bane na fara warwarewa cikin fushi.ban san lokacin da ya zo ba kawai Jin mutum nayi a bayana daf sosai har kirjin sa da bayana sun hadu,kan shi ya daura a gefen wuya na numfashi sa na sauka a gefen wuya na.ban san lokacin da na lumshe idona ba saboda wani irin yanayi da na tsinci kaina a ciki.

Kwace hijabin hannu na da yayi yasa na bud'e ido na sai gani nayi ya ciro wata dark blue irin mai hannun nan ya ajiye na hannu na sannan ya juyo dani ya warware ya fara kokuwan saka min,hannu na kawo da niyyan taimaka mishi ya saka min cikin sauri da sauran fushin sa ya kwabar da hannu na Wanda saida na kwabe fuska dan babu karya naji zafi.

Yana gama saka min yaga wani sihirtacaccen kyau da Kamala sun bayyana kaman yanda yakewa kowace mace data saka hijabi,ajiyar zuciya yayi tare da jawo hannuna muka fito yana aiyyanawa a ran shi cewa dole sai ya nemo min nikaf a gaba.

Har muka fito compound bai sake min hannun ba kuma bai ce min kala ba, wata mota baka dake pake a gefe ya nufa dani ya bud'e gaban motan ya sanya ni a ciki ya.rufe sannan shima ya zagayo ya bud'e mazaunin driver ya shiga ya zauna yayiwa motan key mai gadi ya bud'e mana get muka fita.

Tsit cikin motan baka jin komai sai kira'ar sheikh Sa'ad al ghamdi dake tashi cikin suratul Nisa'i, munyi tafiya mai nisa ba tare da mun kula juna ba domin dukkan mu cikin fushi muka fito amma sauraron kira'ar nan ya saukar mana da natsuwa duk muka rinka sauke ajiyar zuciya akai-akai.

D'an satan kallon inda yake nayi cikin rashin sa'a ashe shima ni d'in yaje kallo, wani sasssanyan murmushi mai kara min natsuwa ya aika min nima ban san lokacin da na mayar mishi da martani ba.

Dayan hannun shi ya miko ya rike min hannu yana murzawa a hankali yana tuki da dayan hannun, haka ya cigaba da tuki muna sauraron kira'ar har muka iso wani hadadden restaurant dake by pass.da alamu sabon waje ne dan ni ko sunan ban taba ji ba.

Shiya bud'e min mota na fito ya kulle motan sannan ya rike hannu na muka shiga ciki,duk inda muka wuce mutane sai sun bimu da ido suke dan ba karamin kyau da dacewa da juna mukayi ba.

Bamu tsaya cikin mutane ba VIP naga muka wuce, Kuma shi yafi ko ina tsaruwa sannan babu mutane, wani table dake can gefe muka nufa yaja min kujera na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fito da wayan shi yana daddanawa cikin basarwa.hakan da yayi ba karamin kyau ya mishi ba,muna zaune a haka wata waitress mai kama balarabiya tazo table d'in mu ta tsaya tana tambaya me muke bukata tare da miko mana menu.

Zafar duk da hankalin shi yana kan wayan shi hannu ya mika ya karba ba tare da ya dago ba balle ya san ya take,nima dai ban dago na kalle ta ba wajan nake bi da kallo domin ya tafi da imani na sosai. Ina daga ido naga ta kafe Zafar da ido kaman ta lashe shi har wani murmushi take ta jerowa ba tare da ta san tana yi ba.

Ras naji zuciya ta tayi wani mugun harbawa ina jin wani zafi na taso min a zuciya dan ji nayi kaman in tashi in shako ta,cikin rashin sa'a kuwa ta juyo muka had'a ido wani banzan kallo mai cike da gargadi na aika mata ina Jin wajan ma ya fara fita kaina sai dai ganin shi Zafar din bai san ma tana yi ba yasa na dan ji sanyi a raina.

"Fried rice and chicken with couslow" muka ji muryan shi ba tare da ya dago ba ya fad'a yana mika mata menu su,cikin sauri ta karba ta bar wajan mu dan kawo mana abinda yace.

Ajiye wayan nashi yayi ya dago ya kalle ni yace" ko wajan bai miki bane naga kinyi shiru"..

D'an turo baki nayi cikin jin haushin kallon shi da tayi nace" sun cika kallo dayawa".

Murmushi mai sauti yayi yana"ki fito fili kice kina kishin wata ta kalle ni".

Sai a lokacin na tuno katobar da nayi dan haka cikin tsare gida nace kishin meye kuma zanyi,wani ne da zai fita naga yana ta kallo na".a take murmushin fuskar shi ta bace lokaci daya yana "meyasa baki gaya min ba a lokacin".

Kamin in bashi amsa waitress d'in ta kawo abinda yayi order ta fara jejjera mana su.

Tana gama jerawa ta juya ta bar wajan ba tare da ta kara gigin hada ido da mu ba,tana tafiya naji yace" meyasa baki gaya min ba?"

"Saboda naga ya fita ne shiyasa"kwafa yayi ba tare da ya kara magana ba ya ture dayan plate d'in gefe yasa min spoon a cikin plate na gaban shi yace min " let's eat".

D'an satan kallon mutane dake wuri nayi naga kowa harkan gaban shi yake dan haka banyi magana na dauki spoon d'in muka fara cin abincin ina mita a zuciya ta kan a wajan ma dan iyayi irin nashi a plate daya zamu ci abincin.

Bai fi spoon 4 yayi ba ya dauki tissue ya goge bakin shi, spoon d'in da ya ajiye nabi da kallo kamin inyi magana ya riga ni yace" it's not tasty at all, Ni tunda na saba da girkin ki bana iya cin abincin ko ina wlh".

Wani dad'i ne ya ratsa ni dan inko abinda ya fad'a haka take to tabbas na kusa mallakan shi,ajiye spoon d'in nayi nima ina " toh mu koma gida mana in samo maka abinda zaka ci".

"No dare yayi yanzu,amma tashi muje "yace yana mikewa nima mikewan nayi saida yazo ta waje na ya rike min hannu sannan ya saka musu kud'in su a cikin bill da suka kawo mana muka fito ,yanzu ma shi ya bud'e min mota na shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya shiga ya tada mota muka fito bamu zo gida direct ba sai da ya tsaya a suya sppt ya saya mana dasu ice cream sannan muka dawo gida.

A nan tsakiyan parlour muka zauna kan rug muka ci naman sosai dan suyan yayi mana dad'i,ice cream kam ni kad'ai ce na sha Zafar cewa yayi baya sha.tattara sauran naman da ice cream d'in nayi na kai kitchen naman na saka su a fridge koda na dawo ban tarar da shi a parlour ba ya shiga dakin shi.

Nima dakin nawa na wuce direct bathroom na fad'a nayi brush na watsa ruwa sharp-sharp na fito,gaban mirror naje bayan na goge ruwan jiki na shafa lotion sama-sama sannan nabi lungu da tsako na jikina da humra mai sanyin kamshi.

Normal rigan bacci na saka amma bashi da wani tsaho dan da kadan ya wuce guiwa na, hawa gado nayi na kwanta ina tunanin yinin mu na yau.Zafar ya canza sosai wanda kullum nake tunanin ko dai ya fara sona ne? Wata zuciyar Kuma kwabata take tana tunanin furucin sa akaina.

Zafar kuwa shima bayan ya gama shirin sa na bacci ya kwanta sai yaji duk kwanciyar bata mishi ba so yake ya gan shi kusa dani mu kwanta irin na jiya.

Zurum ya mike kaman Wanda ya tuna wani abu bedroom sleepers d'in shi ya saka ya fito a hankali yana tsand'a har ya iso kofan parlour ya tura ya shiga ya d'an saurara jin shiru babu motsi ya tabbatar mishi da cewa na gama shirin kwanciya na kwanta.

Sai da ya kara matsowa kusa da kofan bedroom d'ina sannan ya fara yin motsi da abubuwa can Kuma ya kunna kukan mage a wayar shi ya d'an yi kukan sannan ya fice da sauri ya koma nashi dakin ya kwanta yaja bargo ya lullub'a yana dariya tare da fatan Allah yasa tarkon da ya d'ana ya kama mishi tsuntsu gasasshiya.
Chapter 70 · 0% Book details