← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 71

Sashe 30

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ke kuma ki bita da addu'oin zaman lafiya da farinciki Mai daurewa ya tabbata a gidan ta, insha Allah sai ts samu fiye da yanda muke hasashe".

Inna share hawayen ta take wasu na zubowa bata son musu da mahaifiyar ta amma ta san halin Baban mu sai shi, mikewa tayi da niyyan komawa Ya Maaji da bata da hakuri ga zafin zuciya ta bud'i baki da nufin zatace wani abu Maa tayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannnu, kawar da kai gefe tayi tana cize lebe na haushin an hana ta magana.

"Ya Maaji na tafi ki gaida su Bayuram,Maa na gode Allah ya saka da alkhairi ya baki nisan kwana insha Allah zanyi kaman yanda kika ce" Inna ke fad'an haka tana gyara hijhabi dake jikinta.

Ya Maaji da duk takaici ya hana ta saka baki cikin maganan nasu da taga Inna ta juya zata tafi tayi yunkurin magana nan ma Maa bata bata dama ba ta kara daga mata hannu alaman tayi shiru.

Shirun tayi tana kallon Inna har ta fice sannan ta dawo da hankalin ta kan 'yar uwar ta tace " haba yaya yanzu sanyin halin naki ya kai kija baki kiyi shiru a cuci 'yar jikar ki guda d'aya tilo, ni dai wallahi tafiya ta zanyi ba zan zauna bakinciki ya kashe ni ba"

Hijabinta ta shura tayi hanyan waje, Maa tana ta kwala mata kira bata yarda ta juyo ba balle ta amsa, Dan murmushi Maa tayi tana girgiza kai tare da mata addu'a Allah ya rage mata wannan zafin zuciyan.

Lokacin da ta dawo bacci ya d'an sace ni ban san ma ta dawo ba sai cikin bacci naji kaman kuka harda shashheka, a hankali na bud'e ido na dan tabbatarwa, bayan ta na gani tana ta kuka tsakanin da Allah wanda tun tasowa ta banga ko kwatanci sa tayi ba.

Tausayi da kaunar tane naji yana bin ko ina a cikin jinin jikina saboda na san duk a kaina ta tada hanklin ta kan auren da taji Baba yace zai min, banida zab'i dole in kwantar da hankali in nuna mata babu komai ta wajena ko zata samu natsuwa, wannan dalilin yasa naki fad'a mata tun farko kenan amma ba yanda zanyi dole ne ta sani.

D'an motsi nayi yanda zata ji, aiko nan da nan ta shiga share hawayen sannan ta d'an juyo sai taga ido na a rufe, bakin gado tazo ta zauna tana shafa min gashin kaina, jin ta daina kuka yasa na bud'e ido na kaman yanzu ne na tashi daga baccin.

Murmushi ta sakar min tace " bacci kika koma kenan?" Gyad'a kai na nayi nima ina maida mata martanin murmushin.

Ina ta jira inji ko zata min maganan auren amma naji tayi shiru sai jana take da hira tana bani labaran ban dariya, nima dan in kwantar mata da hankali yasa na saki raina nayi ta dariya amma can kasan raina cike ya tab da damuwa.

Bayan sallah magarib sai ga Abban Zafar da tawagar sa a kofar gidan mu Kuma sun taki sa'a Baba yana nan bai tafi ko ina ba, Baba duk ya rikice ya susuce ganin manyan masu kud'in garin maiduguri a kofar gidan sa kuma da sunan sun zo had'a zuri'a dashi.

Makotan mu biyu ya kira sannan ya kira Baban Dije wanda zance shi ya jagoranci komai ya hana Baban mu gudun kada ya kwafsa ko ya saki layi, hakan da yayi ya taimaka kuwa dan shi Abban Zafar tunda yaji ance Mallam ya zata Baban Mallamin ne da gaske.

Wata 2 ciff aka saka na biki mu aka rabu cikin mutunci bayan sun sauke carton carton na minti da chewing gum da goro na rabawa yan uwa, Abba yaja Baba gefe ya bashi check na wasu kud'ad'e kan yayi hidimar biki da gida sannan ya d'aura da basa bukatan a kaini koda cokali guda d'aya su zasu tanada min komai su kawai surka suke bukata.

Murna da Baba yake ji kaman ya daka tsalle amma ganin yanda Baban Dije ya kama kai yake musu magana shima hakan ya kwaikwaya har yayi mishi sallama ya shiga mota driver yaja suka tafi.

Muna zaune sai gani mukayi anata shigowa da kwalaye kaman za'a bud'e shago, kowa kallon kayan yake tare da neman karin bayani sai dai babu mai bamu, sai da aka gama shigowa da kayan tass sannan Baba ya shigo yana jan banban rigan shi a kasa cikin d'aga murya ya fara magana yanda kowa na gidan zai ji.

"Allahu yayi Allahu yayi!!! Ina kuke mutanen gidan nan kowa ya fito yaga abin arziki daya same mu, kayan saka rana ne na 'yar albarka, wata 2 kacal iyayen ango suka ce a saka dan suna bukatan ayi auren da wuri.

Ba wayan nan kayan kawai ba har takardan karb'an kud'i na banki sirikin nata ya bani sannan yace basa bukatan mu kai ta koda cokali su zasuyi mata komai...."

"Aaaaaaayyyyyyiiirrrrrrrr!!! Inna Asabe ce ta rangad'a wannan gud'a cikin farinciki tace" Masha Allah 'ya tayi goshi duk abubuwa daka lissafo duk na saka rana ne ina ga Allah ya nuna mana ranan auren ba magana....."

"Aikin banza aikin wofi kowa yaga dama zaiyi ai tunda abin shige-shige ne" Gwaggo Aisha ta katse ta, Inna Asabe dai bata kula ta sai shewa suke da Allah ya sanya albarka suke da Mama Dije.

Tashin hankali sosai na shiga da ganin kayan da muka maganan Baba duk da na san da zancen, kokarin dannewa nake saboda kada in karawa Inna tashin hankali amma na kasa daurewa,kuka na fashe dashi sosai har jikina yana rawa na shiga d'aki da gudu na fad'a kan gado ina mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro.

.
Jiki a sanyaye Inna ta biyo baya na ta zauna a gefena ta kura min ido itama idon ta na cikowa da hawaye amma ta hana su zubowa, tana rayawa a ranta inama zata iya dakatar da wannan auren da tuni ta dakatar da wanne zan ji cikin lokaci d'aya na had'u da jarrabawan rayuwa ga rad'ad'in rabuwa da Yaya na bai bar ni ba ace kuma ga auren da bamu san daga ina ya fito ba.

Sai dai bata da zab'i dole ne ta karfafa min guiwa inyiwa mahaifina biyayya kaman yanda itama tayiwa nata mahaifin, gyara zama tayi tana gyaran murya sannan ta fara magana cikin rarrashi" wani lokacin kuka bashi ne waraka ba ga matsaloli na rayuwar mu ba,sai dai mu kanji sauki da rad'ad'in da zuciyoyin mu suka tsinci kan su a ciki dan haka ba zan hana ki kuka ba kiyi Zareefa kema ko zaki ji sauki.

A al'adance da kuma addinin musulunci ya bawa mahaifi daman zab'awa 'yar shi miji daya ga ya dace da ita bi ma'ana ya yarda da addinin shi da kuma tarbiyan shi dan haka kada kiyiwa mahaifin ki mummunan fahimta domin ba zai tab'a Kai ki inda zaki wulakan ta ba kuma albarkacin biyayya da kikayi mana Allah zai saka miki da mafi alkhairi ko kuma da abinda baki tab'a zato ba balle tsammani.

Abu d'aya da nake son ki tuna wannan auren ko dan Abdulbasit ya kamata ki rike shi da hannu bibbiyu saboda na san duk inda yake zai ji cewa za'a miki aure,kn ga kuwa kin nuna mishi zaki iha rayuwa ko babu shi sannan zai fahimci cewa kina da masoya ba shi kad'ai ne gare ki ba".

Tun ina kuka kasa-kasa har na daina nayi shiru ina sauraron kalaman Inna, ya zanyi dole ne inyi biyayya in aure shi tunda ya biyo ta hannun Baba, baya ga haka in nace bana son shi waye nake dashi a yanzu, wanda na taso da son shi tun ban san kaina ba ya guje ni ya watsa min kasa a ido I don't have choice rather than accept this man domin na gama soyayya a rayuwata zuciya ta ta rufe kofa tayi ban kwana da soyayya harb abada.

Sanyi sosai Inna taji a ranta na ganin kalamanta sunyi tasiri a kaina har na daina kukan sai ajiyan zuciya da nake akai-akai, matsowa nayi jikin ta sosai tare da d'aura kaina a kan cinyar ta na saka hannaye na duka biyu na rungumo kwankwason ta, itama tasa hannu ta dama tana shafa min gashin kaina na fara magana a hankali kaman mai rad'a.

" Inna ku iyaye nane biyayya a gare ku ya zama wajibi a gare ni, kukan da kika ga inayi ba dan auren da Baba yace zai min bane kawai na tuna da Yaya nane" na karasa wasu sabbin hawayen na zubo min na tausayin kai na, na fad'i haka ne dan in kwantarwa Inna hankali ba wai da gaske ba.

Cikin jin dad'in kalamai na Inna ta kara rungumo ni jikin ta tana shafa kaina tare saka min albarka da addu'oin gamawa da duniya lafiya.

******************

A kwana a tashi babu wuya a wajan Rabbi Izzati, mun cinye wata d'aya cikin watanni 2 da aka saka na bikina kuma gini da Baban mu yake yayi nisa sa dan har an gamawa Inna bangaren ta,2 bedroom da babban parlour sai kitchen da store sosai ginin yayi kyau, yanzu bangaren Inna Asabe da Gwaggo Aisha ake yi.

Maryam ta dage sai rawan kai take akan bikin ni bata san haushi ma take bani ba, duk wasu frnds d'in mu na makaranta ta sanar dasu sai shirye-shiryen su suke ni dai na kawao na mujiya na zuba musu.

A bangaren Zafar ma hakan take dan shi cewa yayi babu wani biki da zaayi sai ranan da zai auri love of his life sannan zasu sha bukukuwa ba biki bama.

Sadiq ne yace bai isa ba dole ne su sha biki in ya tashi yin wancan yayi abinda ya ga dama, yaso yayi jayayya amma ganin yanda Abba da Mom suka dage suna shirye-shiryen auren yasa yaja bakin shi yayyi shiru tare da zuba musu ido ya san in har zai cigaba da nuna halin ko in kula asirin shi zai iya tonuwa.
Chapter 30 · 0% Book details