← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 71

Sashe 29

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*23&24*

"Na sha had'iye wulaƙanci da cin fuska daga wajan sa da matan shi, amma wallahi kada wani yace zai tab'a min ke anan ne zasu ga fushi na". Tana magana ne a wannan lokacin tare da saka hijabinta ta kama hanyan waje.

Da gudu nima na miƙe ina kwala mata kira akan kada ta fita wajan nasu amma ina har ta fice daga d'akin, bakin gado na koma na zauna dabas ina jin zuciya ta na suya tsanar bawan Allah nan na ninkuwa a cikin ta ba dan komai ba sai dan yanda naga tashin hankali da bacin rai shimfud'e akan fuskan ta wanda zan iya cewa tunda aka haife ni ban tab'a ganin koda kwatancin shi a tare da ita ba.

Gata kuma ta fita sa-in-sa da Baban mu da Gwaggo Aisha shima wannan ban tab'a ganin Inna ta kula kowa ba a gidan,koda kuwa me zasu ce mata ko suyi mata bata tankawa kowa sai dai ta shige d'aki tayi zaman ta,nice dai a baya nake dan kula su kasancewa ta bana iya wuce tayi in dai na fad'a ne sannan kuma na tsani wulakanci da raini wanda duk Gwaggo Aisha tayi degree akan su.

Sosai take min fad'a kaman ta doke ni akan kula su da nayi amma yau itace dakanta ta fita yau; " Innalillahi wa inna ilahi raji'un" na zauna maimaitawa ina kuka, wannan wani irin mutum ne shi tunda ya shigo rayuwa ta komai kara cakub'ewa suke " I hate that ugly creature" nace ina Kara fashewa da sabon kuka.

Naci kuka na na more sai dai ga mamaki na banji motsin Inna ta a tsakar gidan ba balle inji muryan ta, Baban mu ma na daina jin muryar sa sai Gwaggo Aisha da take ta ihun ta ita kad'ai.

Shirun da naji yayi yawa ne yasa na mike a hankali na l'eka waje bayan na yaye labule kad'an, tsakar gidan babu kowa da alamu Gwaggo Aisha tayi ta gaji ta koma ciki sai masu aiki da suke ta aikin su sai kanne na da suke wasa a gefe,toh ina Inna ta ta tafi???

Ras-ras naji zuciyata ta harba da karfi kar dai yaji Inna tayi, abinda tunda akayi mata aure bata tab'a yi ba.

Cikin mutuwar jiki na koma d'aki na zauna ina tsiyayan hawaye masu zafin gaske, ban jima da zama ba naji waya ta ta fara ringing ko juyowa banyi ba balle in sa ran zanyi answering, haka ya gama ihun sa ya daina.

Kwanciya ta nayi akan gado ina rokon Allah yasa ba yajin tayi ba cos I can't imagine myself in dis house without my inna, wayance ta fara ringing Kuma cikin gajiyawa na d'auka ina kallon no data kasance special in ban manta ba kaman d'azu dashi aka jera min 2 missed calls.

Saura kad'an ya katse na daga kai kunne na nayi shiru ba tare da nayi magana ba, shiru naji shi wanda ya Kiran ma yayi bashida niyyan magana,mun kusan minti 2 a haka ina shirin cire wayan a kunne na kaman yana kallo na yace;

"Who do you think you are? Da har zaki dinga ignoring calls na, be very careful with whom you are dealing with or akwai lokacin da yana zuwa da zakiyi regretting duk abubuwa da kike".

Yawu mai d'aci na had'iye da ya makale min a makokoro ina sauraran bakaken kalaman sa da suka fi wuta zafi, sarai na gane muryan nashi wanda kullum in yana magana zaki jita cike da isa da kasaita.

Bai san cewe nima a wuya nake ba tunda har ya zama shine silan fara fitan Inna a gidan auren ta da sunan yaji, tsab zan juya mishi duk rashin mutunci da nake dauke dashhi dama nima ba tayar baya bace.

Muryan shi ce ta maido ni hankali na naji yana cewa; " 'yar Mallam kada kice wai saboda na damu da kene nake ta jera miki kira haka, nooo ko daya I just want you to tell Mallam Abbana zasu zo anjima". Kit naji ya katse kiran ba tare da ya jira yaji me zance ba.

" 'yar Mallam!! " Na maimaita sunan a fili "kunbu in na yarda shegiya nake nice 'yar Mallam din, wallahi sai na koyawa dan raini nan hankali ni har akwai wanda zai takale ni in kyale shi never".

Tsakani da Allah na zage ina masifata ni kad'ai kaman yana gaba na, danna mishi kira nayi ina jiran ya daga nima in rama amma har ya katse bai daga ba, ban hakura ba sai da na jera mishi missed calls 5 bai daga ba, cillar da wayan nayi na fashe da kuka sosai dan jin zuciya ta nake kaman ta fashe da ban samu na rama ba dama can ina da wannan halin tun ina karama na taso da abuna, cikin 'yan gidan mu babba ko karami ya tab'a ni sai na rama hankali na yake kwanciya, har duka Inna ta sha yi min akan in daina amma na kasa saboda a jini na yake. Wannan dalilin yana daya daga cikin dalilan da Gwaggo Aisha take min zazzafan tsana.

Inna kuwa tana fita a d'aki bata ko kalli inda Baba da Gwaggo Aisha suke ba ta fice zuwa gidan su, suma dai basu lura da ita ba duk hankalin su yana kan fad'an da suke.

A tsakar gida ta samu Maa da kanwar ta wacce suke kira da Ya ma'aji suna hiran su na 'yan uwan taka gwanin sha'awa, da sallama ta shiga sai dai bata tsaya taji amsawar sun ba ta shige d'akin Maa.

Da ido duk suka bita har ta shige cikin d'aki ba tare da ta tsaya wajan su ba kaman yanda ta saba ba ko kuma ince yanda ya kamata ba, Ya ma'aji ta dubi yayar ta tace" Yaya da alamau yarinyan nan tana cikin damuwa,dubi yanda ta shigo gidan nan hankali tashe, ni wallahi wannan kaddararren auren nata da kina jin shawara ta da tuni ta rabu da shi haba yarinya tana 'yar karamar ta amma kullum cikin tashi hankali take dubi yanda duk ta motsare,ga fitinan miji gana kishiyoyi da wanne zata ji" ta karasa da matukar fushi a fuskarta domin ita halin ta daban dasu Maa fad'a ne da ita sosai ga rashin hakuri.

Murmushi mai sanyi Maa tayi mata tana girgiza kai tace "kai ma'aji akwai ki da daukan abu da zafi baki san halin yaran yanzu ba abu bai kai ya kawo ba zasu d'auke shi da zafi........".

"A'a Yaya kada ki raina hankalin ta na tabbata ko ke da kika fimu sanyin hali aka ki gidan nan nata zasu kure ki,bari inje inji meya faru" tace tana mikewa tare da nufan d'akin da Inna take ciki.

A kan carpet da yake shimfid'e a tsakar dakin ta samu Inna ta had'a kai da giwa tana kuka kasa kasa.

Dafa ta Ya ma'aji tayi yasa ta d'ago da kai suka had'a ido tayi mata murmushi ita kuma kukan ta kara fashewa da shi cikin muryan kuka ta fara magana"Ya ma'aji ku ceci Zareefa dan Allah ku cece ta ni na yarda suyi min duk abinda suke so amma dan Allah su kyale ta tayi rayuwa mai yanci da farin ciki, yarinya ce k'arama bata san rayuwa ba dan Allah kada su jefa rayuwar ta cikin.........."

"Ya isa haka ya isa, ki natsu ba abinda zai faru da Zareefa muna tare da ke kuma Allah yana tare da mu dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki min bayanin me yake faruwa?. Ya ma'aji ta katse Inna da take magana cikin fitan hankali.

"Wai aure zaiyi mata kuma ni baiyi shawara dani ba ban san waye zai bawa ba,kawai yau da safe ya shigo da masu gini wai zai canza ginin gidan zuwa na zamani kuma yana so ayi da wuri kuma a bangare na aka fara saboda auren wai ba zai wuce wata d'aya ba. ni abinda yake bani tsoro na san halin shi in game da kud'i ne komai zai iya yi......."

"Ba 'yar sa bace ko saida ta zaiyi ina ruwanki " suka ji muryan Maa a bakin k'ofa wacce da alamu ta dad'e tsaye a wajan,duk kallon ta suka tsaya yi har ta shigo ta samu waje ta zauna tana fuskantar Inna.

"Kin bani mamaki Bintu da har zaki tada hanklin ki kiyi abinda baki tab'a yi ba wato kawo karan miji, yanzu da kika kwashi kafa kika zo min gida menene a zuciyar ki ko so kike ni in kira shi ince bashi da daman zabawa 'yarsa mijin aurex ko kin manta addinin musulunci ne ya koyar da hakan...."

"Maa na sani wallahi na sani amma kema kin san halin shi zai iya yin komai akan kud'i, sannan ya kamata ya shawarce ni ya fad'a min abinda yake faruwa ba wai inji maganan ta sama ba" Inna ke fad'an haka cikin wani irin murya mai nuna tsananin halin da take ciki.

"Menene halin sa Bint? koma wani irin hali ne dashi ba zai tab'a cutar da Yar cikin sa kuma maganan shawara da kike so yayi dake, wani shawarwan zaiyi bayan ke kan ki a karkashin sa kike.

Tashi ki koma d'akin ki ki cigaba da ibadan ki cikin kwanciyar hankali kaman yanda kika saba sannan kija yarinyan nan a jikin ki,ki kwantar mata da hankali kiyi mata tuni da duk wanda yayiwa iyayen sa biyayya to tabbas zai ga alkhairi a cikin rayuwar sa, kada ki kuma yin abinda zai tashi hankalin ta, duk halin da zata shiga in fana ganin ki a kusa da ita zata ji sanyi,
Chapter 29 · 0% Book details