← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 71

Sashe 62

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I will be right back wifey" yace min cikin wani husky voice sannan ya fice na bi shi da ido har ya shige ciki, ajiyar zuciya na sauke mai karfi ina kara jin son shi na ninkuwa a zuciya ta " how I wishh......." Nace Ina lumshe ido tare da fad'awa duniyar tunani har ban san lokacin da ya dawo ba sai lallausan tafin hannun shi da naji akan fuskata yana shafawa a hankali yasa na bud'e ido na a zabure ina watsa mishi mugun kallo d'an dariya yayi yana d'aga hannun shi sama alaman surrender.

"Tunanin me kike haka da har ba kiji shigowana ba" yace yana juyowa gaba d'aya shi gare ni bance mishi komai ba na sunkuyar da kai na kasa hawayen da ban san na menene ba suka fara sauko min.

"Ohh shiitt me yasa kike min asaran hawayen ki masu tsada da darajan nan, in maganan Baba ne I promised you babu abinda zai same shi kuma soon zai dawo gida pls ki kwantar da hankalin ki kinji " yace yana miko min tissue .

Banyi gardama ba na karb'a na goge ido na tare da gyad'a mishi kai a hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana "good girl" sannan yayiwa motan key muka mike hanyan gida, koda muka iso gida ya hana ni d'aukan kayan yayi shi ya shigo mana dasu duka har parlour na ya kawo min kayan sannan ya ce in fito muci abinci.

"Ni na koshi "nace ina cire hijabin jikina tare da nemawa kaina wajan zama, marairaice fuska yayi yana kallo na can kuma sai ya zauna kusa dani yace " haka mukayi da ke, i thought mun riga da munyi solving komai before mu fita, meyasa kike son maida mu baya pls ki bar komai ya wuce kinji we are now good friends uhum?" Ya karasa cikin rarrashi ya kama hannu na ya mikar dani muka fito, bai saki hannu na ba kaman yanda nima na kasa yi mishi musu har muka isa dinning.

Kujera yaja min na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fara firfito da kayan kwalama da ya sayo mana a restaurant " zabi abinda zaki my babe" yace yana turo min su gaba na.

Tsam na mike ba tare da na bashi amsa ko na kalli tullin abincin da ya turo min ba na wuce ciki abina, da kallo ya bini zuciyar shi na mishi wani irin share shi da nake yi, kasa tab'a komai yayi shima ya ture su gefe ya zuba tagumi yana zurfafa tunanin ta ina zai b'ullo min ya shawo kaina, yaga na dawo da warmer da Inna ta zubo min abincin a ciki na ajiye sanna na zauna ina kokarin bud'ewa .

"Wow ashe kayan dad'i kika kawo mana daga gida" yace yana kallon yanda na cika plate d'ina kuma bani da niyyan zuba mishi, amma jin yanda yayi maganan cikin natsuwa da danganta gidan mu da masu yasa shima na zuba mishi na tura gaban shi ba tare mun had'a ido dashi ba.

Kara jawo plate din yayi gaban shi ya saka spoon ya cika da jallof din shinkafan da yayi shar dashi da tarin nama a ciki kaman ba abinncin sadaka ba ya kai bakin shi a take ya lumshe yana " hmmmm ashe a wajan Momyn mu kika koyi daddadn girki nan, sai dai ita nata yafi naki sau goma kullum Ina santin naki ashe ga original din nan naki photo copy ne".

Ban san lokacin da na d'ago kai muka kalle shi ba fuskata d'auke da murmushin jin dad'in yanda ya yabi Inna ta for the first time naji ya burge ni ban san lokacin da na fara bashi labarin yanda yan gidan mu suke santin girkin ta kullum manya da yara duka.

Cikin jin dad'in yanda na saki jiki muna labari dashi ya rinka ja na yana yabon gidan mu daya lura shine abinda nafi so kuma yake sakani farinciki, sai gashi mun cinye abincin tas harda karawa da fruit sauran kayan kuma na Kai kitchen na ada na su.

Har dare muna tare yana cigaba da jana a jiki babu laifi nima na sake sosai tare mukayi kallo na kawo mana su alewan madara dasu gulli shiwa da Inna ta had'a min acikin ledan dana taho dashi harda su tsumi a ciki sai dai su can cikin drower na bud'e na adana su cos ban san amfanin su a yanzu ba ,har zuwa goman dare muna tare sannan na mishi sai da safe na shige d'aki na bar shi zaune yana jin kaman ya biyo ni mu kwana tare amma ya daure shima yayi d'akin shi yana ganin nesa tazo kusa tunda har ya gano abinda yake saka ni farinciki lokaci d'aya.

Da washe gari haka na taso cikin walwala dan kasncewar mu tare jiya yasa na rage damuwan da yake zuciya ta sosai, kitchen na shiga na fara nema mana abu mai sauki da zamu yi breakfast dashi bayan na gama kimtsa gidan tsab sai kamshin turaren wuta yake tashi ta ko Ina.

Na gama komai cikin kankanin lokaci na jujjuye su a warmers ina cikin juye tea da na dafa da kayan kamshi a flaks naji numfashin mutum dab dani a tsorace na juyo saura kiris ruwan shayin ya zube a kafana yayi saurin tarowa ya rike yana " hey be care full zaki kona wannan kyakkyawan kafan naki ki min asara" bance mishi komai ba sai zamewa da nayi na bar mishi shayin na koma gefe shi kuma ya cigaba da juyewan.

"Ina kwana " nace mishi a hankali Ina kallon kasa.

"Da fatan princess d'in Inna ta tashi lafiya" yace yana murmushi.

Nima murmushin nayi jin ya Kira ni da princess d'in Inna, d'aukan tryn dana jera kayan Karin a kai ya fita zuwa dinning fuskar shi d'auke da zallan farincikin ya samu logo na.

A wajan cin abincin ma haka yayi ta ja na da hira wai abincin Inna na jiya yafi dad'i wai ko dai zamu koma kai mata kwanon mu kullum tana zubo mana abinci, dariya nayi sosai dan ba karamin dariya maganan nashi ya bani ba.

Sai da muka gama yace min in shirya muje gidan mu in ya ajiye ni zasu wuce barrack da Baban mu yake da Baban Dije saboda yau da safen nan aka kira shi kan suje by 12.

Cikin azama kuwa na koma d'aki na fad'a bayi dan yin wanka zuciya ta cike murnan yauma zan ga Inna ta, ban b'ata lokaci ba na fito cikin shirina da nayi da wata atamfa super golden da adon fari a jiki shiyasa mayafi, takalmi da jaka da na riko duk suka zama farare, d'an kunne da sarka da na saka suma white pure gold ne dan haka ba karamin kyau nayi ba.

A parlour na tadda Zafar da shima kaman had'in baki ya saka wata tsadaddiyar shaddar shi fari sol da hula kindai da akayi da zare Mai golden da fari, takalman shi da agogon hannun shi suma duka farare ne sosai muka shagala da kallon juna kowa na yaba kyan da d'an uwan shi yayi a zuciya.

Da kyar na samu na janye ido na daga kan shi na mayar kasa Ina wasa da gefen mayafina naji muryan shi" let's go" yace bayan ya sauke nauyayyen ajiyan zuciya.

Gaba yayi nabi shi a baya zuwa inda motocin gidan suke ya bud'e min wata sport car fari na shiga na zauna sannan shima ya zagaya ya shiga yaja muka kama hanyan gidan mu, cike da nishad'i yake tukin sai murmushi yake ta sakewa shi kad'ai nima yau ban juya kaina gefe ba amma Kuma ba shi nake kallo ba ta kasan ido nake kalon shi.

A kafar gidan mu yayi parking Baban Dije da kawun su 2 da suka zo dama suna tsaye suna jiran zuwan shi, zan bud'e kofa in fita naji yauma a kulle a shagwab'e na juyo ina kallon shi tsabanin jiya da nake aika mishi da mugun kallo.

D'an dariya yayi yana d'aga min gira d'aya yace " in ba dan nayi locked ba da haka zaki fita ki bar ni babu sallama" turo baki nayi na d'auke kaina toh wani irin sallama ne da sai ya wani rufe kofa, bakin nawa da yake matukar birge shi zubawa ido yana ji Ina ma Ina ma.....

Jin shiru bai min magana ba kuma bai bud'e min kofan ba yasa na d'ago muka had'a ido alaman kiss ya min da bakin shi sannan ya min blowing yace " take care of yourself for me princess" duk kunya sai ya rufe ni na rasa yanda zanyi shi Kuma sai murmushi da naji yayi mai sauti sannan ya bud'e mana Lock d'in motan , shiya fara fitowa sannan nima na fito ganin iyayen nawa yasa na Kara jin sabon kunyan kaman kasa ya bud'e in shiga haka nake ji sabida dadewa da mukayi a mota kada suyi mata wata fassara.

Har kasa ya duka ya fara gaishe su nima na zagayo na durkusa na hau gaishe su cike da kunya, cike da kulawa duk suka amsa sannan ni na wuce cikin gida su kuma daga nan barrack suka wuce amsa Kiran Baban Hamis.

Da yake an san da zuwan su babu wani shamaki ko dogon bincike aka bar su suka wuce, direct office d'in shi wani sojan yayi musu jagora suka samu gaba d'ayan su da abokan aikin shi suna jiran isowan su.

Bayan gaishe-gaishe Baban Hamis yayi musu bayanin Baban mu bashida laifin komai hasalima shi wanda suka kama da wani dalilin shi daban wajan yi mishi wannan sharri, nan duk suka hau hamdala daga baya kuma aka kunna musu video da suka d'auka ta cctv camera suka kalla, duk mamaki ya cika su Baban Dije jin wai Abdulbasit yayan Zareefa shine yayiwa baba wannan d'anyen aiki, gaskiya ba zaka tab'a shaid'an mutum ba jibi yanda wannan mutumin yake komai kaman na Allah ne shi ashe mugu ne na bugawa a jarida?.
Chapter 62 · 0% Book details