← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 71

Sashe 33

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana a tashi babu wuya wajan Allah dan yau shine karshen gyaran fata da ake min sai lalle da aka shiga yarfa min na jan lalle gwanin sha'awa taso a yi min kitso nace mata bana so ta bar min gashi na haka, ba dan taso ba ta kyale ni suka maida hankali kan lallen.

Sai bayan sallah isha'i muka samu daman komawa gida ta d'eba min wasu kayan gyaran tace in rinka yi a gida tunda auren saura kwana 3, karb'a kawai nayi na amsa mata da toh amma ba dan ina da niyyan yi ba.

A kofar gida suka sauke ni Maryam bata shiga ba saboda dare yayi suka wuce tana ta santin lallen da akayi mata wai yayi kyau, ni dai ban iya biye mata na juya zuwa gida abina kasancewar na kwaso gajiya.

Mutane na gani cike a cikin gidan mu ana ta cece kuce kuma kana jin maganan kasan kaman fad'a ake , d'an d'aga kai na nayi naga matan gidan mu ne harda makota, ban kara gigin d'aga kai na ba na wuce b'angaren mu tunda banga Inna ta a wajan ba.

A parlour na samu Inna da 'yan uwan ta zaune sun saka kaya a gaba suna maida abinda ya faru duk fuskan su babu dad'i sai ita Inna ce ba zaka gane mataa ba.

Zama nayi a kasa kan carpet na fara gaishe su d'aya bayan d'aya duk suka amsa min fuska sake, muna gama gaisawa na wuce kitchen neman ruwan sha anan ma wasu kayan abinci na gani gari guda.

Ina cikin shan ruwa ne naji Ya Maaji tana magana cikin b'acin rai wanda ya sani maida hankali kan zancen nasu I really want to know what happened.

"Ni dai idan kun san ba zaku canza halin ku ba wallahi karshen ta ba dani za'a yi bikin nan ba, haba wannan wacce irin rayuwa ce ayi ta cutan ka ana kunsa maka bakinciki amma ka kasa ramawa, wa za'a nunawa hakurin muma ai muna da itan matsalsr idan yayi yawa sai a maida ki kwandon shara yanda kowa ya kwaso nashi kan ki zai juye".

"Gaskiya ne hakurin Bintu yayi yawa sosai har ta doke Yaya wajan sanyin hali, amma wannan zalincin ne dai ba zamu bari ba dole ne a d'auki mataki saboda gaba" cewar Aunty Batool.

"Kina ji fa ita Bintun da bakin ta yanzu take cewa ba yau ta fara yi ba wai ranan da aka fara musu gini an ga wasu layu wanda aka kona ita kuma a take ta fara iface-iface wani babban abin takaici wai ita da Zareefa su sukayi mata addu'a har ta samu lafiya...."

"Har ta samu kafan komawa wajan bokan ta zaki ce Batool, in ba dan Allah ya takaita wannan yaro Ibrahim ya ganta yazo ya fad'a ba, da shikenan auren nan ya fasu amma da yake bata da kunya bakin ta bai mutu ba ana magana tana mayarwa" fad'in Ya Maaji.

"Ban ki ta naku ba nima ba wai kuma fad'an ne ban iya ba, amma abinda nake son in tuna muku duk wanda ya rike Allah in ba wani ikon sa ba babu abinda zai same ka, ku duba mana sau 2 tayi yunkurin cutar da mu Allah yana mayar mata da abin ta.

Ban so kuka kula ta ba, jibi yanda asirin ta ya tonu cikin bainar jama'a wannan ma ya ishe ta ishara, mu kuma bama gajiya da d'aga hannayen mu sama insha Allah, Allah zai kare mu" Inna ta basu amsa cikin sanyin murya babu wacce ta kara cewa kala da alamu maganganun ta ya kashe musu jiki.

"Innalillahi wa Inna ilahi raji'un" shi kawai nake ta maimaitawa tare da sulalewa na zauna dabas kan tiles na kitchen d'in, cikin tashin hankali amma ni kam Ibrahim bai kyauta min ba da yazo ya fad'a har aka dakatar da ita, ina ma tayi nasaran sake binnewa da shikenan na fita daga wannan cakwakiyar matsalan.

"Gata da hassada da ya gama bin jinin jikin ta dubi yanda ta fito wai tana nuna adawar ta a zahiri kan kayan cin-cin da aka kawo" naji muryan Aunty Fatima tana magana cikin d'acin rai.

Sai ana na fahimci ashe kayan da na gani kayan cin-cin ne kenan, shikenan yanzu da gaske ake aure za'a yi min, auren ma da wanda bai san daraja ta ba?

Hawaye sai rige-rigen saukowa suke banyi yunkurin hana su ba na bar su suna kwarara domin yana rage min rad'ad'in dake cikin zuciya ta.

Muryan Inna naji tana kwala min kira ba shiri na mike daga zaunen da nayi ina share hawaye na na fito duk suka bini da kallon tausayi .

"Me kike yi a kitchen d'in tun d'azu" ta jeho min tambaya,

"Ruwa na sha " na amsa mata cikin murya kuka, kan kace me kuma hawaye suka fara kwaranya.

"Daga tambayan ki shine zaki fara min kuka? Bari in tashi inyi miki abinda zakiyi kukan da hujja" Inna ke fad'an haka tana shirin mikewa, da gudu nayi d'aki na maida kofa na rufe ina jin su Ya Maaji suna mata fad'an kada ta kuskura ta tab'a ni ta bar ni inyi kuka na, ban ji karshen maganan su nayi shirin kwanciya na kwanta abina.

Da washe gari ga mamakina ashe duk basu tafi ba anan suka kwana sai ya Maaji da ta kwana gidan Maa, da rana ya fara yi sai ga gidan mu ya fara cika da 'yan uwa ashe wai yau ake cin-cin ni dai ganin sun fara yawa na wuce bangaren su Maman Dije saboda kowacce ta ganni sai ta kira ni da sunan amarya basu san hakan kona min rai yake ba shiyasa na gwammace in tattara in bar musu gidan su kara ta.

Kamin in wuce naji sun fara sa-in-sa da 'yan uwan Baba da suka zo cewar su zasuyi, su Aunty Batool kuma suka ce anyi magana da professional bakers su zasuyi kasancewar komai ya zama na zamani ita kuma Gwaggo Hinde ta fara masifa wai ai zagin su akayi a fakaice meye basu iya ba da za'a ce zasu kira wasu suyi dama sun raina su.

Wucewa ta nayi abina ban san ya suka kare ba, ina can b'angaren su Dije Ni kad'ai duk abin duniya ya ishe ni zuwan su Maryam da sauran 'yan class d'in mu yasa naji d'an dama-dama.

Kusan azahar Dije ma ta iso da yaron ta da yayi wayo gidan ya gama kacamewa saboda surutun ta, hatta Hajara nan tazo tana d'an kqma jiki tana baya-baya saboda abinda ya faru jiya, sai da naja ta da wasa sannan ta saki jiki suka cigaba hayaniyar su Jameela ce dai ban san ina take ba domin yanzu abin nata kullum kara muni yake dan sai tafi sati bata gida kuma koda ta dawo to a buge take dawowa ta zama cikakkiyar 'yar kwaya.

Muna nan a b'angaren Maman Dije Har dare a lokacin mafi yawancin 'yan matan sun wuce Dije ma ta tafi sai Maryam da Hajara ne kad'ai suke tare da ni amma itama Maryam d'in shirin tafiyan take wai sai gobe zata taho gaba d'aya ba zata koma ba sai an gama bikin.

Har bakin gate muka raka ta nida Hajara inda driver gidan su yake jiran ta, ta shiga yaja suka tafi mu Kuma muka koma cikin gida, Hajara har tana shirin shiga kofan su na tsaida ta nace " Dan Allah Hajara muje mu kwana tare a d'aki na kin ga har yanzu da sauran mutane a b'angaren mu".

"Kina ganin babu matsala?" Tambayan da ta jeho min kenan idon ta na cikowa da kwalla.

"Wani matsala kuma ko kin manta ke'yar uwa tace" na bata amsa tare da jan hannun ta muka wuce, a parlorn muka tadda su Ya Maaji sun baje suna rarraba snacks da akayi da wayan da aka bayar akayi cikin different containers wai suna rarraba su.

Za'a cire na gidan su Ango da wanda za'a rabawa baki sai kuma w so hg6xhanda za'a rage min "wai" atoh dole ince wai dan ni har yanzu na kasa gaskata aure na ake.

Hajara duk ta kasa sakin jikin ta akan abinda ya faru jiya ga ya ma'aji sai binta da kallon banza take,ganin haka yasa na jata zuwa d'aki da yake mallaki na a yanzu, tunda muka shiga naga jikin ta ya kara sanyi sai bin d'akin da ido take alaman d'akin yayi mata kyau dan sai ince zan iya kira shigowan ta d'akin mu tun kamin ayi mana wannan ginin.

A bakin gado nace ta zauna ni kuma ina shiga bayi nayi wanka tare da dauro alwala na fito na fara shirin bacci,duk tana zaune a inda na bar ta"tashi kema ki watsa ruwa zaki fi jin dad'in baccin" nace mata ina saka kayan bacci na ba musu ta mike ta shiga kamin ta fito na fitar mata da rigan bacci sannan na haye gado na kwanta,ko da ta fito ta mayar da kayan jikin ta nace ta canza tare da nuna mata kayan da na fitar mata.

Ba zan iya cewa nayi bacci ko banyi ba a wannan daren saboda zanyi kaman bacci ya fige ni kuma duk juyi da Hajara tayi ina ji,ni dai gani nan har aka kira sallahn farko na tashi nayi alwala na fara nafila har aka kira na sallahn asuba mukayi tun da sanyin safiya mutane suka fara hidiman gaban su gidan ya d'auki hayaniya na ana shirin biki a gidan da gaske.

Breakfast da aka kawo mana ban iya cin komai illah tea dana sha kawai nayi wanka muka koma can b'angaren Maman Dije a lokacin 'yan uwan sun fara cika gidan na kusa da nesa

'Yan mata da muke mates duk wajan mu suka zo suka dasa sabon hira sunayi suna ta tsokananta amma na kasa kula kowa cikin su sai yake da nake binsu dashi.

Kusan 12 rana sai ga masu decor sun zo wai daga gidan su Ango aka turo su suyi decoration na wajan da za'ayi wushe-wushe.

Duk yanda nayi gudun kitso bai yiwu ba dan Maa ce da kanta ta turo wata mata tace in zauna a min kitso,dole na na zauna aka yaryad'a min kitson KELEYASKU.
Chapter 33 · 0% Book details