← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 71

Sashe 38

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa yayi suka gaisa cikin mutunci sannan ya wuce ciki shi kuma ya kulle gate d'in tare da shigewa makwancin sa, murya can ciki yayi sallama ya shigo parlour ba shiri ya lumshe ido yana shakan daddadan kamshin turaren wuta da Aunty ta saka kamin ta tafi, ya kai good 5 seconds yana shakan kamshin sannan ya bud'e ido yana bin ko ina da kallo yanda aka jera komai cikin tsari gwanin burgewa.

Tab'e baki yayi ya kama tafiya ciki yana da shi Abba ya bawa kud'in nan yaki ya bada order furnitures masu tsadan nan dan da farko shi aka ce ya zab'a min da gangan ya zab'i wasu bakake wai tunda painting gidan masu haske ne wayan nan sune zasu haska.

Abba bai kara kula shi ba ya zab'o wayan nan da aka jera a parlorn, Kai tsaye inda ya san nan ne b'angare na ya nufa ya bud'e kofa kamshi days tarar a nan yafi na farkon, madaidaicin parlour nawa yabi da ido yanda komai aka shirya shi cikin kwarewa da wayewa babu tarkace dayawa amma komai ka gani a ciki classic nd expensive ne.

Sosai parlour ya tafi da imanin shi yana tunanin yaushe Abba ya sayo wayan nan dan shi dai a gaban shi akayi ordern komai, toh meye ma damuwar shi da zai damu kqn shi sai ya san ta ina suka zo kayan.

Cikin sauri ya karasa kofar bedroom da nake ciki ya murd'a handle d'in yaji ta a garkame gam kara murd'awa yayi yana jijjiga kofar wai ko zan zo in bud'e ni kuwa Ina can ina ta sharar bacci na ban san ma yana yi ba.

Tsaki yayi tayi yana cizon yatsa da takaicin kulle kofa da nayi,nan da nan wani tunani ya fad'o mishi ai ba za'a rasa spare keys na ko wani kofa ba, cikin sauri ya juya da nufin zuwa d'akin shi ya duba har yayi steps 2 zuwa 3 ya tsaya cak sakamakon wani abu daya fad'o mishi a rai.

Kar dai ace na rufe d'aki nane saboda ina tunain zai shigo min as ango??

Hmmm inko haka ne ba zai bud'e ba balle in saka ran cewa wani abu ya kawo shi, God forbid ba zai tab'a abinda wannan kucakar zata raina shi ba, dangwaran da ledan hannun shi yayi a bakin kofan ya juya ya nufi nashi d'akin .

Tun a parlour shi ya fara kunce necktie dake wuyan shi da maballan suit din shi a haka ya karasa cikin bedroom ya gama cire kayan ya shiga bathroom, wanka yayi da expensive liquid soaps da kamshin su ya cika gidan gaba d'aya bai dad'e ba ya fito sama-sama ya shafa d'an 🧴 a jikin shi ya saka white pyjamas d'in shi masu taushin gaske ya bi lafiyar gado.

Tsaki yaja shi kad'ai yana kara Jan bargo ya lullub'e jikin shi da kyau yana mai jin haushin kan shi na kawo irin wannan tunanin a ran shi,wai da auren gaske yayi da yana can tare da amaryan shi " Allah ya sauwake 'yar Mallam ce fa Kuma ka aure ta ne dan gujewa Abba ko ba haka ba?" Ya tambayi kan shi yana lumshe ido saboda ya fara jin bacci " Anya zan iya bari tayi min wata 2 a gida? she have to leave within a month kamin nan na samu d love of my life".

Tun yana suratai wa kan shi har bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi.

Hankali kwance na sha bacci na ban tashi ba har sai da naji ana kiraye-kirayen sallah duk da naji na kwanta shiru ina jiran inji Inna ta leko ta tashe ni amma shiru, ganin kila zamu makara yasa na tashi a raina ina mamakin lafiya kuwa yau Inna bata tashi ba.

Da Addu'an tashi daga bacci na tashi zaune ina murza ido, a firgice na mike tsaye ganin Ashe ba a d'aki na da na sani na kwana ba domin Ina kallon komai tar dan ban kashe wutan d'akin ba na kwanta haka saboda tsoro.

A hankali na fara bin d'akin da akace nawa ne da kallo tare da mamakin irin dukiyar da aka narkar a ciki, ba komai ya saka ni mamaki ba sai dan jiya naji suna ambatar cewa Inna ce tayi min kayan d'aki.

Kara kallon wannan Royal set maroon da sirkin baki nayi sai sheki suke kaman an shafa musu mai ko kuma ince kaman da glass akayi su yanda suke walwali da d'aukan ido, ko turaren wuta,humra,kulacham da sauran su da aka jera min a cikin tangamemen show glass abin kallo ne dan kwalaben kad'ai sunyi jarin wani.

Jiki a mace naja kafafu na cikin bathroom nan d'in ma tsayawa nayi ina kare mishi kallo yanda komai na ciki fari ne kal kuma duk na zamani da kyar na gane wasu abubuwan na had'a ruwan zafi nayi wanka dan jiya tsoro ya hana ni yi, alwala ta na d'auro bayan na gama wankan na fito.

Aunty Fatima duk ta nuna min yanda suka ajiye min kaya na duk da ba'a kawo min lefen ba na gidan mu ne da Inna tayi min, wata atamfa doguwar riga na saka wanda ya sha dinki mai kyau kuma cif na cika shi, abin sallah na shimfid'a na saka hijabi na kabbara sallah.

Ban tashi a kan abin sallah ba sai kusan 6:40 domin sai da nayi azkar na safe na d'an yi karatun Qur'an sannan na mike na cire hijab na ninke su da sallaya na ajiye gefe, shafa shaffafen tommy na da yake kaman babu hanji nayi jin yana kukan yunwa dan ni kaina na manta yaushe rabo na da abinci, da fa auren gaske nayi ko kuma da Yaya na na aura I know he will pampered me yana rarrashi yana bani a baki ba zai tab'a bari in kwanta da yunwa ba, but dubi wannan mugun ko irin Kazan amarci da naji ana bada labari bai kawo ba.

A take Kuma wani sashin zuciya ta ya kwab'e ni da cewa ta ina zan sammaci wani kazan amarci daga gare shi bayan ya jadda min dalilin aure na da yayi kuma baya gajiya da nanata min ba so na yake ba.

"Hmmm" kawai nace a raina tare da niyyan neman abinda zan ci, kaman mai tsoron kada wani abu ya kamata na bud'e kofa na leka naga wata fitinanniyar parlour na da ya kusan saka numfashi na barin jikina.

"Masha Allah " nake ta maimaitawa da jinjinawa Inna, yanda parlour nan ya tsaru koma wanene kai dole ne ya burge ka ba'a cika mashi tarkace dayawa ba but yanda aka jera komai a position din shi sai ya fito da kyan parlorn cushions labulaye duk kalan su daya wato peach nd milk color ne sai tangamemen plasma da sauran abubuwan kallo suma wajan su d'aya, abinda da yafi birge ni wasu manyan flower vase da aka ajiye a kowani angle shima ya bada ma'ana.

Tafiya na farayi zuciya ta na dukan 3-3 dan ina tsoron had'uwa da wannan dodon, ina bud'e kofa wani parlour na kara gani har yafi nawa komai I mean girma da dukiya da aka zuba a ciki baya lissafuwa shi kuma nan komai na cikin sa brown nd white ne.

Nan ma da naga kallon ba zai fishe ni ba na fara duba kofofi da na gani a cikin parlour dan neman kitchen na san anyi min gara ba na wasa ba so ko indomie ne in samu in dafa in sakawa cikin nan nawa da nake ji sai kara ya mutsewa yake.

Babu tunanin komai kai tsaye na nufi wata kofa da hankali na ya kwanta dashi na bud'e, wani sanyi da wannan sassayan kamshin sa suka min maraba da sauri na waro ido ganin inda na kawo kaina, a can tsakiyan tanfatsetsen gadon shi na hango shi kwance yana baccin sa cikin kwanciyar hankali dan bai san ma na shigo ba a hankali na mayar da kofan na rufe kaman yanda na samu na juya cikin sauri na koma inda na fito domin har naji na daina jin yunwan.

In ba dan Allah ya taimake ni yana bacci ba wani bayani zanyi mishi na kare kaina, da shikenan sai yace biyo shi nayi.

Ido na rufe sai sauri nake buri na in shige d'aki na naji nayi tuntube da abu a gefen kofata, tsayawa nayi Ina kallo tambarin jikin ledan ba sai an fad'a min ba na gane kajin amarcin ya kawo min amma banida darajan da za'a miko min hannu da hannu shine ya dangwarar min ita anan?

A zuciye nayi ciki tare da banko kofa Ina huci ni kad'ai lalle ya cika d'an rainin hankali, nima ban d'auka kaman yanda ya ajiye abin shi haka zai dawo ya d'auka sai dai yunwar ta kashe ni.

Na kusan minti 30 zaune sai tsaki nake ta jerawa saboda takaicin da ciki na ke bani na kasa hakurin yunwan ni kuwa nace sai dai in mutu ban cin kazar da aka dangwar min.

Jiki na rawa ya fara na kai last stage da ba zan iya jurewa ba kuma,tashi na kara yi ina tafiya da kyar tare da addu'an Allah yasa bai fito ya d'auke ba dan na lura in na zauna yunwar ta kashe ni ba matsalar shi bace Inna ta akayiwa asara.

Ina bud'ewa kuwa naga tana nan ajiye kaman yanda na barta, wawurar ta nayi na koma ciki da sauri bayan na maida kofa na rufe, ban iya karasawa cikin bedroom din ba a nan parlorn na zauna jiki na rawa na dauki goran yogurt na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tas sannan na ajiye roban Ina ajiyan zuciya.

Kullin kajin na warware shima na fara ci hannu baka hannu kwarya, ban sarara ba sai da naji nayi kat sannan na ture su gefe na jingina da jikin kujera sai sakin ajiyan zuciya nake amma kuma can kasan zuciya ta kuma haushin kaina nake ji da na kasa hakuri na ci wannan kayan shikenan ya samu hanyan cewa ni kwad'ayayyiya ce na san kad'an daga cikin halin sa kenan.
Chapter 38 · 0% Book details