← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 71

Sashe 14

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*Addu'ar Cin Abinci*

Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;

بِسْمِ اللهِ.

Bismi l-lahi.
Da sunan Allah

Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)

بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ.

Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.
Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.

Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ.

Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.

Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.

Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ.

Allahumma barik lana feehi wazidna minh.

Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar)

*10*

Rufe fuska ta nayi da hijabi na ina dariya ba tare da nayi magana ba,shima dariyan yayi ya d'auki yam ball d'aya ya kai baki ya gutsura ya fara taunawa har da lumshe ido wai dad'i ya kawo sauran baki na cikin sauri na kawar da kai na duk kunya ya gama mamaye ni.

Yaci ba laifi dambun naman da kunun ayan ne dai yace su kam gida zai tafi dasu sunyi dad'i sosai ya kara da cewa duk ranan da zai zo toh ya daina cin abinci anan zan rink'a mishi yana ci, koda ya gama muka sha hiran mu yauma kaman kada ya tafi haka nake ji amma haka muka hakura da zai tafi wani babban jaka ya bani yace in bawa Baban mu sannan muma ya bamu namu tsaraban mu nida Inna ya tafi.

Sai da na nemi taimakon wasu yaran sannan muka shiga da kayan cikin gida Gwaggo Aisha da sauran 'yan koron ta suka bini da harara wanda ban san ma sunayi ba.

"Ni ba wai bana son yayiwa Mallam alkhairi bane ba a'a yanzu Baban ku yazo yaga wannan tulin kayan da sunan nashi, gaba zai iya neman gidan yaron yace zai je maula ya zubar miki da mutunci gaba d'aya" Inna ke fad'an haka bayan na nuna mata jakan da Yaya na yace na Baban mu ne.

Shiru nayi ina tunanin maganan dan na san gaskiya Inna ta fad'a, zuwa can na fara murmushi ni kad'ai saboda na samo mana mafita.

"Inna in kin bashi kayan kice mishi a hukuma Yaya na yake aiki, kinsan yanda Baba yake tsoron hukuma na tabbata daga wannan rana ba zai yarda su had'a hanya ba balle har ya roke shi" na karasa ina dariya sosai dan na tuna yanda Baba yake bala'in tsoron su ban san kome yasa b ba.

Dariya Inna kanta tayi bata kuma ce min komai ba nima ban kara magana ba na kwashi tulin kayan da Yaya na ya kawo min da sunan tsaraba na fara jerawa cikin babban trolleyn kaya na.

Bayan sallah magariba Baba ya shigo d'akin mu ina gama mishi sannu da zuwa na wuce wajan Dije abina na basu waje wanda sam Inna bata san hakan domin ina barin wajan zai fara kokarin canza salon hiran nasu dan haka ba b'ata lokaci ta d'auko jakar kayan tsarabar shi ta ajiye a gaban shi ta koma can nesa dashi ta zauna.

Fara bud'e jakan kayan yayi yana mitan wai Inna ta maida shi dodo da zaran sun kasance su 2 a waje d'aya sai ta koma can gefe.........

Kasa magana Baba yayi saima jikin sa daya fara b'ari ya zaro ido yana kallon jakan in shock kawai, Inna da ta watsar da lamarin sa tana wasu sabgogin ta bata san halin daya shiga ba sai da ta juyo, a tsorace ta mike ta nufo shi tana," Mallam lafiya meya faru?"

Bai motsa ba kuma bai bata amsa ba sai da ta saka hannun ta a kafadar shi ta jijigashi da karfi tana," Mallam.... Mallam..." Sai a wannan lokaci ya firgita yaja dogon numfashi ya d'ago da kai yana kallon ta ba tare da yace komai.

"Kamin magana mana Mallam meya faru nace?"

Ajiyar zuciya yaja ya sauke kusan sau uku sannan ya ce," Bintu wayan nan kayan masu tsada kuma masu yawan da nake gani duka nawa ne kika ce?"

Ajiyan zuciyar itama Inna ta sauke jin cewa ashe wai kayan ne suka firgita shi ta koma wajan zaman ta ta zauna sannan ta amsa mishi da nashi d'in ne.

Firfito da manyan shaddodi da suke ciki ya fara bakin sa kuwa kaman gonan auduga sai da ya fito da guda shida suka kare sai takalma suma masu kyau guda 2 da huluna mu had'u a banki guda 2 da kud'in d'inki a kasa dubu hamsin.

Suma ne kawai Baban mu baiyi ba a wannan rana ya rasa ya zaiyi da rayuwar sa ya d'aga wannan kaya ya kalla sai ya d'aga wancan ga kud'in kuwa ya rike a hannu gam ya kasa ajiyewa kaman wani ne zai kwace mishi.

"Bintu.... Bintu Allah yayi miki albarka yanzu wannan duka a dalilin 'yar albarka na samu dama ai wannan yaron kana ganin shi kaga dan albarka shima, ko ba shi bane na gan su tare kwanakin baya?" Ya tambaya yana ta washe baki.

"Shine mana ma'aikacin hukuma ne ai, ni ko soja tace min ne ko d'an sanda, na manta dai" Inna ta bashi amsa ta kauda kai kada dariya ya sub'uce mata ganin yanda nan da nan Baba fuskar shi ta canza ya koma kalan fargaba da tsoro.

"Oho ashe hukuma ne, toh yayi kyau madallah da har ina cewa in naga ya dawo zanje in mishi godiya kuma muna gaisawa ashe yafi karfina". Baba ya fad'a bakin shi na rawa.

Inna had'iye dariyar ta tayi ta juyo tana kallon shi can ta ce," haba Mallam wani irin magana ne wannan, uhum sirikin naka shine yafi karfin ka?"

"Kema dai Bintu da son jan zance kike kin san bana shan inuwa d'aya da hukuma, Allah yajikan Baban ki ai ta nan ya rinjaye ni nayi ta bashi kud'i mudin in ya tambaya ko a wani waje sai naje na ciwo bashi na kawo mishi duk da shi na san yayi ritaya amma nake tsoron sa balle wanda yake saurayi mai jini a jika?

Hmmm ke dai kawai ki cewa 'yar albarka ta mik'a godiya ta a wajan sa".

"Toh shikenan Mallam zan fad'a mata" Inna ta bashi amsa.

Tun daga wannan rana Baban mu shima ya koma d'an gaye daga ya canza wannan sai ya cire wancan har a majalisan su yanzu shi yake mulki kowa so yake ya zama makusancin shi, maimakon kud'in nan daya samu ya juya su a kasuwanci suyi albarka ya rike gidan sa kaman kowani magidanci saima lalacin nasa ya karu d'an masarar da yake sayowa ma yanzu ya daina ba abinda ya shafe shi da lamarin cikin gida illa ya d'au wanka ya shigo d'akin mu yayi breakfast ya tura kud'i a aljihu yayi ficewar shi.

Aike kuwa Yaya na bai daina yi mishi na kaya dana kud'in duk bayan kwana bibbiyu yake aikowa, ranan da ya rasa na kashewa kuwa ni yake tambaya in bashi dan ya san ko ya tambayi Inna ba bashi zatayi ba.

Wahalar da muke ciki yanzu ya dawo kan Inna Asabe dan itace mai yara dayawa a gidan ga babu abinci babu jari balle ta daurawa yara sana'a, kananan yaran ta kullum a d'akin mu suke cin abinci.

Rannan Gwaggo Aisha bata gida Inna ta fito ta kawo mata rabin bugu na shinkafa da kuma carton na taliya sannan ta bata dubu goma tace tayi jari ita mai yara kanana zama haka ba zai yiwu ba.

Kuka wiwi ranan Inna Asabe tasa tana Inna ta yafe mata abubuwan da tayi mata a baya gashi wacce ta biyewa sukayi mata rashin mutunci yanzu babu ruwan ta da ita koda zasu wuni su kwana basu ci ba kuma basu sha ba ko a kwalar rigar ta sai wacce suka wulakanta itace yau ta mutumta ta haka?

Inna Asabe tun daga wannan rana ta samu abinyi itama kuma tun daga wannan rana ta fita harkan gwaggo Aisha tsakanin ta da Inna ta kuma sai mutunta juna.

**********************************

*Rubby private school* makaranta ce mai matukar tsada ta 'ya'yan masu kud'i ko manyan 'yan kasuwa, anan Yaya na ya nemo min gurbin karatu na fara fita ss1 abina kuma ya ajiye min mai napep da yake zuwa ya kaini kullum da safe kuma ya d'auko ni in an tashi, wata nayi kuma ya biya shi kud'in sa.

Maryam Alhaji idris itace seat mate d'ina tun ranan mu na farko da had'uwa muka kulla k'awance da ita domin Allah ya had'a jini mu sosai.

Kasancewar Maryam tana kusa dani yasa al'amarin makarantan yazo min da sauki, sosai take taimaka min kana ganin ta kaga wayayyiyar yarinya 'yar gayu tsabanin mu namu wayewar kauyenci ne a wajan su.

Ba'a magana da hausa sai turanci a makarantan abinda ya fara bani matsala kenan sannan kuma in ana koyarwa shima sai turanci ko kad'an basa d'an sirka hausa yanda irin mu zamu fahimta sai dai in an gama koyarwa Maryam ta kara wayar min da kai.

Term d'aya kawai mukayi na canza nayi wayewan 'yan gayu ga turanci ya fara zama a bakina domin makarantan ba wasa.

A wannan lokaci ne kuma aka saka bikin Hajara da Alhaji data samu ,wata biyu kawai aka saka Gwaggo Aisha sai habaice-habaice take 'yar ta zata je gidan hutu gidan kud'in halal bana yankan kai ba, wai kud'in Yaya nane na yankan kai.
Chapter 14 · 0% Book details