← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 71

Sashe 64

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin zan dago yasa ya fuske yana " ai ba wani abu bane dan mutum yana aiki ya yanke a kitchen, it's normal ai" a'a ni dai nagode kaje ka huta" nace ina karbe wukan daga hannun sa.

"Ok toh ki bani wani aikin" yace min bashida niyyan fita ko kadan " hmmmm " kawai nace na cigaba da girki na, shi kuwa kememe yaki fita yana nan tare da ni duk abinda na kama zanyi sai ya saka hannu wai shima sai yayi har tuka tuwon ndalayi shima saida yasa hannu, duk yanda naso daurewa in rabu dashi kasawa nayi na rinka dariyan sa.

A haka muka karasa aikin yana ta min shirme kala kala ina shan dariya na, tare muka jera abinci akan dining sannan na wuce daki na bar shi domin magariba ya gabato, wanka na fara yi sannan na d'aura alwala na fito na shimfida abin sallah na kabbara sallahn magariba jin har an fara a wasu masallatai.

Ban fito parlour ba bayan na idar da sallahn na cigaba da da addu'oina har aka kira Isha'i shima nayi sannan na mike tare da cire hijabin dake jikina na ninke na ajiye a wardrobe,ina kan ninke sallaya wannan fitinannen kamshin sa mai saka natsuwa ya fara min sallama sannan naji muryan shi mai cike da natsuwaa yayi sallama.

Amsawa nayi tare da ajiye sallaya a mazaunin shi " fito muci abincin mana ni yunwa nake ji" yace yana shafa cikin sa, murmushi nayi ina kallon yanda kananan kaya da ya saka ya matukar kara fito da kyan sa da alamu shima wankan yayi.

Gyada kaina kawai nayi muka fito, shi ya ja min kujera na zauna sannan shima yaja na kusa dani ya zauna ba bata lokaci na fara serving d'in shi zan zuba nawa ya rike min hannu wai in bar wannan d'in ma ai ya ishe mu.

Kallon shi na tsaya yi cike da mamakin ta yaya zan iya cin abinci tare da shi? Ganin irin kallon da yake min yasa na sauke nawa idon nayi shiru, Bismillah ya min ya d'auki loman farko ya kai bakin shi

"Hmmmmmm delicious wow..." Yace yana wani lumshe ido ya juyo yana tauna abincin da yake bakin shi cikin wani salo mai burgewa " jinjina ga Innar mu, gaskiya da za'a bud'e eatery ana saida girkin ta na tabbata people will go crazy" yace yana kara kai wani loman bakin shi ni dai sai bakin nashi nake kallo ina jin farinciki yanda yaba min Inna ta.

"Open ur mouth girl kiji yanda yake nasan sai kin fin santi " yace yana nufan bakina da spoon d'in da ya debo abincin, Bai tsaya jirana ba ya kai abincin direct cikin ikon Allah ban iya musa mishi ba na bud'e bakin ya juye min abincin.

Tsatsare ni da ido yayi yana kanne min ido d'aya yace" ya kika ji? Nasan tunda kika fara girkin nan ba kiyi testing ba". Murmushi kawai nayi ina taunawa a hankali.

Haka ya rinjaye ni da wasa da dariya muka cinye abincin dana zuba mishi malmala 2 har ya kara mana ban ankara da irin lodin da nayi ba sai da naji ciki na yana barazanan fashewa sannan na cire hannu na ina cewa na koshi.

"Haba dai nida nake Shirin kara mana zaki ce kin koshi?" Yace yana min wani kallon kasan ido wanda yake kara dagula min lissafi akan shi, girgiza kai nayi da wuri ina mai mikewa a wajan tare da fara tattara kayan da muka bata na kai kitchen na wanke su na ajiye komai a mazaunin shi sannan na fito a lokacin shima ya tashi a kan dinning d'in ya koma parlour yana kallo

.

Zuwa nayi zan wuce ciki yace min in zo in zauna mana muyi kallo ko hira in daina zama ni kad'ai a d'aki, samun kaina nayi da kasa musa mishi na dawo na zauna kusa dashi da yake yana zaune ne akan kujera 3 seats.

Mbc2 yake kallo ana haska wani film gashi nan shi ba advanture ba shi ba horror ba amma sai shegen dad'i,ni kuwa in akwai abinda na tsana shine horror film amma saboda dadin da ya min na kasa tashi a wajan muka kalla har zuwa karshe duk da a lokacin kaman kace min aaarr in fita a guce.

Ganin dare baiyi nisa ba ya mayar da tashan zuwa mbc Bollywood yana ai ya san nafi son Indian films ba Ni kad'ai ba most haka mata muke, murmushi kawai nayi ba tare da na musa mishi ba dan na san gaskiya ya fad'a ina bala'in son kollon duk abinda ya shafi India.

Raaz shine film d'in da suke haskawa a wannan daren yayi bala'in dad'i amma akan fatalwa akayi film d'in ga d'an banzan tsoro gaba daya tsigar jikina sai mikewa suke saboda ina masifan tsoron abinda ya danganci fatalwa ji nake kaman gaske ko hiran naji anyi dare nayi zan ta tuno da labarin in kasa bacci wani lokacin sai na koma dakin Inna nake samun bacci

Bamu gama kallo ba sai wajan 12:30 , duk a tsure nake ina tunanin ya zanyi bacci yau? Haka na daure nayi mishi sai da safe na wuce d'aki na ina ta waige-waige duk da ga hasken fitulun d'akin kaman rana amma ji nake zan ga gilmawan wani abu, wankan ma a gurguje nayi shi na fito nazo gaban mirror da lalume na kwashi turaruka na koma bakin wardrobe sannan na bud'e ido na wai duk ji nake in na kalli madubi a wannan lokacin zan ga wani abin tsoro.

Rigan bacci na saka irin mai guda biyun nan na cikin karami ne mai hannun shimi ga tsayin shi bai wuce guiwa ba
sai na saman shi da yake dogo har kasa da dogon hannu sai dai gaban a bud'e yake sai igiya ta tsakiya da mutum zai daure in ya saka, turarukan na feffesa na dawo kan gadon na kwanta da tsoro fal a raina bayan na ajiye dogon rigan baccin a gefena na jawo bargo na rufu sannan na fara addu'oin ina ta shafawa a jikina.

Kasa kashe wutan d'akin nayi na lumshe ido da sunan bacci amma sai na kasa baccin sai films din suke ta dawo min kaman yanzu nake kallon,wani motsi motsi kunnuwa na suka fara jiyo min ta gefen gado, cikin hanzari na jawo bargon na rufe har kaina tare da kara rutse ido na da karfin gaske ina karanto duk addu'an da yazo bakina.

Bargon da yake tab'a ni ji nayi kaman mutum ne yake min tafiyan tsutsa da mugun gudu na wacalar da bargon na mike jikina na bari, dakin na tsaya kallo kaman me neman wani abu tsaban na saka tsoron a raina har golmawan inuwan mutum na gani, ban san lokacin da na kurma ihu da dukkan karfina ba na manne a jikin bango jikina na kara bari gumi sai tsiyaya yake a jikina.

A bangaren Zafar kuwa zuciyar shi fes ya shiga dakin shi ya hau cire kaya, yana gama cirewa ya fad'a bathroom dan yin wanka yana imagining ina ma muna tare da ba abinda zai hana muyi wankan tare.

"Sannu bata hana zuwa" yace yana lashe lips d'in shi na kasa tare da rarrashin kan shi cewa ya kara hakuri tunda har na fara sakin jki dashi mun kusan zama abu 1. Koda ya fito daga wankan singlet da boxer farare kal ya saka yabi jikin shi da turarukan shi masu kamshin gaske sannan ya kara karfin Ac yana shirin hawa gado yaji razqnannen ihu da na sake.

A guje ya fito bayan yayi wurgi da remote din hannun shi ya banko kofan d'akin ya shigo can ya hango ni manne da gini duk na fita hayyacina in banda karkarwa da gumi ba abinda jiki na yake, da gudu ya karaso wajena yana tambayana meya faru?.

Ina jin muryan shi na juyo na fad'a jikin shi tare da kankame shi ina cigaba da kukana, shi kuwa sai da yayi suman kusan ten seconds sannan ya dawo hayyacin shi,hannayen shi duka 2 ya saka ya kara manna ni ajikin sa yana aikin sauke tagwayen ajiyan zuciya yana jinsa a wata duniya daban, da kyar ya samu ya had'iye wani busahhen yawu daya tokare mishi makokoro sannan ya samu bakin magana.

"M.....meyaaa.. faru...? Yace yana hada kalmomin da kyar.

"Ni tsoro nake ji ina ta jin motsi a dakin nan kuma na san fatawa ne irin na film din da muka kalla dazu ne ta biyo ni" nace cike da kuruciya.

Wani irin dad'i ne ya lullube Zafar yaji kama ya daka tsalle dan yaga zallan kuruciya a magana ta kuma ya samu hanyan da zai kara samun kusanci dani.

"Ya Salam baby, kin san all these ghost stories are real? Shiyasa ban so mu kalla ba but saboda naga kina so muka kalla just kiyi addu'a ki kwanta ba abinda zai faru" yace min yana karamto duk addu'a da yazo bakin shi kan ince mu kwana tare ko in bishi dakin shi.

Saurin rike mishi singlet nayi ganin zai zame ya fita ya bar ni " Dan Allah kada ka fita ka bar ni Dan Allah".

Wani munafikin murmushi ya saki ya sake dawowa baya yana kara kire ni da kyau yana godewa Allah da yasa muka kalli horror films d'in nan. " Shhhh it's okay gani nan babu inda zan je, muje ki kwanta I'm with you".

Sake shi nayi na juya a hankali na fara tafiya zuwa bakin gado shi kuwa yabi kafafuna da suke waje da kallo yana had'iyen yawu, zama yayi gefen gadon yana kare min kallo dan duka rabin kirjina a waje yake.yana ganin zan bud'e ido ya dauke kan shi da wuri Yana " toh kina nufin Ni kwanan zaune zanyi kenan?" With much hope din nace ya hau gado ya kwanta.

"Akwai bargo a cikin wardrobe ka dauka sai ka shimfida ka kwanta a nan" nace mishi ina nuna mishi kasa gaban gadon.
Chapter 64 · 0% Book details