← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 71

Sashe 35

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon hannun nawa nayi wanda ya koma jajawur saboda azaba su kuma a haukan su suna yabawa sun zata zallar soyayya ce, cike da jin haushin su na juya musu baya tare da jan duvet na rufe har kaina, ina jin su suka cigaba da suratan su daga baya suka hakura suka kwanta bacci.

Basu dad'e da kwanciya ba duk sukayi baccin su hankali kwance, tashi nayi na zauna ina kallon su cikin sha'awa ni da nake jin ido na a bushe babu alaman d'igon bacci, ba yau kad'ai ba tunda maganan auren nan ya tabbata na rabu da bacci mai dad'i dan sai in d'auki lokaci Mai tsawo ban runtsa ba, ko kuma na samu baccin ya kwashe ni daren yana rabawa rabi sai in farka kuma wani lokacin ya tafi kenan wani lokacin kuma sai kusan asuba zai kara sace ni.

Yanzu ma da naji kwanciyar ya ishe ni na shiga bayi nayi alwala nazo na tada sallah tare da neman agaji wajan ubangiji na.

A b'angaren su Zafar kuwa yan uwan Abba cikin farinciki da Kuma yaba yanda iyaye na suka karrama su suka isa gida yayin da yan uwan Mom sai tab'e baki suke wai ya rasa inda zai nemo aure sai a wannan gida kaman akurkin kaji.

Shi kuwa Zafar ko bai kula kowa ba ya shige part din shi ya kulle kan shi a ciki dan kowa ma haushi yake bashi, duk yanda abokanen shi suka so su gan shi bai yiwu suka wuce.

********************
Hausawa sun ce rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, toh hakane ya kasance a yau asabar itace ranar daurin auren kaman yanda naji suke fad'a kuma nake gani a yanzu duka gidan ya kaceme da hayaniya kowa sai hidiman gaban shi yake, masu gyaran gida nayi masu girke-girke nayi masu wanka ma nayi.

Ni kuwa ina can kuryan d'aki abin duniya duk ya ishe ni ganin cewa fa da gaske ne auren nawa za'a daura maimakon na tsinci kaina cikin farinciki kaman kowace amarya sai dai ni a bakinciki na tsinci kai na dumu-dumu ga kewan Yaya na da ya dawo min sabo fil, na san da aure na da shine da nafi kowa farinciki a rayuwa amma sai gashi yau da wanda bai sona bai san daraja ta ba za'a had'i ni aure.dashi wace irin rayuwa zan shiga???

Kuka naji mai tsanani ya taho min na tausayin kai na, mikewa nayi ba tare da na kula 'yan mata da suke ta hayaniyar su ba na shiga
bathroom dan in samu sukunin yin kuka na ko zan ji saukin rad'ad'in da zuciya ke min.

Zama nayi dirshan a ciki na kama kuka kaman rai na zai fita ji nake kaman rayuwa ta tazo karshe ji nake shikenan nayi ban kwana da farinciki a rayuwa ta ji nake kaman na yanki ticket na shiga kunci na har abada.

Ban san iya adadin lokaci da na d'auka a bathroom d'in ba sai knocking da naji ana yi a kofan yasa na d'an tsagaita kukan tare da maida hankali na kan mai bugawan.

"Zo ki bud'e kofan nan Zareefa" naji muryan Inna daga waje, goge hawaye na na shiga na nufi kofan na bud'e tare da komawa gefe kai na a kasa naki yarda mu had'a ido da ita, shigowa tayi ciki tana bin fuska ta da kallo.

"Rufe kan ki kikayi kina kuka ko?" Ta tambaye ni still tana karantar yanayi na ta maida kofan ta rufe, maimakon in bata amsa fad'awa nayi jikinta ina mai kara rushewa da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro balle ita da take mahaifiya a gare ni.

Rungume tayi itama tana kokuwa da nata hawayen dan kada su zubo da kyar tayi nasaran maida su sannan ta dago ni tana share min hawayen fuska ta tanayi wasu na kara zubowa.

Murmushi d'auke a fuskata ta take kallo na sannan ta fara magana " toh menene abin kuka anan kuma uhum? Yakin matan kenan muma haka aka rabo mu da gidajen zuwa inda bamu saba kuma muka d'auki hakuri da juriya muka saba kema hakuri zaki yi wata rana sai labari.

Aure bautan ubangiji ne a gare mu mata shine kuma mafi saukin hanyan shiga aljanna in min bi Allah kuma kika yiwa mijin ki biyayya kaman yanda Allah ya umarce da muyi toh tabbas zaki rabauta, miji a duk yanda kike tunani a musulunci ya wuce nan miji babban jigo ne a rayuwar 'ya mace tunda da zaran an kai mace d'akin mijin ta shikenan komai nata ya koma hannun shi ko iyayen ta basu da iko a kanta ko kad'an misali koda mutuwa akace nayi in yace ba zaki zo jana'iza ta ba dole ne kiyi hakuri ki zauna kiyiwa mijin ki biyayya...."

A razane na dago jajayen ido na da kuka ya rina ina kallon ta ina son yin magana amma na kasa sai baki na da yake ta karkarwa.

Gyad'a min Kai tayi tana mai cigaba da murmushin " irin wannan biyayyan ake son mace tayi a gidan mijin ta, nasan yanda kike ji na san abinda kike tunani amma ina mai baki shawara a matsayi na na mahaifiyar ki, ki cigaba da hakuri kiyiwa mahaifin ki biyayya insha Allah gaba ba mu ba ke da kan ki sai kinfi mu alfahari da wannan aure zan cigaba da yi muku addu'a insha Allah komai zai dai-dai ta .

Yanzu kiyi wanka ki fito ga masu miki kwalliya suna jiran ki a d'aki" tana fad'an haka ta wuce ta fita ta ja min kofa bata tsaya a ko ina ba sai bathroom din ta,ta fashe da kukan da take ta dannewa tun d'azu " ya Allah ka taimake ta ka kare ta kada ta fuskaci irin rayuwar da nayi a cikin gida na ya Allah ka sanyawa rayuwar auren ta albarka".

Haka ta cigaba da kukan ta tana sumbatu domin a kullum daurewa kawai take ace a aurar da 'yarka ga wanda baka san daga inda yake ba balle ayi bincike a san halin shi babban tashin hankalin ta shine bata da daman cewa komai akai saboda mahaifiyarta ta gargad'e ta tun farko, amma ba zata daina fad'awa Allah ba ya bani ribar biyayyan da nayi musu.

Da kyar ta rarrashi kan ta ta daina kukan ta fito jin hayaniya na kara yawa alamun mutane suna karuwa kenan.

Ko da ta fito sai ta aro jarumta ta daurawa wanda take dashi a baya ta cigaba gaggaisawa da yan uwa da abokan arziki amma taki yarda ta kalli gefen da Maa take balle su had'a ido ta fahinmci tayi kuka, sai dai bata sani ba ta makaro domin Maa ta riga da ta gane halin da take ciki, murmushi kawai tayi tana yaba jarumtar 'yar tata.

Bayan fitan Inna daga bayin sabon babin kuka na bud'e inayi ina mai tausayin kaina ta yaya zan iya yin biyyan nan da Inna take Fadi ga wannan azzalumin? Da kyar na rarrashi kaina na daina kukan na fara wankan sanadiyan takura ni dasu Maryam suka yi.

Koda na fito na kasa kallon kowa a d'akin sai kan stool na gaban mirror naja na zauna kai na a kasa ba dan komai ba sai dan bana son yawan magana, su kuma masu make-up suna ganin na fito suka iso dan yin aikin su, ban hana su ba kuma banyi musu gardama ba suka fara min sai dai yau light make up sukayi min amma duk da haka ba karamin kyau nayi ba, Maryam da jikin ta duk yayi sanyi ganin yanayi na ta d'auko musu trolley da aka saka kayan da zan saka yau da safe ta kawo musu.

Su suka taimaka min na shirya cinkin wata expensive lace fari sol dashi yasha diamond stones, ni dai tunda nake a rayuwata ko labarin irin lace din ban tab'a ji ba balle gani, headtie na wani yadi mai sheki suka nad'a min shima fari ne sai set na dan kunne da sarka harda zoben shi na pure diamond suka saka min.

Ba zan iya kwatanta muku yanda ni Zareefa nayi kyau a wannan rana ba just imagine it urself sai dai ko kad'an babu abinda ya burge ni a ciki in na tuna sabon rayuwan kunci da zan shiga ma sai inji kuka na neman kwace min.

Kawaye na suma sun fito cikin wani hadadden atamfa da sukayi anko kowacce sai zuba kamshi da haske suke zubawa ana jiran su angwaye su karaso dan karfe goma sha d'aya ne daurin auren.

A can gidan su Zafar suma haka suka tashi da shirye-shiryen gaske ba irin na jiya ba dan Baawa jiya bayan dawowar su daga gidan mu ta kai karan su Mom akan yaja musu kunne kada su zubar mishi da kima gidan surukai, aiko bata ji da dad'i ba wajan Abba dan sosai ya nuna mata b'acin ran shi sannan yaja mata kunne tayiwa 'yan uwanta magana kowacce ta kama kanta in ko ba zasu kama ba kofa a bud'e take duk su watse bayan son harkan k'ananan mutane, dole ta nuna tayi nadama a gaban shi da alkawarin babu wata b'araka da zata taso daga gare su sannan ya kyale ta ta koma ciki cike da tsana ta.

Sadeeq shine yazo ya tada Zafar daga bacci dan har tara saura yana kwance yana bacci cikin kwanciyar hankali abin shi, ya shirya tsaf cikin hadaddiyar shaddar shi ash color sai kamshi yake zubawa kaman shine angon,Koda ya farkan ma fad'a sukayi tayi shida Sadeeq din kan me yasa zai tashe shi yana cikin baccin shi mai dad'i.

Ganin yana son yaja hankali sauran abokanen su da suke parlour yasa shi yayi shiru yace toh yayi laifi kuma ya amsa ya tashi yayi wanka ya shirya ga Abba da sauran abokan su suna jiran shi su tafi wajan daurin auren.

Jin ya ambaci sunan Abba yasa ya mike Yana kumbure-kumbure kaman karamin yaro ya shige bathroom d'in shi dan yin wankan, dariya Sadeeq yayi sai da yayi Mai isar sa sannan ya ciro mishi kayan da aka tanada mishi domin d'aurin auren.
Chapter 35 · 0% Book details