← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 71

Sashe 43

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*37&38*

A hanyar su ta komawa gida sauran mata suna ta hira da santin gida na amma banda Inna da tayi jigum duk abin duniya ya ishe ta dama shiyasa bata son zuwa Maa ta tilasta mata dole tazo gashi ta ga abinda ya tayar mata da hankalin, alamu ya nuna cewa ni da Zafar babu matsala a zamanta kewar mu amma mahaifiyar shi itace babbar kalubele a cikin rayuwar aure na.

Duk yanda miji ya Kai ga son matar shi in har dangin shi basa kaunar ta toh fa babu zaman lafiya balle ace mahaifiyar shi ce sukutum bata son ta ai babu kwanciyar hankali, ajiyan zuciya ta sauke mai nauyi har Maa da take kusa da ita ta dago suka had'a ido, alama tayi mata da ido cewa kada ta tada hankalin ta sai sunje gida zasu nemi mafita.

Wani ajiyan zuciyan ta sauke tana mai lumshe idanun ta alamun ta fahimta, a bakin kasuwa mafi yawancin matan suka sauka kowacce zata nemi motan da zai Kai ta Anguwan ta sai su Inna, Maa, Maman Dije dasu Inna Asabe sune kad'ai aka karasa dasu kofar gida.

Maa bata shiga gidan mu ba ta wuce gidan ta su kuma suka shigo gida, a tsakar gida suka iske Gwaggo Aisha tana wanke wani abinta cikin bucket, sallama kawai sukayi kowacce ta wuce bangaren ta ba tare da sun tanka mata ba domin habaice-habaice take tana bin su da harara wai kwadayi yasa suka bi Inna, ita kuwa har duniya ta nad'e bata ga abinda zai sa tabi ta ba dan har abada a matar cushe matar biyan bashin take kallon ta.

Wankin ta bari tana cizon yatsa dan ba haka taso ba taso koda Maman Dije ce ta tsaya acikin su ta tanka mata sanin halin ta na bata barin ta kwana sai dai yau harda itan suka ki kulatan.

"Ai duk hanyan da zan bi sai nabi naga bayan ki Bintu baki isa kiyi walwala ba muddin ina numfashi a doron kasa sai nabi na kuntata rayuwar ku keda wancan kod'add'iyar 'yar taki" tana magana ne da dukan karsashi dake zuciyar ta fuskarta kuwa na nuna zata iya aikata koda kisa ne dan cimma burin ta.

Hajara da shigowar ta kenan gidan tana tsaye a bakin gate kuma tana jin duk kalaman da mahaifiyar ta take furtawa akan mu, hawaye take na tausayi mahaifiyar tasu kan rayuwar da ta zabarwa kanta kullum cikin addu'an neman shiriya take mata amma da alamu tayi nisa sai a hankali, hawayen fuskarta ta goge tsab tana ayyanawa dole ne tayi wani abu na dakatar da duka Shirin ta in ba haka ba ta san halin mahaifiyar ta zata iya aikata komai da ta fada koma fima.

Bayan ta tabi zuwa cikin parlour su da ko carpet din arziki babu, da tsaki ta shigo maimakon sallama ta zauna a kasa tana kara jan tsakin da karfi yanda zata ji tayi magana.

" Ke kuma lafiya zaki zo ki saka mutane a gaba kina ta jan tsaki kaman wata tsaka?" Gwaggo Aisaha ta tambaya tana mata wani mugun kallo dan harda ita cikin wayan da take jin haushin su kan ko kad'an bata son taji anyi maganan mu balle a fad'i laifin mu.

"Umma ki taimake ni zuciya ta zata buga, wannan kyakkyawan mijin da gida kaman aljannar duniya dani ya dace ba wannan kod'add'iyar yariyan ba" ta karasa tana kara b'ata fuska kaman zata fashe da kuka.

A mamakince Gwaggo ta juyo tana kallon ta fuskarta d'auke da alamun tambaya tace " wai maganan wa kike min kuma wwni gida?"

Sai da Hajara ta tab'e baki kaman abinda zata fad'a har cikin ran ta ne tace " hmmm maganan wannan kod'add'iyar yariyan mana 'yar gidan Bintu".

Cikin wani irin sauri tazo gaban Hajaran ta zauna tare da kamo hannayen ta duka 2 ta rike cikin nata fuskarta cike da tsansan farinciki tace " Hajara da gaske kike ?"

"Gyad'a kai tayi ta kwakulu hawaye tace" Umma kin gan shi kuwa kaman wani balarabe ga gidan ma yanda kika San a kasar waje kike, ni dai gaskiya ki taimaka in kwace su duka a hannun ta" ta karasa tana goge hawayen ta

"Alhamdulillahi!!! Allah nagode maka wannan mugun asiri da matar cushen tayi miki ya karye Hajara ta ta dawo gare ni" tace tana rungume ta harda kwallan farinciki a idon Gwaggo.

"Asiri gaskiya ce ni shaida ce tunda gashi nagani akan 'yata mafi soyuwa a gare ni amma kiri-kiri aka raba mu ba kya son a ambaci sunan su koda da wasa da mutum ya tab'a su gwara mutum ya shararawa uwar ki mari goma" Gwwggo ke fadin haka cikin kuka dan da gaske take farinciki dawowar tan domin tun ada baya itace abokiyar shawarar ta daga baya Kuma da ta gane gaskiya sai taja baya da ita.

Ta dad'e tana da burin yin wasu abubuwa da dama akai na da Inna ta amma ta rasa dawa zasu had'a Kai suyi domin Jameela kullum bata gida koda ta dawon ma a buge take shigowa.

"Kinga yanzu 'yar uwar ki halin da ta zabarwa kanta kenan bana ma samun ganin ta sai bayan satika ko kwanaki koda na ganta ma ba a cikin hayyacin ta take shigo min ba sai cikin maye dama kece kad'ai kika rage min ta raba mu da mugun asirin ta sai dai ta Allah ba tata ba gashi komai ya karye Alhamdulillahi" ta karasa cikin tsantasan farinciki da ta dad'e bata ganta a ciki ba.

Mayar hawayen idon ta tayi na tausayin mahaifiyar tasu sannan ta maye gurbin da murmushi tace " toh yanzu meye abin yi Umma?"

"Tun kwanaki Lantana ta min alkawarin kaini wajan wani boka da aikin shi yake kaman kaifin wuka, dama rashin ki a kusa dani yasa na bar maganan amma tunda komai ya warware zanyi mata magana mu tafi cikin kwanakin nan komai da suka mallaka sai ya dawo gare mu ".

***************

Shiru gidan kake ji kaman ba shine dazu take cike da mutane ba, duk sai naji babu dad'i Ina nan zaune a inda suka bar ni na kurawa tv da yake ta karaji shi kad'ai ido kaman kallon nake amma kuma hankali na ba anan yake ba ya tafi ga tunanin haka rayuwa ta zata kasance zama da wanda bai san daraja ta ba wanda yasha fada min da bakin sa ba sona yake ba, tunda aka kawo ni gidan nan ban abu wai shi farinciki ba ina dai zaune ne kawai in mun hadu banda mugunta ba abinda yake shiga tsakani na dashi.

A da nima haushi yake bani kuma in yayi min muguntan bana samun kwanciyar hankali har sai na rama amma a kwanakin nan ban san me yasa ba ko me yayi burge ni yake maimakon inji haushin sa, in yana zaune a parlor ko yana cin abinci nakan buya inyi ta kallon shi tunda ya min iyaka da inda yake yace kada in kuskura in zauna inda yake, so must time ko ina parlour in ya shigo zan tattara in koma nawa inyi ta leken shi wani lokacin nakan ji haushin kaina tare da tambayan toh me hakan yake nufi amma babu mai bani amsa.

Wani abin takaici ko cikin dare na tashi wani lokacin na kan leka d'akin shi,ina iya hango shi yana baccin shi cikin kwanciyar hankali, cikin d'an hasken dim light dake bari na gefen gadon shi ba na sanin ko minti nawa nake a wajan all I is ina dadewa sannan in koma in kwanta

Sallamar shi cikin azzakar muryan shi naji ya daki kunne na duk da ciki-ciki yayi ta dan na san baiyi tsammanin da mutum ba a parlorn ba, kasa amsawa nayi saima bin shi nayi da kallo har ya shige , yayi min matukar kyau cikin wani lallausan yadi maroon da ya saka anyi mata dinkin zamani irin iya cinyan nan kan shi babu hula sai bakin gashin kan sa dake sheki yana d'aukan ido.

Kara fitowa yayi sai dai wannan karon ya cire rigan sai farin vest ne a jikin shi murdadden jikin sa a wake, hannun shi d'auke da laptop yana duba wani abu gaba daya hankalin sa yana kai, ni kuma ina nan tsaye yanda ya barni na kasa motsawa a wajan duk da naga inda nake yake nufowa amma na kasa matsawa ina kallon yanda shima vest din ta zauna a jikin shi, wato shi komai ya saka sai tayi mishi kyau.......

Ina cikin zancen zuci naji mutum ya fad'o min mukayi baya tare kan kujera dake bayana ya kasance yayi min rumfa da faffadan kirjin shi, wani irin yanayi da ban tab'a tsintan kaina a ciki ba yau naji ni a ciki ganl kamshin jikin shi da kuma d'umin jikin sa da suka had'u suka bada wani yanayi na musamman, lumshe ido na nayi Ina addu'an Allah yasa mu dauwama cikin wannan yanayin Mai wuyar fassara.

Cikin wani irin zafin nama ya d'aga ni tare da hamb'are ni gefe na fad'i kasa dole na waro idanu na dana lumshe na sauke su a kan shi, kaman wanda ya tab'a Kashi haka yake ta kakkab'e jikin sa yana watso min mugun kallo kaman idanun shi zasu zubo kasa.
Chapter 43 · 0% Book details