← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 71

Sashe 47

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuruf ya mike yana cewa naga kwana 2 yana d'an sake min shiyasa na fara kawo mishi raini bari ya shiga ya gyara min zama, yana maganan ne tare da nufan d'aki na.

Hankali kwance nake sipping tea na naga mutum ya shigo min babu sallama sai wani had'a fuska yake wai shi ala dole zai tsoratani.

"Ke tsaban kin raina mutane shine har zaki shigo ki fita ba zaki gaida mutane ba?" Ya fad'a cikin tsawa.

Sai da na turo baki na dan kalle shi na watsar nace" ni dai banga mutane ba,mutum daya na gani a parlorn".

Mamakin da yake fuskar shi kasa boyuwa yayi yana bina da wani irin kallo, had'iye abin shi yayi ya Kara wani tsare gida yace" ohk in ma mutum dayan kika gani ba zaki gaida shi ba kenan, nd what do you mean by ki shiga daki ki zauna shan tea sauran mutanen gidan ba zakiyi musu girki bane?"

Sai da na kuma kurban tea na hankali kwance sannan na bashi amsa " I don't feel like cooking today"

"What!! Ni kike fad'awa u don't feel like cooking, kin ga ina bin ki a hankali shiyasa ko jira ni ina zuwa zaki min bayanin yanda ya dace" yana fad'an haka ya fuce fuuu kaman zai tashi sama, tab'e baki nayi na raka shi da ido wai ni zai rainawa hankali wai mutanen gidan me zasu ci, yace min dai me zai ci?.

No Abba da tun jiya nayi saving a wayata na kira na saka a handsfree na ajiye kusa da ni muna gaisawa Ina karasa shan shayi na daya rage ya shigo dakin a zafaffe da belt a hannun shi har zai bud'i baki yayi magana jin muryan Abban shi yasa yayi tsit yana zare ido, kallon up nd down na mishi ina murmushi Abba yace" da fatan kin tashi lafiya my daughter"

Kara kwantar da murya nayi sannan na amsa mishi da" yau na tashi da jiri da amai da zazzab'i Abba ko tashi bana iya yi shine na nemi alfarman ba zan iya shiga kitchen ba yau amma yake ta min fad'a"

"Mene! Yana ina, ki bashi wayar in yana kusa" Abba ya karasa a d'an zafaffe.

Ina kif-kifta ido kaman da gaske nace " gashi nan Abba" tare da mika mishi wayan, sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya saka hannu ya karb'a yana min mugun kallo, ni kuwa ko a jikina saima murmushin mugunta dana bi shi da ita.

"Assalamu alaikum Abba barka da safiya" yace cikin sanyin murya.

" Wa'alaikum salam son me nake ji haka kada ka kasance cikin mazan da basa kyautatawa iyalin su mana kayi koyi da manzan Allah dan ya kasance mai kyautatawa iyalan sa,ko kaga haka muke da Momyn ka?" Bai iya bude ya bashi amsa sai girgiza kai da yayi kaman yana gaban Abban.

"Kada in kuma jin irin haka try to be a good husband ok, nd get something for her tayi breakfast". Insha Allah Abba" ya amsa cikin sanyin murya sannan ya katse kiran.

Ina jira inga ko zai hau kaina da wannan masifan nashi amma ga mamamki na sai ajiye min wayan yayi ba tare da yace komai ba ya fita daga dakin, murmushin nasara nayi tare da gyra kwanciya ta kan kujera na d'auko wayata na shiga watsApp.

Bayan fitan shi kaman da minti 30 sai gashi ya kara shigowa da sallama da wasu shopping bags a hannun shi ya ajiye min harda na pharmacy a ciki da alamu magani ya sayo.

"Ga breakfast dinki da drugs ki sha bayan kin gama nd pls next time in baki da lafiya let me know" yana gama magana ya fita, ni abin ma sai naji shi wani bambarakwai wai yau Zafar ne yake min magana a nitse babu tsawa harda wani pls? Hmmm tab na yarda da maganan Yasmin da tace yana bala'in tsoron Abban shi daga waya sau 1 har ya sauya.

But sai nake jin kaman ban kyauta ba da na had'a shi da mahaifin shi har yayi mishi fad'a, wani bangare na zuciya ta na kara ingizani cewa sai me ai shima lokacin da yake takura ni bai tausaya min ba.

Bud'e ledan eatary nayi naga manyan package na take away guda 2 na farko cike da chips da kwai sai na biyun kuma cike yake da pepped chicken sai kamshi suke ba b'ata lokaci na d'iba na fara ci ina zuba santi,sai da nayi nak sannan na tattara sauran na kai kitchen ban gan shi a parlorn ba ban kuma bi ta kan shi ba nazo na cigaba da charting na.

******************

Washe garin ranan da suka dawo daga wajan boka Gwaggo Aisha tasa Hajara wanka da sassafe ta shirya wai ta taho gida na su fara aiwatar da kudurin su tunda wuri, bata musa mata ba ta shirya tsab tayi kwalliyar ta cikin doguwar rigar ta na atampa daya amshe ta sosai,tana bari tayi breakfast kamin ta fita amma ta hana ta tace in azo nan gidana taci.

Haka ta fito wajan 8 da wani abu ba tayi nisa da gidan namu ba ta samu kwata ta jefa maganin a ciki tayi wucewar ta, bata son zuwa gidan da sassafe haka ta san duk yanda akayi kila ko farkawa daga bacci bamuyi ba, tunda ta shigo anguwan da nake ta fara jan kafa dan bata san kowa a anguwan ba da ta shiga ta dan ja lokaci har sai Zafar din ya fita kamin ta shigo.

Dole haka ta karaso kofar gidan tayi knocking mai gadi yazo ya bud'e mata kofan ta shigo daga ciki sannan ta gaishe shi cikin girmamawa da yake ya dan manyan ta, amsa mata yayi cikin kulawa kasancewar yaji dad'in yanda ta gaida shin.

"Dan Allah Baba masu gidan sun tashi kuwa?" Ta tambaya shi lokacin yana shirin komawa dakin shi.

"Gaskiya bana jin sun tashi dan sai kusan goma sannan muke kin motsin farkawan su" ya amsa mata.

" Toh dan Allah zan zauna a nan kamin su farka" tace tana nuna mishi wasu kujerun roba da suke can gefe cikin furanni.

"Toh toh shikenan ki zauna sai sun fito" yace yana shigewa dakin shi, karasawa tayi ga kujerun ta zauna tana ajiyar zuciya samun relief ta ciro wayar ta daga cikin jaka ta fara game dan ya rage mata zaman kad'aici, ya ko taimaka matan dan bata san lokacin da taja a wajan zaune ba hankalin ta duk yana kan wayan taji saukan ruwa kaman daga sama a jiki ta, a firgice ta mike tana " innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" a masifance ta juyo da niyyan ciwa wanda yayi mata wannan danyen aikin mutunci sai dai tana jiyowa idanun su suka sarke dana juna shima ya taho da niyyan bata hakuri saboda sam bai kula cewa da mutum a zaune a wajan ba domin kullum yazo haka zaiyi aikin shi ya koma ba tare da yaga wani na gidan ba gwara shi Zafar din sukan had'u wasu lokutan.

Da kyar ya samu bakin bata hakuri cikin sanyin muryan shi da ya zame masa jiki, sai a lokacin Hajaran ta dawo hayyacin ta ta janye idon ta akan shi a kunyace tare da ce mishi babu komai.

Ajiye tiwon hannun shi da yake bawa flowers ruwa dashi yayi cikin sauri ya koma can inda ya ajiye kayan shi wajan Baba mai gadi ya d'auko wani babban handkie ya dawo duk tana tsaye tana bin shi da ido yazo ya goge mata ruwan da ya jika kujera da take kai sannan ya dube ta wannan karon fuskar shi d'auke da murmushi yace " ki zauna Hajiya kiyi hakuri wallahi ban lura da mutum a wajan bane d z an kullum Ina zuwa aiki ban tab'a cin karo da wani a nan zaune ba shiyasa".

Zama tayi a hankali itama fuskar ta d'auke da murmushin tace " kada ka damu na san ba da gangan kayi ba, nima na zauna a nan ne kamin masu gidan su farka daga bacci, ba matsala ka cigaba da aikin ka nagode".

" Toh Hajiya nima nagode" yace yana komawa kan aikin shi sai dai tunda ya fara hankalin shi gaba daya yana kan ta haka itama ta kasa natsuwa hankalin ta kacokan yana kan shi sai kallon shi take ta kasan ido dan ba laifi shima kyakkyawa ne gashi da hasken sa dan yafi ta haske sosai.

Suna had'a ido sai su sakarwa juna murmushi a haka har ya kammala aikin shi ya dawo wajan ta yana ko ya taya ta zama ne tunda har yanzu da sauran lokaci, bata musa ba ta bashi dama ya zauna sai gashi suna hira kaman sun dad'e da sanin juna kamin Zafar ya fita har sunyi exchange na phone number tsakanin su.

Zafar ya fito zuwa gaishe da iyayen shi kaman yanda ya saba ya shiga mota ya wuce su sun ga fitowan shi Amma shi sam hankalin shi bai Kai kan su ba yaja motan shi ya fita bayan mai gadi ya bud'e mishi gate.

Koda Zafar ya fita sai da suka kara kusan minti 20 tare kamin su rabu ta samu daman shigowa cikin gidan a lokacin ni kuma na gama breakfast nazo nayi kwanciya ta naji salkamar ta, cikin ihun murna na fito na rungume ta zan iya cewa bayan yinin bakwai da akayi sai yau wani nawa yazo min dan haka cike da farincikin na tarbe ta ina tambayan ta Inna ta da mutanen gida tace min duk suna lafiya.

Bayan gama gaishe-gaishe na gabatar mata da sauran abincin da na rage ta fara ci muna hira cikin tsananin farincikin da kewar juna.

Shi kuwa Zafar tunda ya tafi gidan su hankalin shi na kaina dan ya kasa sakin jiki suyi hira kaman yanda suka saba, bini-bini sai kallon agogo yake har Abban shi ya gano shi yace" ya kamata ka tashi ka koma gida son dan my daughter tana bukatan kulawar ka musamman a halin da take ciki yanzu".

"Wani hali take ciki kuma?" Mom da tundazu taki saka baki a hiran nasu ta tambaya a d'an rikice.
Chapter 47 · 0% Book details