← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 71

Sashe 56

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kaman minti goma yaji dawowar su tare da ingiza wani ya zube a kusa dashi har yana bige baba da yayi tangal-tangal kaman zai fad'i da kyar ya samu yayi gaining balance din shi ya zauna amma har yanzu bai d'ago ba balle yaga waye aka kawo.

" Kai d'ago ka dubi mutumin gefen ka nan" Baba yaji an daka tsawa amma duk da yaji muyar da akayi maganan sai bayi saurin d'agowa ba domin duk a zaton shi da wanda aka kawo yanzu suke, a babu zato balle tsammani yaji saukan gindin bindiga a gadon bayan shi har sai da ya kwanta saboda azaba " how dare you ana yi maka magana kana jin mutane". Yaji wanda ya buga mishi bindigan ya yace yana huci.

"kuyi hakuri ranka ya dad'e wallahi ban san dani kuke ba " ya amsa daga kwancen sai jujjuya kai yake na azaba da yake jin tana ratsa har kwakwalwan shi.

Wani irin shure shi yaji an kara yi da kafa har sai da ya mirgina gefe cikin wani irin babban murya yaji ance " kana kwance kake bawa oga amsa, sit properly my friend" yaji an kara daka mishi tsawa.

Duk da ba jin turancin yake ba amma sarai ya gane me yake nufi dan haka cikin dauriya ya yunkura ya tashi zaune yana b'ata fuska alaman har yanzu yana jin zafi, a hankali kaman mai tsoro ya kalli gefen shi mutum ya gani fuska a kumbure da kayar ma ake iya kallon kwayar idon shi.

Duk wannan kallon cikin second 5 yayi su ya sauke kan shi kasa ba tare da yace wani abu ba.

"Ka san shi ?" Yaji babban cikin su ya tamabya, Baba bakin shi har rawa yake wajan bashi amsa dan har yanzu yana jin zugin da bayan ke mishi " ban san shi ba ranka ya dad'e"

" No enough don't hit him " babban nasu ya dakatar da wanda ya dago bindigar shi domin kara kwad'a mishi .

"Ka gaya mana gaskiya bana son kana b'ata mana lokaci ka gan mu nan muna da abinda zamuyi muka tsaya anan muna binka a hankali ko in kana so in barka dasu su tambaye ka toh....."

" A'a wallahi Allah ranka ya dad'e ban san shi ba hasalima ban tab'a ganin shi ba. Baba ya amsa har yana katse shi jin cewar za'a bar shi da masu zallan muguntan nan.

"Nd you gaya mana gaskiya kace shine shugaban nan naku amma yace bai sanka ba " ya tambaya tare da maida hankali shi kan d'ayan mutumin da aka kawo shi yanzu, cikin dashassiyar muryan shi da bata fita sosai na alaman yaci wuya a hannun su ba na wasa ba yace " shine shigaban mu Mallam Hassan"

A zabure Baba ya d'ago da kan shi ya zubawa mutumin nan ido da yace shine shigwaban su kuma sai yake jin kaman ya tab'a sanin mai muryan, murmushi mai kama da kuka ya sakewa Baba da kumburarren fuskan shi ganin yanda ya zuba mishi ido yace;

"Baka gane ni ba ko Mallam Hassan? nine Abdulbasit yaron ka mafi kusanci da kai cikin yaranka wanda har kayi alkawarin bani Yar ka Zareefa da aure ka tuna, kana mamakin ya akayi suka kama ni bayan tarin makamai da ka bamu toh sun kama ni ne a hanyan mu na kaduna da ka saka mu muyi kidnapping minister man fetur ashe ba securities d'in shi da muka saya bane suka rako shi wasu sabi ne daban Kuma suma dan rashin amana basu gaya mana ba sai clashin mukayi dasu, munyi yunkurin guduwa sauran Allah ya basu sa'a sun gudu sai nine kad'ai suka kama sanadiyan harbi da suka min a kafan dama " ya karasa yana nuna mishi kafan shi na dama da yake a kumbure ya sha daurin bandage.

"Kayi hakuri wahala yasa na fad'a musu sunan ka da inda za'a same ka , yanzu ma tambaya suke menene Shirin mu na gaba shine nace baka fad'a mana har sai zamu fita aiki kake fad'a mana abinda zamuyi" yana gama magana ya sunkuyar da kai kasa alamun he is sorry for what happened.

Baki bud'e kawai Baba ke kallon shi ya kasa gaskata abinda yake faruwa kaman a mafarki ko Shirin film, tsoro, mamaki, firgici yasa ya kasa furta komai sai kallon wanda ya kira kan shi da Abdulbasit yake dan haka ko kad'an bai ji abinda babban sojojin yace ba sai gani yayi an had'a su waje d'aya an ingiza su zuwa wani babban d'aki sai dai wannan karan ba cikin duhu bane an bar su da haske , suna fita suka kulle su ta waje aka bar su su kad'ai.

********************

Ina farkawa da safe bayan na idar da sallah ban iya tsayawa nayi azkar d'ina da kyau saboda wani irin bacci da ya cika min ido har wani yaji-yaji yake min, nan na bingire kan sallayan ko hijabi na ban cire ba bacci mai dad'i yayi awon gaba dani.

A bangaren Zafar kuwa ko da safen ma kasa komawa baccin yayi zuciyar shi har yanzu zafi take mishi akan abinda ya faru tsakanin mu, sosai abin yake mishi zafi kuma yana jin dole ne ya koya min hankali but tayaya? Shine abinda yafi damun shi ya rasa ta yanda zaiyi ya hukunta ni.

Dik wani hanya da yake ganin ya cancanta yabi ya hukunta ni sai ya ga ba zai iya ba saboda zan cutu ta hakan sannan deep down him kuma baya son ma ya d'auki matakin saima hanyan da zai bi ya rarrashe ni yake nema dan shi kad'ai yasan abinda yake ji game dani.

Sai kusan karfe goma na farka ina mamakin irin baccin da nayi ban b'ata lokaci ba na cire hijabin jikina na nad'e sallayan na ajiye su a mazaunin su na gyara daki da parlour na tsab sannan na shiga nayi wanka da brush na fito da yake na san na sakawa kofa ta key shiyasa cikin kwanciyar hankali na shirya cikin riga da skirt na less light blue daya ji aikin stone sai walkiya suke.

D'an kwalliya nayi tare da d'aura d'an kwlin na fesa turare sannan na nufo kofa zuciya ta na bugawa ban san had'uwa ta dashi ya zata kasance ba yau, parlour na na fito na bud'e kofan main parlour ina leke ganin babu kowa yasa na fito abina kai tsaye nayi kitchen Dan yunwa na fara ji sosai.

Turus nayi a bakin kitchen d'in ganin Zafar a gaban coffee machine yana hadawa, jin motsina yasa ya juyo muna had'a ido na tsuke fuska ina shirin d'auke nawa idon ga mamaki na wani sasssayan murmushi ya jefo min wanda kana gani daga kasan zuciyar shi take.

Saura kiris in zubda ajina da nake kokarin karewa agaban shi domin a take naji notinan kai na sun kunce saboda ban tab'a ganin yayi irin wannan murmushin ba tunda na san shi shiyasa a take naji gaba daya jikina yayi lakwas.

Daurewa nayi na wuce shi zuwa wajan fridge na ciro kwai 3 da niyan soyawa sai ji nayi yana " ba sai kin sha wahalan soyawa ba, I have already made breakfast for you" yace yana nuna min wani hadadden tray mai d'auke da wani plate a rufe, d'auke kaina nayi na cigaba da fito da kayayyakin da nake bukata wajan girkin da nayi niyya.

Wuka na d'auko zan yanka albasa naji karaf ya rike min hannu wani mugun kallo na watsa mishi ina mishi kallon meye haka, shi kuwa marairaice fuska yayi harda wani langwab'e kai irin pls din nan.

Kwace hannu na nayi ba tare da nace mishi kala ba nayi hanyan parlour, saida yayi murmushi sannan ya biyo ni da tryn akan kujera ya same ni zaune na dafe goshi na da hannun dama dan na rasa abinyi ajiyewa yayi a gaba na ya koma kitchen din ya fito da mugs guda 2 da ya had'a coffee a ciki ya ajiye suma a gaba na sannan ya durkusa Yana leka fuskata.

"I'm very sorry for what happened yesterday dan Allah kiyi hakuri na miki alkawari hakan ba zai kara faruwa ba ki bar komai ya wuce let's be friends for the rest of the time we will spend 2geda" yace cikin sanyin murya.

Ban iya d'agowa ba nayi shiru ina sauraron shi dan na rasa a wani mizani zan auna maganganun nashi, dan sun dan sanyayya min jiki kamin in samu abin cewa waya ta da na bari a kitchen ya d'auki kara, kamin in mike har shi ya rigani mikewa kitchen din naga ya koma sai gashi ya dawo da waya ta a hannu ba tare da yayi magana ba ya miko min..

Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama maganar shi a zuciya ta na cewa ba girki da d'auko waya zai rinka yi ba ko menene zaiyi ba zai tab'a cin nasara a kaina ba tunda na riga da na gane manufarsa a kaina.

Hannu na saka na karb'a daidai wayar ya katse duba sunan nayi naga Dije ce babu bata lokaci na kira ta kaman kuwa jira take bugu daya kawai ta d'aga cikin ihu tace " kaji matan mayan Alhazawa basa d'aukan kira sai dai su kira mutum".

Murmushi kawai nayi dan yanda yake zaune kusa dani yana jin abinda muke cewa ba zan iya sakewa inyi magana yanda raina take so ba nace " Dije ba kya rabo da zolaya ya kike?"

" Lafiya lau Zareefa ya muka ji da wannan iftila'in daya fad'awa Baba ku?" Ta amsa min cikin sanyi.

" Wani iftila'i kuma Dije?" Nima na tambaye ta cikin rashin fahimta.

"Ke kuma akwai ki da wani zance, wani iftila'i kuwa banda wanda sojoji suka tafi da Baban ku"

" Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!!! Kawai nake iya maimaitawa cikin mugun tashin hankali da ban tab'a tsintan kaina a ciki ba, Baban mu a hannun sojoji toh meya faru meyasa babu wanda ya gaya min a gida.

Kuka na fashe da Ina" Baban mu sojoji suka kama Dije tun yaushe , meyasa babu wanda ya fad'a min"
Chapter 56 · 0% Book details