← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 71

Sashe 21

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tau kake ji suka d'auke wani saurayi da bindiga babu wani nisa tsakanin shi da Gwaggo Aisha.

Kaman kiftawan ido suka fara rige rigen cire kayan jikin su, aka kwashe duka aka zuba su cikin wani buhu sannan suka umarci driver da su shiga mota su koma cikin Maiduguri a haka.
[1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

*15*

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*15*

Shiru cikin motan kaman ba wani mai rai a ciki sai muryan mata da suke kuka kasa-kasa saboda kukanta su da akai babu mai kallon d'an uwan sa duk sun takure waje d'aya suna tunanin tayaya zasu shiga gari a haka? Ita kuma Gwaggo Aisha tana ganin kaman kaifin asirin Inna shi ya hana ta zuwa ga wannan mashahurin bokan har 'yan ta'addan suka samu daman yi mata aika-aika.

A wani kauye driver ya tsaya Allah ya sa akwai wani tsumamun riga da ya maida duster yana goge-goge dashi a cikin motan, shi ya saka ya fita ya karasa cikin kauyen yayi musu bayanin halin da suke ciki, nan da nan mai garin yasa aka hado musu suturu na maza da mata ya kai musu dan ba karamin tausaya musu sukayi ba.

Koda ya kai musu kayan kowa ya d'auka ya suturta jikin sa sannan suka mike hanya zuwa cikin gari.

Azahar dai-dai suka shigo driver ya zubar da kowa nan cikin tasha ya kama gaban shi, Gwaggo Aisha da kyar taja kafafun ta da har yanzu rawa suke saboda firgita ta fito ta samu adaidaita sahu zuwa gida duk da ta san bata da ko sisi a hannu.

A hanya ji take kaman kada taje gida ta wuce ko gidan 'yan uwan ta ko zata samu canza suturan dake jikin ta wai kada su Inna su raina ta, canza akalan tafiyan tayi daga gidan mu zuwa gidan kanwar ta.

Da yake duk tafiyar su d'aya da kanwar nata da taji abinda ya faru da Gwaggo Aisha maimakon ta nutsar da ita ko ta d'aura ta kan hanya saima kara zuga ta da ta rinka yi harda cewa ta samu kudi ta kara komawa, kuma kar ta kuskura ta nuna gazawar ta har sai ta kawo karshen Inna ta.

Da wayan nan kalaman nata ta kara karfafa mata guiwa, sai bayan sallahn magriba ta dawo gida hankalin ta kwance kaman babu abinda ya faru, anyi sa'a Jameela tana gida cikin murna ta tarbe ta kannuwan ta duk sun zaku da son jin daddadan labarin yanda sukayi da boka, Hajara tana yi mata sannu da zuwa ta fice ta bar musu d'akin tare da nema musu shiriya daga rabbi.

"Umma wannan wani irin magana ne haka kike cewa ko kuma dai sabon rainin hankali da kika zo dashi kenan?" Muryan Jameela ke tashi daga cikin dakin nasu cikin tsawa kaman ba da mahaifiyar ta take magana ba.

"Na lura tunda nace ki daina sana'a zanyi miki komai kika koyi wasa da kud'i saboda baki sha wahalan neman su ba, toh wallahi nima daga rana rin ta yau na daina baki kud'i na sai dai ki koma yin sanar ki dan ba zan iya ba" ta karashe tana harare-harare ita kad'ai.

Gwaggo Aisha kin kula ta tayi ta shige can d'aki ta rabu da ita domin ta lura asirin ta take son tonawa gaban kishiyoyi wanda ba zata tab'a bata daman hakan ba duk da kwanan nan alamun karara sun fara bayyana cewa Jameela ta fara tab'a shaye-shaye.

Hajara kam tana gefe tana sauraron su bata da daman saka.
baki Gwaggo Aisha ta hau kan ta da bala'i, Jameela ta gama suratan ta tayi ficewar ta.

Bata bawa kowa labarin abinda ya same su a hanya ba ta had'iye kayan ta amma ta kudiri aniyar neman kud'i tukuru domin ta samu tara kud'i ta koma wajan bokan ta.

Ko sati bai kai ba muka ga ta fara sana'ar ta na abinci kaman yanda ta saba sai dai banbancin yanzu almajiri keyi mata tallah saboda bata da yara kanana yanzu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wata rana dad'i wata rana kuma akasin ta, sai dai mu kam babu abinda ya canza a soyayyar mu sai ma karuwa da yake a ko wani dakika cikin zukatan mu.

Cikin ikon Allah yau muka gama waec d'in mu muka fito cikin farinciki muna taya juna murna tare da fatan Allah yasa mu fito da sakamako mai kyau, IV muka shiga rabawa kawayen mu na dinnern auren yayan Maryam Shamsuddeen wanda za'ayi sati mai zuwa.

"Yaushe zaki zo gidan mu muje saloon tunda shine kad'ai ya rage mana cikin shirye-shiryen bikin?" Maryam ke tambaya ta bayan mun fito daga makaranta.

"Toh uwar zumud'i in kin manta let me remind u auren fa saura sati". Nace ina aika mata da hararan wasa.

Dariya tayi sosai sannan ta ce" nafi ki sanin cewa saura sati kuma ai ba cewa nayi muje yau ba ko?"

"A toh ai na zata tsabar zumud'i yasa kin d'auka yau ne auren,ni ya kamata inyi wannan rawan kafar kin ga munyi waec d'in mu Allah yasa kada Baba yace sai anyi neco za'ayi bikin mu da Yaya na ayi mana yanzu wallahi in lokacin yin neco yayi sai ya rako ni muzo tare ina yi mishi 'yar...."

Duka da Maryam ta d'ad'a min a baya shi ya hana ni karasa magana ta, ina sosa wajan nace" ke me yasa kin cika mugun ta ne?"

"Ke ko kunya ba kya ji, bari in yi hanzarin zuwa gidan ku in fad'awa Inna tayi saurin aurar dake kada ....."

"Da kin taimaka min kuwa dan Allah zo muje ki gaya mata yanzu " nace in riko hannun ta.

Warce hannun ta tayi tana" Allah ya shirye ki Zareefa". Mukayi dariya dukan mu.

A nan mukayi sallama ta shiga motan su da driver yake jiran ta nima na shiga a daidaita da yake zuwa d'auko kuma ya kawo ni makaranta kullum kaman yanda Yaya na ya tsara.

Tun daga wannan rana bamu kara had'uwa da Maryam ba suna can hidima tayi musu yawa amma kowacce rana sai munyi waya kuma tana neman inje in taya ta wasu abubuwa sai dai kwata-kwata bana cikin natsuwa kasancewar Yaya na yau kusan kwanan shi 5 kenan da yin tafiya amma shiru bai dawo ba kuma wayar shi bata shiga balle inji lafiyar shi.

Wannan dalilin yasa bani da kwanciyar hankali sam shiyasa na kasa zuwa gidan su Maryam d'in, haka kawai kuma nake jin yawan fad'uwar gaba har na kasa daurewa na fad'awa Inna tace min inyi ta addu'a ba abinda zai faru.

A haka na daure nake dan al'amura na har ta kai gobe ne dinner gidan su Maryam kuma tun safe ta matsa min da waya kan yau bata son wani excuse lalle inzo da safe dan akwai abubuwan da zamuyi, ba dan ina so ba na amsa mata da toh kawai na katse waya ta dan rashin jin labarin Yaya na ya sanya bana jin dad'in duniya sam.

Da washe gari ma Inna ce ta matsa min akan in tafi tun safen tunda haka ta bukata ko akwai ayyuka da zan kama musu itama tana zuwa anjima kad'an,dole na na shirya nayi mata sallama na fita.

***********************

Tun jiya yaje tsadadden saloon da yake zuwa aka aske mishi gashin da ya tara kuma akayiwa askin zamani, sanin cewa in Abba shi ya gani ba zaiyi mishi da sauki ba , ko da yaji Abban nashi ya dawo duk daukin son ganin shi da yake sai da ya d'auko natsuwa da jarumta sannan ya nufi part din iyayen nasa cikin fargaban kada yayi mishi maganan aure.

A parlour ya tadda su zaune suna hira Abba na shan fruit salad da Momy ta had'a mishi da kan ta.

Kusa da kafafun shi ya karasa ya zauna tare da d'aura kan sa akan cinyan Abba ya kwantar, cikin tsantsan kaunar tilon d'an nashi ya hannu yana shafa kan a hankali fuskar shi d'auke da murmushi yana matukar son d'an nashi sai dai wasu halayan da ya kwaso marasa kyau ya d'aurawa kan shi yasa basa shiri, ganin sa cikin shigar kamala kad'ai yau yasa shi farinciki.

Babban burin shi yanzu shine yaga d'an nashi yayi aure ko zai natsu ya daina abinda baya so sannan shima girma ya fara zuwa mishi yana bukatan hutu yana son d'aura shi kan d'inbin dukiyar shi da shi kan shi bai san iyakar su ba.

Cikin girmamawa yayiwa Abban nashi barka da zuwa shima ya amsa cikin kulawa, zama ya gyara ya d'auki spoon d'in da Abba shi ke shan fruit shima ya fara sha yana kai na farko baki ya lumshe ido yace" Mom ji yanda wannan fruits din yayi dad'i amma ni in nace ki min ba yayin dad'i haka".

Mom tana dariya tace" kayi aure matar ka zata yi maka wanda yafi wannan dad'i".
Chapter 21 · 0% Book details