← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 71

Sashe 54

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Goge hawayan da suka cika mata ido Hajara tayi ta juyo tana kallon ta da kyau tace " Umma duk halin da baba na ya shiga dole ya dame ni tunda mahaifi na ne shi kuma a kowani hali yake ina son shi dan shine yayi sillan zuwana duniya kuma ina matukar alfahari dashi, sannan maganan Inna da kike cewa asiri tayiwa mijin Zareefa kema kin fad'a ne kawai amma kin san da asiri yana tasiri da kin dad'e da zama millionaire saboda haka babu inda zan je har sai naga mahaifi na ya dawo LAFIYA". Tana karasa maganar ta ta fice a dakin zuwa wajan su Inna ta kama musu suka cigaba da aikin tare.

Tagumi Gwaggo Aisha ta zuba tana kallon Hajara har ta gama ficewa daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tace " Ina murnan asirin ya sake ta ashe da sauran aiki a gaba na dole in kara d'aura d'amara yaki da wannan algungumar".

Hajara bata san ma tana yi ba suna can suna aikin su da sauran mutanen gida, jalof rice sukayi lafiyayye Inna ta saka yaran gida kiran almajirai suzo su karb'i sadakan abincin nan da nan kuwa suka cika gidan har da ma wayan da ba almajirai ba aka rarraba musu abincin suna karb'a bakin su d'auke da addu'a.

Su Baban Dije sai yamma likis suka dawo a gajiye ba tare da wata nasara ba , giwa Barack da 3-3 Barack suka je suka sha wahalan banza dan ko bakin gate ba'a bar su sun wuce ba sun dai wuni suna zagaye bakin gate d'in daga baya ma da kyar suka kwaci kan su a wajan sojojin bakin gate dan cewa sukayi basu yarda dasu ba.

Jikin kowa kara sanyi yayi jin babu wani labari gashi duk cikin zuri'ar mu babu wani mai kud'i balle mai mulki da zai tsaya mana wajan neman inda yake balle ayi maganan fito dashi.

"Gaskiya talauci baiyi ba, Inna ko za'a fad'awa Zareefa ne ko mijin ta zai iya taimaka mana a fito da Baba" cewar Hajara kenan tana share hawayen fuskarta.

"Kul kada inji wani yayi wannan gurguwan tunanin a cikin ku yaushe akayi mata auren da har irin maganan nan zai je kunnen mijinta, insha Allah zamu samu inda yake kuci gaba da addu'a, musamman ke Bintu kinyi tunani mai kyau da kikayi abinci kika sadakar hakan nada kyau sosai domin sadaka tana maganin musifa" Baban Dije ya karasa fada tare da wucewa bangaren shi.

Kowa haka ya watse cike da jimami tare da karfafa zukatan juna kan cewa za'a gan shin a cigaba da addu'a, har a wannan lokaci Gwaggo Aisha bata fito ba tana ciki tana jin mutane Hajara da ta shiga bata ma kalli inda take ba tayi wucewar ta uwar d'akar su itama Gwaggo Aishan bata ce mata ci kan ki ba dan a cewar ta sai ta tashi tsaye har yanzu asirin da Inna tayi mata bai gama sakin ta ba.

*******************

Zafar ya dad'e a dakina zaune a bakin gado yana dafe da kan shi da hannuwa duka 2 ji kaman yayi ta ihu ko zaiji saukin abinda yake damun shi dan ji yake zuciyar shi kaman zata fashe saboda azabar son kasancewa dani, ko da ba zai tab'a ni ba mu zauna waje d'aya yayi ta kallo na ma ya wadatar dashi.

"Ya Allah na roke ka yaye min wannan fitinan ko zan ji sauki a rayuwata" yace yana kara kallon kofan bathroom d'in, shi kan shi bai san adadin lokaci daya bata a zaune ba ya hakura ya fita ganin bani da niyyan fitowa.

Duk abinda yake ina kallon shi ta b'ulin mukulli sai dai banji abinda yake cewa kuma ko kad'an ba banji wani abu na tausayin shi a cikin rai na ba dan nasan ba abinda namiji ba zaiyi ba saboda cikar burin shi.

Ina ganin ya fita daga d'akin nima na fito na murza key a kofa ta na jingina a jikin kofan Ina sauke numfashi tare da lumshe ido sauran hawaye da suka mak'ale min suka samu nasaran zubowa, Allah ya sani soyayyar shi na wahal dani amma dole in kare kaina ba zan bari yayi nasara ba.

Shiryawa nayi cikin riga da skirt na wani material light blue ya min kyau sosai banyi wani kwalliya ba illah kwalli dana zira sai powder da wet lips, ina son fita amma ina gudun kada mu kara had'uwa da shi yasa nayi zama na a cikin d'akin ina chart dasu Maryam ina ce mata nayi fushi tunda taki zuwa inda nake tana bani hakuri wai zata zo kwanan nan.

Kiran sallah azahar ne ya tada ni daga kwancen da nake na shiga bathroom na d'auro alwala nazo na kabbara sallah, cikin natsuwa na idar na zauna nayi addu'oi na dan haka kawai nake ta jin gabana yana yawan fad'uwa.

Ganin zaman ba zai yiwu ba yasa na fito ina leka parlorn kaman wata barauniya cikin sa'a kuwa naga baya nan cikin sauri na shiga kitchen abubuwa dana girka dazu na had'a na mikawa Baba mai gadi bayan na zurmuka dogon hijabi na har kasa sannan na fita na bashi na dawo ciki.

Sabon girki na d'aura ba dan Ina jin yunwa ba sai dan farantawa Zafar har cikin raina ina jin dad'in yanda yake son abinci na.

Lafiyayyen white macroni da coslow nayi wanda ya wadatu da veggies sai kamshi yake, sabon warmer da ban tab'a amfani dashi ba na d'auko na zuba rabon shi na kara mishi da carrot juice na jajajjefa ice block a ciki na rufe tare da jera su akan maidaicin tray sannan na fito dashi kan dinning na shirya su a lokacin har an fara kiran sallah la'asar da alamu kuma har yanzu bai shigo gidan ba.

Komawa nayi ciki nayi alwala nayi sallah , sai a lokacin naji cikina yana kukan yunwa dan tun safe babu wani abin kirki daya shiga ciki na, fita nayi na zubo abincin a plate na dawo parlour na kunna kallo na fara ci ko rabi ban ci ba naji sallaman shi da wannan sabuwar muryan shi mai sanyi ba kaman da ba da sai yaga dama yake sallaman ko zai min magana cikin tsawa yake min.

Sanin muhimmancin sallaman a musulunci yasa na ansa ba tare da na kalle shi ba duk da zuciya ta tana kwad'ayin hakan amma na fuske naci gaba da cin abinci na.

"Kina fitowa main parlour muna ci tare mana , manzon Allah yace yafi albarka" yace bayan ya gama kare min kallo.

Sai a lokacin na d'ago na mishi kallon da baifi second 2 ba na d'auke kaina sannan nace " tun farkon shigowa ta gidan nan abinda na saba dashi kenan ,in ka manta ne in tuna maka cikin yarjejeniyan da mukayi na kamin wata 3 ya cika mu rabu kowa rayuwar shi zaiyi babu ruwan wani da wani so y all this?" Nace ina kara tsuke fuska ta da kyau.

Shiru yayi kaman bai ji abinda nace ba domin bashi da niyyan bani amsa nima kuwa ban damu ba na bawa iska ajiyr shi, ya kusan minti 2 a tsaye sannan ya fita sanyayaye, tab'e baki na nayi na cigaba da cin abinci na a zuciya ta Ina bari dai ai gwara da na tuna mishi yasan cewa ban manta ba balle ya cigaba da yi min wayo.

Kaina tsaye na fito yanzu babu wani tsoro irin na d'azu ga mamaki na yana zaune na gan shi akan dining ya saka abincin a gaba ya kasa ci yana dafe da kanshi da hannaye duka kana ganin shi kasan yana cikin damuwa, jin motsina yasa d'ago da kai yana bina da ido nazo na wuce kitchen ina jin wani iri a raina.

Jiki a sanyaye na ajiye plate d'in hannu na ina fuszar da iska a baki na, juyowan da zanyi naji nayi karo da mutum a firgice naja baya Ina zuba mishi harara domin na d'auki alkawarin ba zan tab'a bari yaudarar shi yayi tasiri a kaina ba.

"Meye haka ne Mallam, dan girman Allah ka daina bibiyata ka barni in sha iska" na fad'a a fusace ina kara jan jiki na baya.

Cikin muryar shi mai rauni ya fara magana " No I just want to..." Ban tsaya na saurare shi ba nabi ta gefen shi na wuce abina.

Ina shiga ciki na dafe zuciya ta da take bugawa kaman ya fito nayi Ina lumshe ido na zauna dabas tare da tunanin mokomata.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!!! Yake maimaitawa tare da jingina da jikin bango ya runtse ido , inama inama.... inama zai iya yayewa kan shi wannan damuwa da yake ji inama zai iya kyale ni kaman da, shi ba wani abu ba so yake kawai muyi magana na fahimtan juna amma naki bashi had'in kai, dole ne ya nemi mafita kamin wani abun ya same shi.

Fita yayi gaba daya daga gidan kaman d'azu dan gwara in baya gida ya kan ji sauki akan ya zauna dani karkashin rufi d'aya, gidan su Saddeq ya nufa kaman yanda ya saba kwana 2 nan kuma ko yaje baya iya gaya mishi abinda yake damun shi sai dai ya samu waje ya zauna ya zubawa waje d'aya ido duk kuwa yanda Saddeq zaiyi dashi ba zai ce kala ba sai dai in yaji da zaman ya tashi ya tafi abin shi.

A parking lot na gidan ya ajiye motan shi ya wuce part d'in Sadeeq kai tsaye sanin yana gida dan yaga motan shi a parking space, babu kowa a karamin parlorn nashi sai TV da yake ta aiki shi kad'ai.

Kan kujera ya samu ya kwanta tare da lumshe ido yana tunanin halin da yake ciki, Sadeeq ne ya fito a cikin bedroom d'in shi da waya a kunne yana waya da wani daga shi sai boxers da singlet alamun bai dad'e da shigowa cikin gidan ba.
Chapter 54 · 0% Book details