← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 71

Sashe 16

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan hidima anya batayi yawa ba, yau kuma harda zinare?" Inna ke fad'in haka cike da jimami.

" Yaya ne fa Inna meye abin damuwa saboda ya saya min kaya, ai ya riga ya saba yi " nace hankali na kwance kuma tsakani na da Allah na fad'a.

Shiru kawai Inna tayi ba tare da ta kara cewa wani abu ba kasancewar ta gane in banda tarin kuruciya babu komai a cikin kaina, abu d'aya yake sanyaya mata zuciya shine yanda bata sakaci wajan tsayuwar dare kuma duk a kaina.

A baya bata damu da lamarin Yaya na sosai ba kaman da yanzu na girma, duk da cikin hikima irin tasu ta manya tana jin yanda muke tsakani na da shi ko hannu na bai tab'a tab'awa ba.

Addu'an Allah yayi jagora ya tsare daga duk abin ki tayi ta tashi a wajan ni kuwa cikin zak'uwa da zumud'i na jawo kayan na fara kallo saboda dazu idon Inna ya hana in sake in kalla da kyau har na kosa goben tayi in saka kaya na.

Da washe gari da hayaniyan mutane muka tashi gidan mu ya cika ba masakar tsinke gaba d'aya sai naji na takura dan da naje da niyyan shiga bayan gida da gudu na dawo ina kakarin amai saboda yanda mutane suka b'ata shi, ba shiri na samu 'yar karamar jaka ta na had'a duk wasu abubuwa da zan bukata na zuba a ciki na wuce gidan Maa bayan na fad'awa Inna a can zan shirya sai in dawo.

Ko da na je gidan Maa itama bata zauna ba gidan namu ta tafi aka bar ni kad'ai a nan Inna ta aiko min da abincin safe da akayi na d'aurin aure,da yake safe ne sai na kasa ci na fito na samu yaro a waje na aike shi wajan mai shayi ya had'o min breakfast na nayi na kwanta bacci ni ban tashi ba sai kusan sha d'aya .

Ina shirin shiga wanka naga an ajiye min wani abincin bayan na safe, Allah sarki Inna ta na san wannan duk aikin ta ne, ban ci abincin ba sai bayan na fito daga wanka.

Lotion kawai na shafa na saka kayan da Yaya na ya kawo min jiya da daddare, aiko ya zauna das a jikina kaman an gwada ni irin gown d'in nan da bayan yafi gaba tsayi wani sarka da d'an kunnen kira Dubai data sayo min a baya shi nayi amfani da shi dan gold din Inna b'oye shi tayi tace ba zanyi amfani da shi ba,ko minti goma banyi da gama shiryawa ba kiran Yaya na ya shigo waya ta hijabi na d'aura akan kayan na fito.

Yau manyan kaya ne a jikin sa tsab'anin da ya murza hulan Ahaiyye a kan sa ya matukar kyau sai zuba kamshi yake.

"Yaya naaa ka gan ka kuwa kayi kyau sosai sai kace kai ne angon" na ce mishi ina dariya.

Murmushin sa mai sanyi ya yi min sannan ya ce" hmmm ke ba?"

"Ni me?" Na tambaye shi ina turo baki.

"Ke kanwa tace na ce".

"Kanwa only?" Na kara tambaya ina fiddo da ido waje.

"Baki kyauta min ba kin ki fad'a min auren nan in time balle in kawowa Baba wani abin kirki shiyasa na ki zuwa daurin auren,amma ki min magana da shi in bashi hakuri da gudumuwa na ko kad'an ne". Ya ce saboda kawar da wancan maganan da muka fara.

Gyad'a kai kawai nayi na juya ina dan dariya tun kamin inga draman da zai faru tsakanin Baba da Yaya na.

Allah yasa a hanya muka had'u da shi yana dawowa gida da yake ba a kofar gidan mu aka d'aura auren ba a can wani masallaci dake kan kwanan layin mu, yanzu haka suna tare da wasu 'yan uwan sa da sauran abokan shi ne a wajan bayan mutane sun watse.

"A'a 'yar albarka ke ce, ina zuwa kuma?"

"Baba dama wajan ka zan je, ummm...hmmmm wannan d'in nan da yake aiko maka da kaya shine ya zo yana so wai ku gaisa kuma ya baka hakuri da gudumuwan sa" na karasa kai na a kasa saboda kunya.

"Wai wannan mai zuwa wajan ki nan?" Ya tambaya yana zaro ido.

Danne dariyar daya taso min nayi ina gyad'a mishi kai.

"Toh meye sai mun gaisa da shi,naga a baya ke yake bawa ki kawo min ba yau ma ya baki d'in mana".

"Baba nima ban san dalilin da yake son ku gaisa ba yau amma tunda ya bukata kila yana da wani dalilin" na fad'a ina kallon yanda naga duk hankalin Baba ya tashi kaman ba yanzu na gan shi cikin annashuwa ba.

"Ki ce ya zo nan ya same ni ina jiran sa a nan " .

"Toh Baba" na ce tare da juyawa na koma wajan Yaya na sannan na fad'a mishi sakon Baba.

Naso bin shi inga yanda zasu kare da Baba sai kuma naga rashin cancantan hakan na tsaya jiran shi.

A nesa Baba ya hango shi yana zuwa yana saka wayar shi a aljihu wanda shi kuma Baba kallon bindinga sak ya yiwa wayan, nan da nan ko zuciyar Baba ta fara zillo kaman zata fito.

Cikin matukar sauri ya juya ya fara tafiya kaman zai kifa ya nufi masallaci inda ya bar mutanen shi suna jiran shi, yana cikin tafiyan kuma wani tunani ya fad'o mishi ya canza hanya zuwa bayan layin mu.

Yaya na yana zuwa wajan ya ga wayam bai ga kowa ba kaman zai koma kuma ya fasa ya karasa har bakin masallacin aka ce mishi baya nan, haka ya hakura ya dawo ya ce bai gan sa.

A hanyan mu na zuwa saloon sai murmushi nake dokawa ina hana dariya ta fitowa na san Baba k'in tsayawa yayi saboda tsoro.

Babban wani tsadadden saloon ya kai ni a west end wanda ba abinda basa yi na gyara da kamshi har da lalle, gefe naga Yaya na ya kira wata da alama ita ce babban su a wajan ban san me suka tattauna ba naga ya bata kud'i masu yawa ya fita, nan da nan suka shiga hidima da ni har da su drinks da snacks suka kawo min.

Ba b'ata lokaci suka warware yalwantaccen gashi na suka wanke suka gyara shi nan da nan kuwa ya kara kyau sai d'aukan ido yake, wanke min kafa suka yi a wani abin wanke kafa ni dai ban tab'a gani ba sai ranan,fara ce na su ma sun gyara sannan suka yaryad'a min lalle mai ja da baki.

Light makeup suka yiwa fuska ta daya kara fito da ainihin kyawu na, wani haddaden net mai kauri da yayi matching da kayan jiki na suka d'auko a shagon nasu suka nad'a min shi in a unique way.

Fad'an irin kyan da nayi ma b'ata lokaci ne dan sai in rantse da Allah ban tab'a sanin ina da irin wannan kyau ba sai yau, sai kallon kai na nake a madubi, su ma 'yan wajan sai yaba kyau na suke.

Da zan fita na fara kokarin saka hijabi na, 'yan wajan ne suka min caa wai kar in saka daurin net d'in zai lalace tun ban isa gidan auren ba,tunda a mota muka zo in tafi a haka.

Ba dan naso ba na fito a cikin saloon d'in ina takawa a hankali kaman mai tausayin kasa saboda tudun takalmin kafa na har na iso bakin motan Yaya na bai sani ba kasancewar ya kwantar da seat ya kwanta da earpiece a kunnen shi ban san me yake saurara ba.

Bud'e kofan motan nayi na shiga na zauna kamshin turare na shi ya isar da sakon isowa ta a gare shi ya bud'e ido ya sauke su a fuska ta da nima shi nake kallon, mun dad'e muna kallon juna daga baya nice na sauke nawa idon kasa ina d'an murmushi.

Ina jiyo shi sai da ya sauke ajiyan zuciya har sau uku sannan ya tashi ya zauna tare da gyara kujeran, ya juyo ya kara kallo na kaman zai ce wani abu kuma ya fasa ya tada mota muka kama hanyan gida,har muka iso babu wanda ya yi magana.

Yana yin parking na ce," nagode Yaya naaa zan shiga ciki sai anjima".

Har na bud'e kofan na fita bai amsa min ba na fara tafiya, nayi kaman taku uku naji muryan shi ya ce," Zareefa...."

Da matukar mamaki na juyo dan jin suna na a bakin shi yau.

" Kinyi matukar kyau....,kyan da baki ba zai iya furawa ba, amma dan Allah in muna tare ki rinka saka hijabin ki" yana gama maganan shi yaja motan shi ya tafi.

A hankali na juya zuwa cikin gida ina murmushi da mamakin me yasa yake yawan cewa in saka hijabi ba.

Ina saka kafa gidan mu ido ya dawo kai na kowa ni yake kallo da gudu Dije ta zo ta rungume ni cikin ankon da suka hana ni yi sai naga ashe da a lokacin ma naga ankon ba sai sun hana ni ba da kaina zance ba nayi.

Can b'angaren su taja ni muka tafi tana in bata labari meye sirrin?

A nan muka zauna ina bata labarin saloon d'in da muka je na fara jin sautin kid'a daga waje.

Da mamaki na ce", kaman kid'a nake ji?"

"Eh dama naji Hajara da kawayen ta zasu kawo DJ tun shekaran jiya suke zancen Ina ga shi d'in ne suka kawo" Dije ta bani amsa.

"Taso muje mu gani...taso muje" cewar Dije tana jan hannun na .

Muna zuwa kofar gida muka ga Amarya da kawayen ta suna ta rawa, jan hannu na Dije ta fara wai muma mu shiga nace mata ta shiga ina zuwa.

Ina daga gefe ina kallo kawai naga mutane sun rufu a kai na suna min liki, maza da mata amma mazan sun fi yawa na rasa ta ina ma suka zo dan ni dai ban san su ba.

Neman shiga gida nake amma sun tare ko Ina ba hanyan wucewa daga cikin matan naji wata tana ", ke Hindu ki zo ga Amarya nan kiyi mata liki"
Chapter 16 · 0% Book details