← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 71

Sashe 60

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Baban Dije ya sauke tare da furta " Allah ya kyauta, yanzu kowa ya fita a bar Yaya ya huta...." Bai gama rufe bakin shi ba kowa ya mike ana kara mishi Allah ya sauwake sannan muka fita tare da ja mishi kofa.

Maimakon Baba yayi baccin kaman yanda akace sai dai kunan da zuciya shi keyi ya hana shi jin rad'ad'in da jikin nashi ke mishi balle har yaji wani abu wai shi bacci, yanzu wannan 'yar cikin sace a haka har take mishi fatan mutuwa saboda abinda yayi musu. Tabbas ba zai taba ganin laifin kowa a cikin mu ba domin ya cancanci fiye da haka ma dama duk wanda Bai bi hanyar da Allah yace yabi ba dole zai ga sakamakon abinda ya aikata tun kamin akai ga zuwa kiyama.

Sai dai shi a yanzu babu abinda zaice sai ALHMDLLH ga Rabbil Izzatti daya ankarar dashi halin da ya jefa kan shi da iyalan sa amma ta ina zai fara gyara wannan babban barna da yayi???

Kuka sosai Baba yayi kaman karamin yaro Yana yi yana kara godewa Allah har la'asar tayi bai samu ya runtsa ba.

Gwaggo Aisha bata saki hannun Jameela ba sai da ta kai ta can cikin d'aki Dan ko a parlour basu tsaya ba, watsar da ita tayi a tsakar d'akin tayi taga-taga kaman zata fad'i da kyar ta samu courage ta tsaya tana auna mata harara tace" wai ke Umma meye haka ina cikin magana zaki wani jawo ni ki kawo ni nan kaman wacce ta fad'i ba daidai ba"

" Eh dole kice haka mana kina can kina kokarin tona min asiri cikin makiyana, ba zaki bari komai kike son cewa ki fad'a min a d'aki ba" gwaggo Aisha ta bata amsa itama tana mata mugun kallon.

"Ni ina ruwana duk inda naga dama zanyi magana ta kuma babu wanda ya isa ya hana ni, gobe zan dawo in karasa abinda nayi niyyan fad'a sai na fad'a wallahi" tace tana mai juyawa ta kama hanyar fita.

Cikin sauri gwaggo Aisha ta riko ta tare da fara rarrashinta kada tayi hakan domin ta san halin Jameela tsab zata aikata abinda yafi hakan ma tunda ba tsoron kowa take ji ba, da kyar ta rarrashe ta harda bata 200 kan ta bar maganan sannan ta hakura ta fita abinta cike da murnan ta samu na cakewa.

Duk yanda nake kuka Inna bata kula ni ba wucewa tayi ciki ta kama aikin gabanta, a nan parlour na zube kan kujera na cigaba da kuka na a wannan lokaci babu abinda nake so kaman in sanya shi a ido na domin akwai maganganu dayawa da nake son muyi dashi amma tayaya zan samu daman ganin shi waye zai kai ni???

Zafar gida ya wuce direct sai huci yake shi kad'ai a mota dan sosai kukan Zareefa ya tsaya mishi a rai shaid'an kuwa sai kimtsa mishi yake kan cewa kukan rabuwa da masoyin ta take, tsaki yaja tare da dukan staring da karfi Yana " da aure na akan ta take wannan kukan rabuwa da b'arawon ko kidnapper ko? Hmmmmm I will show her" yace yana dannawa mai gadi horn kaman zai cire mishi kunne.

Da gudu yazo ya bud'e gate d'in yana mishi barka da zuwa, ko kallon inda yake Zafar baiyi ba balle ya amsa mishi saima jan motan yayi dagudu kaman zai bi ta kan shi Allah ya bashi sa'a ya kauce cikin zafin nama yabi motan da kallo yana mamakin yau me ya b'ata ran mai gidan nashi haka ya shigo cikin fushi haka??

Ko parking d'in kirki baiyi ba ya fito cikin wani takun da zai tabbatar maka da ran shi a matukar b'ace yake ya nufi kofan parlour ya shiga ya kama safa da marwa shi kad'ai " na san yanzu Allah Allah take in sake ta dan ta samu komawa gare shi ko??" Ya tabayi kanshi.

Toh kai meye naka a ciki in ta koma gare shi ko ka manta ba son ta kake ba? Yaji zuciyar shi tana tuna mishi abinda ya manta " yes ba son ta nake ba but dole she should mind her business kamin in sa......" Yay shiru yana jin girman furucin da yake shirin furtawa kuma yana ganin abune da ba zai yiwu ba.

Jagwab ya zube akan kujera tare da dafe kan shi da hannu 2 yana mayar da numfashi dan ya rasa kalan tunanin da zaiyi.

Sai da yayi sallah la'asar sannan yaji zuciyar shi tana mishi sanyi kad'an-kad'an sakamakon tunanin da yayi na cewa yanzu fushi ba nashi bane dole yabi komai a hankali domin babu abinda fushin zaiyi saima kara jagula al'amura, sabon wanka yayi ya canza shigar sa zuwa shadda gezner armyn color d'inkin zamani kayan sun zauna sosai a jikin shi sai maiko yake amma bai saka hula ba sai lallausan gashin kan shi daya sha gyara yana d'aukan ido.

Cikin takun sa na cikakken namiji mai ji da class ya fito ya nufi motan shi bayan yayiwa kanshi wanka da turarukam shi masu dad'in kamshi, bai tsaya b'ata lokaci ba ya nufi gidan mu yana kara tausan zuciyar shi kan ya kau da idon shi kan duk yanayin da ya gan Ni a ciki saboda wannan kidnapper.

Ni kuwa a gida sai da Inna ta nuna min jan ido sannan na had'iye sauran kuka na ba dan raina yana so ba, nasiha tare da fad'a tayi min sosai akan kada In kuskura in kara nuna damuwa ta akan wani d'a namiji bayan miji na hakan zai iya haifar da babban matsala balle shi da kowa ya san munyi soyayya a baya.

Shiru nayi ina sauraron ta ba tare da nayi magana ba domin duk abinda zan fad'a ba lalle ne ta gane ba, ni ba kukan rabuwa da shi nake ba kawai dai ina kukan tausayin sa ne da kuma halin da yake ciki yanzu wanda nasan da kyar in za'a mishi sassauci a kotu, koma menene Allah yasa ayi mishi saukin.

Bayan munyi sallah la'asar muka ji sallaman Zafar a nan bakin parlour Inna, cikin azama Inna ta amsa tana gyara hijabin dake jikin ta dama bata cire ba ni kuwa ina kan sallaya ina ta rokon Allah ya fitar da Yaya na, sai da Inna tace mishi ya shigo sannan ya shigo kan shi a kasa kamshin turaren shi duk ya cika parlour.

A nitse ya kara gaishe ta ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa ya amsa yana tambayan ya jikin Baba ta amsa da sauki ta tashi ta fita zuwa d'akin Baba dan dubawa ko ya tashi.

"Let's go home" yace yana leken fuskata dan naki dagowa in kalle shi duk da ina jin yanda Inna ta zungure ni da kafa kamin ta fita sarai na gane nufin ta cewa in gaishe shi amma sai nayi kaman ban fahimci me take nufi ba na watsar dashi, " hello " yace yana shafa min gefen fuskata.

Cikin sauri nayi baya dan ban san lokacin da ya iso gaba na ba sai jifa na yake da tsadadden murmushin sa mai kara mishi kyau, Ni bai san duk haushin sa nake ji ba kan me yasa ya dawo yanzu dan nafi son in kai dare kamin ya dawo.

"Let's go home Baby yanda zan ji dad'in rarrashin ki kinga nan gidan Inna ne I will not be comfortable to do....."

"Ni ban nemi rarrashin ka ba pls leave me alone" na katse shi sabin hawaye na taruwa a ido na, zai kara yin magana muka ji muryan Inna tana sallama cikin sauri ya koma inda yake zaune da farko nima nayi saurin share hawayen fuskata tare da fara magana bayan na amsa sallamn Inna kaman tun farko hira muke.

"Eh ai tunda muka fito Baba yake ta bacci ban kara komawa wajan shi ba" na karashe da murmushi a fuskata, shima murmushin ya min yana kara tsunne kai ganin Inna ta shigo.

"Muje mu kara duba jikin nashi sai mu wuce gidan tunda kince kina son mu isa da wuri" yace da d'an muryan da Inna zata iya jinsa domin da ta shigo direct tayi hanyan d'akin ta ba tare da ta kalli inda muke ba, takaici naji ya cika min ciki Ni yaushe nace zan tafi har yake min sharrrin wai ina son mu isa da wuri?" kanne min ido 1 yayi yana dariya kasa-kasa, Ni ko baki na murkuda mishi ina hararran shi ta gefen ido.

Nuna kan shi yayi da yatsa yana kallo na alamun dashi nake, maimakon in bashi amsa sai kara murkuda bakin nayi murmushi yayi tare da cizon lip d'in shi na kasa, duk abinda muke akan idon Inna da take hango mu daga can cikin d'akin ta zuciyar ta fari ka ganin ma kwantar da hankalina.

"Zareefa"! Naji muryan Inna tana kwala min Kira, amsawa nayi tare da nufan d'akin nata cikin natsuwa.

"Ki tashi ku tafi kada dare yayi muku, ku biya kuyiwa Baban ku sallama sannan ku wuce" tace min lokacin da na karaso inda take zaune a bakin gadon ta.

B'ata fuska nayi kaman zanyi kuka na bud'i baki zanyi magana ta katse ni da " bana son jin komai wuce ku tafi".

Dole na fito ina kara b'ata fuska alaman saura kiris in fashe,yana ganin na fito shima ya mike yazo kusa dani ya durkusa kasa yayi mata sallama ta amsa da mu gaida gida, fuuu na fice na bar shi a baya zuwa sashen Baban mu na same shi zaune akan sallaya da carbi a hannun shi yana ja, kallon mamaki na bishi dashi wai yau Baba ne da carbi?.

Da sauri na shanye mamaki na tare da dukawa kasa muka fara gaishe a tare da Zafar da shima shigowar shi kenan, amsa mana yayi da kulawa kaman ba Baban mu da na sani ba a baya daga nan godiya ya kara yiwa Zafar shi kuwa yana kara tsunne kai yana babu komai saboda kunya wasu kalaman Baban ke bashi.
Chapter 60 · 0% Book details