← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 71

Sashe 7

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya kasa zama yayi a d'aki sai safa da marwa yake,sai yayi kaman zai kira wani kuma sai ya fasa can dai yaja wani dogon tsaki shi kad'ai yana," in banda b'atawa kaina lokaci nake ba ita Bintun yaushe har tayi wani abin kanta zan tsinka kaina gaban yarinya k'arama" yana magana ne shi kad'ai tare da neman hanyan fita.

Ta gefen ido yake kallon yaran da suke ta buduri da taliyarsu bakin nan duk mai yasa kai ya fice.

Yana fita teburin mai shayi ya tafi kaman yanda ya saba ya bayar da naira d'ari yace a bashi shayi empty na naira ashirin da bredi na hamsin,ana bashi canji akwai mai kosai a gefen mai shayin itama ya sayi na talatin a wajan ta ya samu waje a rumfar mai shayin ya fara karyawa.

A da in yana cin wannan had'in ji yake kaman mai cin kaza amma yau sai yaji babu taste sam sai tuno taliyan nan daya sha mai da kifin gongoni yake,kaman dole haka ya rinka cuccusawa har ya gama ya tashi ba dan dad'i ba.

A gida kuwa muna gama karyawa da Inna ta tace mu shirya ta kaini makaranta kada wani abu yazo ya fad'awa kud'in,

Muna gama shiryawa muka kama hanyan ainihin makarantan mu na da wato *YERWA PRACTICE* akwai jss a ciki daga 1 zuwa 3, cikin ikon Allah komai yazo mana da sauki ba kaman yanda Inna ta zata ba domin kud'in registration da kud'in PTA duka dubu biyu suka karb'a,daga nan uniform,takalmi,jaka,takardu duk kyauta aka bani kuma principal yace gobe in fara zuwa domin har an fara karatu.

Cike da farinciki muka kama hanyan gida, a hanya sai da mukayi 'yan cefanen mu da kud'in hannun mu sai dubu uku ya rage muka dawo da kaya niki-niki a hannu.

Gwaggo Aisha tana yiwa Hajara fad'a a tsakar gida kasancewar Inna Asabe ma ta fita,tana ganin mu tayi shiru sai rarraba ido take alaman basu da gaskiya,mu dai bamu bi ta kan su ba muka wuce d'aki suka bi ledojin hannun mu da kallo.

Muryan Gwaggo Aisha ya cika gidan tana yiwa Hajara masifan me take bata fito ta tafi tallah ba gashi har azahar tayi,na fito da buta a hannu na dan zagawa makewayi muka had'a ido da Gwaggo Aisha ta gallah min wata muguwar harara,niko dan in cusa mata bakinciki sai nayi mata dariya dama in ina son kullar da ita haka nake yi.

Ai kuwa ta hau yanda ya kamata ta hau zagina harda Inna ta da bata san wainar da ake toyawa ba,ni kuwa ko a jikina na shige bayan gidan na kama ruwa na fito tsakar gidan na fara alwala ita kuma bata fasa zagin nawa ba,dana lura bata da niyyan dainawa nayi mata gwalo amma sai na fake da cewa Jameela da take kusa da ita tayi min nima na rama.

Ban gama wanke d'ayan kafa na ba naga ta rarumo murfin tukunya da yake kusa da ita ta jefi ni dashi, Allah ya taimake ni kamin ya karaso na gauce nayi d'akin mu da gudu ina dariya.

Had'iye dariyan nawa nayi ganin fuskar Inna ta babu alaman wasa ta ce," wai ke wace irin yarinya ce Zareefa,ban hana ki kula su ba ko akwai sa'ar ki a ciki,bayan haka duk matan Baban kine saboda babu abokin wasan ki a cikin su tsakanin ki dasu shine girmamawa".

Jiki a sanyaye na ce ," kiyi hakuri Inna ba zan sake ba dama ni bada ita nake ba nida Jameela ne"

"Naji ki kiyaye bana son neman magana" ban kara cewa komai ba na fara sallah na a zuciya ta kuwa banga zan kyale ta ba in ta min wannan shegen kallon tunda ba wani laifi nayi mata ba.

Da yamma Inna ta fito tayi tuwan ta na shinkafa da miyan yakuwa da yaji biscuit bone da wadacaccen gyad'an miya, jin yauma kamshi ya cika gidan yara suka fara tsallen murna suna," yauma Innar Zareefa zatayi mana kayan dad'i" iyayen su na hantaran su amma basu fasa ba.

Yauma d'aki nabi su da abincin ba wanda ya kalle ni balle inji sun ce basa cin abincin da aka same ta ta haramtaccen hanya.

Da wuri yau Baban mu ya dawo gida tare da tsammanin an girka kayan dad'i irin na d'azu,yana saka kafa a gidan kamshin abincin ya mishi maraba wanda sai da ya had'iye yawu yana bin tsakar gidan da kallo,yaji tsit kaman babu kowa a gidan saboda kowacce tana d'aki da yaran ta suna kwasan gara.

Da gangan ya d'aga murya wai dan Inna taji ta aiko mishi nashi ya hau fad'an an watsar da kaya a hanya amma aka rasa wanda zai kula shi.

Yana nan tsaye yanayi Ibrahim d'an gidan Inna Asabe ya fito da kwanukan da suka ci abinci yana kokuwa da kashi tare da tand'e yatsu.

"Kai zo nan,zo ka kwashe kayan nan" ya yafito Ibrahim da hannu yazo yasa hannu ya kwashi kwanuka guda biyu da suke gefe har ya juya zai tafi ya rike shi murya kasa-kssa ya ce," kai yauma Bintun ce tayi girkin" gyad'a mishi kai Kai yayi dan santin kashin ya hana shi magana.

Maida hankalin shi yayi kan d'akin mu da muka sauke d'an yalolon labulen mu, juyawa yayi ya shiga d'akin shi ya zauna jiran ko yauma za'a kawo mishi.

Ya kai kusan rabin awa zaune yana kallon k'ofa amma ko motsin mutum bai jiba balle yaga mutum,tsaki yaja a karo na ba adadi ya mike ya fito tsakar gida tare da kama hanyan waje,bukutin roba na Maman Dije da yake ajiye a gefe akai ya sauke haushin sa sannan ya fita,ji kake kararass ya fashe sakamakon harbi daya kaiwa bucket din da k'afa.

Fita yayi yana ta zage-zage shi kad'ai dole ne yasan yanda zaiyi ya shawo kan Inna ta kamin girkin ta ya zagayo.

Da washe gari ba girkin Inna ta bane d'an haka indomine ta girka min na karya dashi ta bani talatin kud'in tara na fita makaranta cikin tsantsan farinciki domin haka naga sauran yara ake musu nima yau anyi min.

Sosai a ranan na mayar da hankali na nayi karatu tsabani da,karfe d'aya dai-dai aka tashe mu na kama hanyan gida.

Tun daga zaure na fara jin muryan Gwaggo Aisha tana zagina tare da aibata ni ga dukkan alamu kuma Baban mu take fad'awa,a jikin bango na makure naki karasowa sanin halin Baban mu ya kware a rankwashi.

"Munafuka daina kallo na da shegun idanunki kaman na mujiya" cewar Gwaggo Aisha tare da aika min mugun kallo.

"Ke Aisha ba kya kula da lokacin daya kamata ki tari mutum da magana,ni yanzu a gajiye na shigo hutu nake nema" yana gama fad'a kuwa yayi hanyan d'akin shi ya shige ya bar Gwaggo Aisha baki bud'e.

Kuyi manage ba yawa

*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 500 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu'a Idan Mutum Ya ga wani abu mai ban Mamaki, ko na farin ciki*

سُبْحَانَ اللهِ!
Subhanal-lah!.

Tsarki ya tabbata ga Allah.

اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar

Allah ne mafi girma.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*6*

Yanda Gwaggo Aisha ta bud'e baki ta kasa rufewa saboda mamaki kowa a wajan sai da ya wangale baki muka bi Baba da kallo har ya shige d'akin shi abin sa ko waigowa baiyi ba.

Wata wawiyar Ajiyar zuciya na sauke na samun tsira daga rankawshin Baba, kasancewar a tarihin rayuwa ta yau shine karo na farko da Gwaggo Aisha ta kawo kara ta yaki fad'a ko kuma duka na dan haka cikin jin dad'i fuska ta d'auke da murmushi na wuce d'akin mu.

"Ni kikewa dariya dan uban ki,toh ba dani kike ba da lusarar uwar ki kike " cewar Gwaggo Aisha cikin matukar fushi.

"Ni wallahi Inna banyi mata magana" na fad'awa Inna cikin marairaicewa saboda ganin irin kallon da take bi na dashi.

Kwafa kawai tayi ta cigaba da d'inkin hular ta da take,cire uniform na nayi na saka kayana na gida har mukayi sallah Gwaggo Aisha nata bala'in ta babu wanda ya kula ta sai can Inna Asabe ta saka baki.

"Kema dai Aisha akwai ki da son surutu,kullum Mallam yana biye miki ya zane 'yar nan amma dan yau kad'ai ya fad'i haka kika tashi hankalin ki,ya kamata ki mishi uzuri ki...."

"Eh lallai Asabe kike kowa kin samu kaina har ni kika kalla kike cewa ina son surutu saboda wuyan ki yayi k'wari, ba surutu nayi ba uban surutu nayi sai inji bugu ga uwa ta nan" tana yi tana kara matsowa kusa da Inna Asabe wai tana jiran taji bugu.

"Hmmm Allah ya tsari gatari da saran shuka kema kin san inda kika baro ta bani ba" cewar Inna Asabe tana kawar da kai gefe.

Wannan kalaman sun fi k'ona mata rai akan na farkon nan da nan taci d'amara da d'an kwallin kanta suka fara zagin juna,har baka jin me suke cewa tsabar ihun da suke.
Chapter 7 · 0% Book details