← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani maka da Gwaggo ta kai min a gadon baya ban san lokacin da na saki roban na gatsare tare da fasa ihun azaba ba, wuyan matattacen uniform d'ina ta kama ta jani zuwa ciki tana" lalle na yarda wannan 'ya ta gado mugunta, hasada da tsiya yo banda tsiya yanda kuke ke da uwar ki baku da allura a cikin d'akin shine ta koya miki yanda zaki na yi min barna kina jawo min asara??

Ke Bintu koki fito wallahi kabo na ba zaiyi ciwon kai ba duk inda zaki shiga ki fita sai kin bani kudina yanzu kuma wallahi ba sai anjima ba, ki fito na ce ".

Kallon yanda wuyan uniform d'ina yake kara yagewa yasa nace" Gwaggo ki sake min uniform d'ina kinga kina kara......" Ban samu karasawa ba sakamakon buge min baki da tayi tana huci tace" inifon din banza inifon din wofi ke iskanci uwar taki take koya miki ko boko shegiya yarinya duk wani gantali kin iya wai an likawa boko da baida baki"

"Ni ai abin nasu dariya yake sakani haka masu bokon suke ko akan su aka fara oho, dubi kiga ko takarda d'aya bata dashi balle fensir,ko da uwar me take rubutun?" Cewar Inna Asabe.

Inna ta duk tana jinsu amma ko lekowa bata yi ba balle ta tanka musu, hayaniya sosai ya kaure a gidan mu harda mokota masu zugi sai yi suke harda masu cewa a gaban su ma abin ya faru, dole yasa Inna ta fitowa daga d'aki jin abin yaki ci yaki cinyewa.

"Yauwa daddawa uwar zaman d'aki dole ai yau ki fito azo a biyani kud'ina naira dubu daya da dari biyu ciff wallahi ko biyar d'ina ba zaiyi ciwo ba".

Dariya suka fara suna " keko Aisha ina wannan taga har dubu da dari biyu sai dai in 'yar zata sai da ta biya ki" ko kuma kije wajan tsohon soja" wani tsohon soja sai dai ayi sata" ire-iren kalamai da suke jifan Inna ta dashi kenan.

Kaman yanda ta saba bata kula kowa ba ta koma cikin d'akin ta sai gata ta fito da dubu d'aya da dari biyu ciff da Gwaggo Aisha ta ambata ta mika mata babu kunya ta sake min riga ta karb'e kudin tana lissafi tana mamakin ina Inna ta ta samu wannan kud'i ita da burin ta yau sai ta wulakan tamu yanda taga dama amma cikin ikon Allah ta biya.

Duk watsewa suka yi cike da mamaki wasu ko cewa suke dama bar raina mutum baka san sirrin sa ba.

Ana cika min rigata na shigo d'aki ina kallon wuyan rigata na ce, "Inna dubi fa yanda ta maida min wuyan rigata gobe ya zanyi in tafi makaranta?"

Inna da ta had'a rai sosai ta ce, "ba wuyan riga ya kamata kiyiwa kuka ba, gobe kika ce za'a rufe karb'an kud'in common entrance ko?"

Gyad'a mata kai nayi ina cire kayana.

"Toh kud'in da nayi wata 3 da wani abu ina tara miki na common entrance d'in su na bada a maimakon abincin mutane da kika zubda, gobe ma in kin taso daga makaranta kada ki rinka kula da gaban ki".

Yawan comments yawan typing.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```

*_And now_*

*_💃🏻UWANI💃🏻

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu'a Ga Wanda ka zage shi:*

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce;

اَللَّهُمَّ فَأَيـما مُؤْمِنٍ سَبَبْتُهُ فَاجْعَلْ ذَلِكَ لَهُ قُرْبَةً إِلَيْكَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ.

Allahumma fa'ayyuma mu'minin sababtuhu, faj'al zalika lahu kurbatan ilayka yawmal qiyamati.

Ya Allah! Duk wnai mumini da na zage shi, to ka sanya wannan ya zamanto sababi gare shi na samun kusanci zuwa gare Ka ranar kiyama.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*2*

Kasa cire rigan nayi na zaro ido waje ina kallon Innara na ce," Inna kud'in common entrance d'in kika basu?"

"Ya kike son inyi? Kin san halin Aisha sarai a gidan in ta fara fitina zata kai awa goma tana yi ba tare da ta gaji ba,ni kuwa kin san ba iyawa zanyi ba gwara in bata a rabu lafiya gobe ma idan zaki shigo gida kada ki natsu " Inna kenan ta bani amsa.

Zama nayi da rigan a wuyan na ina hawaye na ce," shikenan za'ayi banda ni kenan,ko yau ina kallo akayi ta rabon abubuwa a makaranta ni ban samu komai ba akan 200 balle 1500 nasan gobe ko class ba za'a barni in shiga ba".

"Haka Allah ya kaddara ba zaki rubuta ba a wannan shekaran amma kiyi hakuri zuwa shekara mai zuwa ko kuma muyi addu'an Allah ya kawo wata hanyan,kinji ko?" Inna ta fad'a min cikin rarrashi.

Goge hawayen fuskan ta nayi na tashi na cigaba da cire uniform d'in na ba tare da na kara cewa komai ba.

"Ki d'auki hamsin cikin d'ari ukun daya rage kije ki sayi wani abin kici" cewar Inna.

Dariya na fara kyakyalewa da shi harda rike ciki sai da nayi mai isa ta sannan na ce," ai inna ciki na kaman zai fashe saboda koshi, dan lokacin da Hajara tayi b'ari almajirai suka fara wawaso nima roba 2 na wawashe na cinye tas abina Gwaggo Aisha data ji haushi kinji yanda ta zuba min dundu a baya Wallahi ko jin zafi ma banyi ba".

Cikin tsuke fuska Inna ta ce," wai ya akayi kika yi musu b'ari? Kullum inayi miki fad'an ki natsu amma ba kya ji ko?"

Daina dariyan nayi sannan nayi kalan tausayi na fara bata labarin abinda ya faru a makaranta har zuwa yanda mukayi karo da Hajara,ajiyar zuciya Inna ta sauke tana mai jin tausayin na ta ce," hakuri zakiyi Zareefa insha Allah wata rana sai labari,karatu kuma da yardan Allah zakiyi shi".

Gyad'a kai kawai nayi na fita yin alwala zahar a lokacin duk yaran gidan anyi musu abin sana'a duk sun fita talla,ina idar da sallah na fara shirin islamiya shi kam cikin dokin zuwa nake shirin na kasancewar a can bana takura kaman boko.

Akwai wani Malamin mu da yake d'aukar mu Qur'an shi ya tsaya minsosai sabo kokarin na dan har kudin wata 500 shi yake biya min domin kullum dai-dai nake kawo hadda ta yanzu haka mun bawa izufi 30 baya.

Ina gama shirin na nayiwa Innata sallama na tafi.

Ina fita Inna ta kwaso uniform dana cire ta hau wanke min da sauran Omo da ta rage jiya,tanayi tana jin su suna ta haice-habaicen su ta gama ta shige d'aki ta rabu dasu.

Mun taso a islamiya ni da kawayen na muka nufi gida muna d'an wasan su na yara,muna zuwa dai-dai gidan mu na fara jin muryan Baban mu yana ta masifa kaman zai ari baki.

Dariya sauran yaran suka fara har suna lekowa ta rububben ginin daya zagaye gidan.

Jiki a sanyaye na nufi cikin gidan namu dan nasan yanda Baba yake d'aga muryan nan nasan da inna ta yake,muryan Gwaggo Aisha naji tana kara zuga Baba da fad'in karya da gaskiya.

"Toh ai Mallam dan ma baka ga irin rashin kunyan da yarinyan nan tayi min a waje ba,inda zaka san da gayya ta b'arar da kayan sana'a shine,itace farkon daka wawa sannan sauran almajirai suka bi bayanta.

Koda yake b'ata baki na nake ina gaya maka abinda ya faru na san babu wani hukuncin da zaka d'auka tunda 'yar amayar ka ce abin sonka".

A fusace Baba ya juyo kanta yana," wannan wani irin maganan banza kike min matar da *Ba sonta nake ba* aka lika min ita dole yasa na karb'a dan kar inyi asaran kud'i na,amma wallahi Aisha kin cuce ni"..

Gwaggo Aisha ta saki shewa dama Kalmar da take son ji kenan.

Baba ya cigaba da fad'an shi inda yake cewa," duk kin bi kin b'ata yarinya bata ganin kowa da darajan a gidan nan da anyi magana kice wai boko take sai kace ki d'in bokon kikayi aikin banza kawai zata zo ta same ni a gidan sai jikin ta ya gaya mata"

Yana juyowa muka had'a ido ina can makure karshen bango ,aiko baiyi wata-wata ba ya nufo ni zai sake min wannan rankwashin sa nan da sai yasa kullum na saki fitsari a wando.

A guje nayi d'akin mu na shige kamin ya kama ni sanin cewa in ba wani babban dalili ba baya shigowa,cikin sa'a kuwa bai shigon ba ya tsaya a tsakar gida yana cigaba da fad'an,sam na daina jin me yake cewa domin ganin Inna ta na kuka abinda ban tab'a gani ba kenan tun tasowa ta dan komai akayi mata a gidan ko Baban mu ko matan gidan sai dai tayi murmushin mai ciwo tace akwai Allah.

Toh tana furta wannan kalman duk yanda za'ayi da ita ba zata kuma tankawa ba na sha tambayan ta me yasa itama ba zata ke rama cin fuska da ake mata ba sai dai tayi wannan murmushin nata mai ciwo ta ce," bakomai Zareefa akwai Allah" daga nan kuma ba zata kara cewa komai ba.

Zuwa nayi har gaban ta na durkusa a gaban ta tare da d'aura hannu na kan guiwoyin ta na ce," Inna kuka kike,meya same ki?" Duk na jero mata wayan nan tambayoyi a lokaci guda.

Murmushin nan nata mai ciwo tayi min kana ta ce," babu komai ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga ido na".
Chapter 2 · 0% Book details