← Book details Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 71

Sashe 36

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadeeq shiya taya shi shiryawa sunayi suna fad'a shi dai Sadeeq dariya yake ta mishi ganin yanda yake turo baki kaman wani karamin karamin yaro mai shagwab'a.

Farar dok ce mai matukar tsada yasa mai d'aukan ido yasha aikin hannu wato (gatau) hula takalmi duk farare ne wrist watch na hannun shi shima na pure diamond ne sai kamshi na musamman yake kana ganin shi kaga haddaen ango, suna gamawa suka fito parlour inda abokan sa suke jiran sa.

Yana fitowa ihu suka fara suna mishi kirari saura na tsokanan shi dan sake fuska yayi ya dan biye musu suka tab'a wasa sannan suka raka shi wajan Mom.

Tsakar gidan babu mutane sosai dan haka basu sha wahalan karasawa cikin ba , parlour Mom a cike yake ana ta hidima suna ganin shi wata mai murya ta saki wani irin gud'a da ya cika gidan nan da nan sukayi kan shi ana ta wasa da dariya da kyar ya samu ya karasa sama d'akin Mom, tana zaune cikin kawayen ta da 'yan uwan ta suna hira.

Ido ta zuba mishi har ya karaso ciki zuciyar ta kuwa kaman farar takarda yau Allah ya nuna mata auren tilon d'an ta.

Albarka suka yi ta saka mishi bayan ya suguna har kasa ya gaida su, Mom harda hawayen farinciki dan yau babbar rana ce mai babban tarihi a rayuwata.

Kiran da Abba yayi mishi ne yasa shi mikewa ya fita ya tarar da tawagar Abba har sun fara tafiya, ba b'ata lokaci shima ya shiga cikin abokan sa suka kama hanya.

Akwai wani babban masallacin juma'a a bakin layin mu kuma a nan ne za'a d'aura auren, so duk a can wajan layin sukayi parking wasu ma ko wajan parking din basu samu ba saboda yawan motocin dan haka wasu suka fara shigowa cikin layin namu Dan samun wajan parking.

Masallacin kan shi ma har yayiwa mutane kad'an wasu basu samu shiga ba ko ina ka duba taron al'umma ne, in wanda bai sani ba yazo yaga taron zai zata auren 'yar babban mai kud'i ake ba ko dan siyasa ba 'yar Mallam Hassan ba.

Baba yau in ka ganshi kaman yayi hauka saboda farinciki harda su governor a daurin auren 'yar shi harda manyan kusoshi na gomnati ,ba'a tsaya b'ata lokaci ba aka daura aure na da Zafar kan sadaki naira million 2.

Muryan maroki da ya fara shelan d'aurin auren har cikin gudan mu a lokacin ina tsakar gida cikin mutane dan Inna ta saka ni fitowa waje gaida 'yan uwan Baban mu, a take wajen ya kacame masu farinciki suka fara masu bakinciki ma nayi, ni kuwa ji nayi kaman an saka ni a cikin kankara haka naji jiki na yayi wani bala'in sanyi tare da zazzab'i mai zafin gaske ba shiri na nufi bangaren mu kamin na karasa d'aki na har na fara rawan sanyi ina shiga na kwanta na lullub'a da bargo ina hawaye a haka Aunty Batool tazo ta same ni cikin rarrashi tayi min nasiyan yadda da kaddara sannan ta bani magani na sha bata bar d'akin ba sai da taga bacci mai nauyi ya d'auke ni sannan taja min kofa ta fita.

Anan d'aura aure su Abban Zafar gaba daya suka wuce reception da Abba ya had'a a nan cikin gidan shi, su Zafar ma bayan shi suka bi duk yanda Sadeeq yayi dashi akan su tsaya ya d'anyi pics tare dani saboda tarihi yaki ya shiga mota suma suka rufa mishi baya.

Sai yamma naji d'an karfin jiki na aka kara canza min kwalliya zuwa walima cikin abaya da Inna ta siya min saboda walimar ba'a dad'e da farwa ba yan gidan su Zafar suka kawo lefe na da ya kusan haukata mutanen gidan mu dana anguwan baki d'aya, nima a yanda naji Maryam tana lissafowa ban tab'a jin labarin irin su ba.

Bayan an gama cece-kucen ganin lefen suma suka shiga cikin mu akayi walimar dasu inda Mallama Falmata Zanna ta wa'azantar kan biyayyan aure ko Inna ce tace tayi hakan oho, sai kusan magariba taro ya watse bayan anyi rabon manyan jakkuna masu d'auke da Al'quran ma daidaici sai sallaya da hijabi,nayi mamakin yaushe Inna ta shirya haka ko dan ban maida hankali ga bikin bane ban sani ba.

Basu bar ni nayi alwalan magriba sai da nayi wanka da ruwan turare sannan nayi alwala na fito nayi sallah ina kuka ganin cewa dai da gaske suke dan sai shirye-shiryen kai ni suke shirya ni sukayi cikin atampa super mai ratstsin silver a jiki , d'an kunne da sarka da suka saka min suma duk silver ne sannan suka nad'a min laffaya mai masifan kyau shima silver color aka fito dani wajan su Inna da yan uwan ta.

Nasiha suka fara min kan hakuri d'aya bayan d'aya Inna ta dai tana gefe tana kallon yanda nake kuka kaman raina ya fita, Maa ce ta katse ta tace itama tace wani abu mana.

Murmushi mai ciwo tayi muryar ta na rawa tace" me zancen Maa da ku baku fad'a ba, ni sai dai inyi mata addu'a Allah yaa...." Kukan da take rikewa ne ya kwace mata ta tashi cikin sauri tayi d'akin ta, kara kuka na nayi na mike zan bita suka rike ni ina musu magiya da roko amma basu saurare ni suka sada ni da d'akin Abba yana zaune shi kad'ai sai washe baki yake.

"Sai ku fita ku d'an bamu guri ni da 'yata ko" yace musu bayan sun zaunar dani a tsakiyar parlour shi, Aunty Batool har ta tsaya da nufin gasa mishi magana Aunty Fatima ta mata alama da ido da tayi shiru kawai su fita, ba dan ta so ba suka fita tana mitan wai dama ya san ni 'yar sace?

Suna fita ya juyo gaba daya gare ni yana kara washe baki yace " ke kuma in banda kuruciya menene abin kuka anan, Allah ya azurta ki da samun irin wannan mijin da babu kamar sa duk maiduguri yaushe kuka hadu dashi amma ga yanda ya sauya mana rayuwa baki d'ayan mu,

Wannan ai abin alfahari ne a gare mu ba ki saki baki kina kuka ba d'aurin auren ki har da gomna fa suka zo" ya karasa feeling very proud Yana gyara Zama.

"Abinda nake so dake shine kada kice zaki manta da gida dan kin samu daula ya kamata ki san yanda zaki rinka tatso wasu abubuwa daga gare shi kina aiko mana ai kin gane abinda nake nufi" ya karasa tare da zuba min ido gyad'a mishi kai nayi hawayen takaici na zubo min dan ni da yace su Aunty's dina su fita na zata zai min nasiya ko kuma ya rarrashe ni kan auren da ya d'aura min ashe shi tunanin shi daban, wai yaushe ne Baban mu zai canza?? Na jehowa kai na tambayan da babu mai bani amsa.

D'aga murya yayi ya kira su Aunty Fatima suka zo suka fita dani direct sai mota suka sakani suna ta zabga guda Aunty Fatima da Aunty Batool su suka sakani a tsakiya suna hirar su anan naji cewa wai Gwaggo Aisha da taji labarin taron d'aurin auren ta yanki jiki ta fad'i yanzu haka tana asbiti ba lafiya.

Har muka karasa gidan Zafar da ya amsa sunan shi gida ko ince Aljannar duniya dake can bolori lay out hawaye bai kara zubo min saboda mamakin halin Baban mu dana Gwaggo Aisha.

A maidaicin compound din gidan da fitilu da flowers suka ma ado drivern yayi parking ,Aunty Fatima dake zaune a gefe na dama ita ta fara fita sannan ta kama hannu na tace in fito da kafar dama, hakan kuwa nayi na fito kaina a kasa dan rabin fuskata a rufe yake tana rike da hannu na har entrance din parlour nan ma cewa tayi inyi Bismillah sannan in shiga da kafar dama.

Ni dai tafiya kawai nake ban san inda nake jefa kafa ta ba har naji mun shigo wani d'aki kuma naji an zaunar dani akan wani tattausan gado, sai a lokacin naji sabon kuka ya zo min na fara ina rike a jikin Aunty na, sauran yan rakiyan kuwa suka bazama duba gidan suna ta santi tare da yaba kayan d'aki da Inna ta min wanda ni ban san ma yaushe akayi su ba kasancewar naji Baba na cewa ba za'a min komai ba dan sun ce basa bukata komai daga gare mu.

Allah sarki Inna ta na san tayi hakan ne dan samo min martaba da Kuma daga gare su, bamu fi minti talatin da zuwa ba naga sun fara shirin tafiya dinner nima kara shirya ni sukayi cikin wani Indian material mai dan karan tsada da kyau, net suka saka min a tsakiyan kai suka kama da pin ana ganin kitson da aka min na gaba sai suka saka min sarkan kai wanda yazo min har goshi sarkan set ne da dan kunne da sarkan wuya da warwaro masu bada sauti mai dad'i.

Kamin su gama min duk sun tafi sai Maryam da wasu cousins dina 2 su suka tsaya Jira na da kuma Aunty Fatima har bakin wata arniyar mota da ko sunan ta ban sani ba suka rako ni tare da bud'e min kofa na shiga, ina jira inga ta shigo kaman dazu sai naga ta mayar da kofan ta rufe suka nufi wasu motoci guda 2 daya a gaban mu yake daya kuma a baya ya kasance sun saka mu a tsakiya.

Har motan ya fara tafiya naji motsi a gefe na a firgice na juya dan a zato na Ni kad'ai ce a cikin motan sai ganin mutum nayi a kishind'e kaman wani basarake yana latsa waya ko kallon inda nake baiyi ba, ni kuwa kasa d'auke ido nayi a kansa ganin sa cikin arniyar suit ko dan ban tab'a ganin ya saka bane sai naga ya masifan yi mishi kyau,

"Bana son kauyanci ki daina kallo na da wayan nan idanun naki" naji muryan shi ya katse ni.
Chapter 36 · 0% Book details