← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 47

Sashe 9

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ta dawo daga makaranta ta tarar da matan gidan cirko-cirko Umma tana tijara akan su fito mata barawo da ya shigar mata daki yayi mata sata. Ji tayi kamar kasa ta tsage ta nutse a ciki, tace, "Umma miye aka sata?" Umma tana maida lumfashi tace, "Leather da muka ajiye a karkashin gado." Tace, "Umma kin manta kin ce in mayar mashi dasu, jiya na mayar mashi." Sabuwar fitina ce ta tashi jin inda leather ta tafi, su salme suna bala'i akan sata da Umma ta laka masu. Umma tayi mursisi da idanu tana nade tabarmar kunya da hauka, "Halinku na sani na sata shiyasa na fad'a, cokali wannan idan mutum yayi wanke-wanke ya manta kafin ya fito an samu wata marar tsoron Allah tayi ciki dashi. Mutum yayi k'arya ya kirani da barauniya saidai ace min fitinanna kuma fitinata sai an janyoni nikeyi, aikin banza aikin wofi." Ji Hafsat tayi ba zata iya zama ba ta juya ta koma gidansu Jalila, Jalila tayi mamakin ganinta la'akari da basu dade da rabuwa ba amma bata tambaya ganin yanayinta. Ta zubo mashi abincin sanin yunwa da suka debo throughout fitarsu gurasa kawai suka ci a student center.

A gidansu fitina aka yi sosai, Salme tace sai takai Umma k'ara anbi mata hakkinta, Umma tace, "Da kuwa anyi tone-tone akan sace-sace da kikayi min wanda ina sane na kyaleki ne kawai domin idan kafi karfin abu kawar da idanu kakeyi." Salame ta shige daki fuu a cewarta zata dauko mayafi daga nan babu wanda ya k'ara jin motsinta.

Saida dare ta koma gida, Umma ta dubeta da tuhuma tace, "Hafsat mi ya faru? Ban ce maki ki mayar da sauran." Hafsat ta sauya maganar ta hanyar cewa, "Umma ina abincina idan tuwo ne ba zan ci ba." Umma ta dauko warmer ta ajiye a gabanta tace, "Gashi nazo dashi daga gidan aikina." Zata janyo Umma ta rike hannunta ta murtuke fuska tace, "Tambayarki nike, mi ya faru kika mayar mashi dasu?" Ta rumtse idanu sannan tace, "Mun rabu, alakata da Al'ameen bazata yiyu ba shiyasa na mayar mashi da kayansa tareda kudin." Ta mike ta fita domin tayi alwallar barci, ta fito tsakar gida tana ganin matan gidan zaune suna gulma ta kawar da kai tana mamakinsu, sun ki sana'a sun zauna majalissar gulma. Tayi alwalla ta koma daki ta ajiye buta a bayan kofa, ta kwanta, Umma tace, "Abincin fa." Tace, "Naci abinci a gidansu Jalila." Umma tace, "Amma da kanki kika tambaya." Tace, "Ina k'ok'arin sauya hirar ne." Daga nan bata sake magana ba, tayi lamo kamar tana barci.

Umma tayi kwafa, cikin ranta tace, "Wannan yarinya kin cika taurin kai, Hafsat kenan, idan kin san wata baki san wata ba."

Washegari da safe ta shirya ta wuce school, sai karfe goma sha biyu na rana sannan ta dawo gida, tayi turus tayi tareda sakin jikkar dake hannunta a sanadin halin da taga Umma a ciki. Umma ce a cikin halin ciwo, tana kwance akan tabarma tana maida lumfarfashi yayinda k'awarta Nana take zaune a gefenta tana mata firfita da mafeci, da gudu ta k'arasa inda suke ta durkushe ta kamata tana kuka tace, "Umma mi ya sameki? Mi ya faru?" Umma tana maida lumfashi dakyar tace, "Hafsat karkiyi kuka, In sha Allahu zan tashi, ba zan mutu ba, ki kwantar da hankalinki."

Hafsat tana mai fashewa da kuka tace, "Aunty Nana mi yake damunta?"

Nana tace, "Likita dai yace ta sakawa kanta damuwa ne har ciwon zuciya yana barazanar kamata."

Ta ware idanu tana mai cigaba da hawaye tace, "Umma miye damuwarki? Please ki fad'a min. Mi yake saka maki damuwa har kika shiga wannan halin na ciwo? Ki fad'a min abun da zan yi maki?"

Umma ta kama hannunta tana maida lumfashi tace, "Hafsat damuwa da ya wuce burina na ganin aurenki, bana fatan na mutu na barki ba tareda aure ba, zan mutu ne a salama idan nasan da kina da miji wanda zai kula dake, bana son mutuwata ya zama sanadi na tagayyara rayuwarki, dangin mahaifinta babu na kirki, dangina ba zasu amsheki ba, kaicona da na janyo maki wannan rayuwa mai cike da kalubale." Hafsat tana sheshshekar kuka tace, "Umma In sha Allah, zakiga aurena." Umma da muryarta dake fita dakyar tace, "Allah yasa." Hafsat tace, "Ameen."

Wuni tayi tana nanike da Umma, da marece Jalila tazo ganinta tareda Mamarta, Hafsat ta damu sosai akan rashin lafiyar Umma, ta rasa abun da yake mata dadi.

Da daddare ta kasa bacci ganin yadda Umma take jin jiki, tace, "Umma ko komawa asibitin zamuyi?"

Umma ta girgiza kai tace, "A'a sun bani magani kuma nasha."

Hafsat tayi tagumi tana tunanin yadda zatayi da rayuwa a lokacin da aka ce Umma bata a doron kasa, ita kadai gareta, ita kadai ta sani, bata san danginta ba, dangin mahaifinta kuma dasu da babu duk daya ne, bata rumtsa ba har asuba, yadda taga rana haka taga dare, sai bayan da tayi sallar asuba sannan ta samu bacci yayi awon gaba da ita.

Karfe tara na safe ta farka, da sauri ta kalli inda Umma take domin gani take kamar zata rasata, Umma da muryarta wacce bata fita sosai tace, "Hafsat."

Hafsat ta janyo hannunta ta rike tana mai zubar da hawaye tace, "Umma. Kina buk'atar wani abu?" Umma ta girgiza kai, Hafsat tace, "Umma ya jiki?" Umma ta d'aga kai tace, "Da sauki." Tace, "Allah ya k'ara sauki." Yace, "Amin."

Kira ne ya shigo wayar Hafsat ta kalli sunan wanda ya kira sannan ta amsa, tayi jim sannan tace, "Kuma yau? Dole ne ko yau. Okay, na gane." Ta zare wayar daga kunnanta, Umma ta dubeta, Hafsat tace, "Daga makaranta ne ana son ganina yau kuma gashi baki da lafiya, ban san in fita in barki a wannan halin."

Umma tayi murmushin karfin hali tace,
"Ki shirya ki tafi, Nana zata zo ta zauna a tare dani."

Hafsat tayi jim, Umma tace, "Ki tashi ki tashi, karatun nan da kike burina ne."

Ba don ranta yaso ba ta gyad'a kai, "Okay. Umma Allah ya k'ara sauki amma please idan kinji ciwon ya k'aru ki kirani in dawo muje asibiti." Umma ta gyad'a kai.

Hafsat ba don ranta yaso ba tayi shiri, ta tsakuri abinci kadan, ji take kwata-kwata babu dandano a bakinta a sanadin damuwar da take a ciki akan rashin lafiyar Umma, tana tafiya tana waigowa har ta fita, wuni tayi a school, tana a makarantar ne amma hankalinta yana gida ta damu akan halin da Umma take ciki, kallo daya za'a mata a fahimci tana cikin damuwa, tun kalaci da tayi bata k'ara cin wani abu ba har karfe biyar da ta baro makaranta, lokacin da ta koma gida ta tarar da tashin hankali, jikin Umma ya k'ara tsanani, kwana tayi tana kuka saboda halin da Umma take ciki na tsananin ciwo.

Washegari wuni tayi tare da Umma tana kula da ita. Tace, "Umma ki tashi muje asibiti." Umma tace, "Zamuje tareda Nana." Hafsat tace, "Amma mi yasa ba zakije dani ba?"

Umma ta dubeta tace, "Saboda zakije makaranta." Hafsat ta girgiza kai, "A'a, ba sai naje ba, lafiyarki ta fiye min komai." Umma ta girgiza kai tace, "Gobe ki shirya kije makaranta, zamuje asibitin tareda Nana."

Washegari, saida ta tabbata tayi wa Umma komai sannan ta wuce school yanayinta cike da damuwa ganin har lokacin Umma tana jin jiki sosai, two hours lecture tayi attending ta dauki drop aka kawota har kofar gida, ta mik'a mashi kudinsa sannan ta fito ta shige, tana tunkarar kofar dakinsu ta jiyo muryar Umma tana waya tana dariya tana shewa tana cewa, "Na kad'ata ta tafi makaranta. Ta cika taurin kai shiyasa nayi mata haka, ta amsa min ne kawai akan zata auri mai kudin amma idan nayi mata saku-saku sai inji wani zancen, kinga da nayi wannan ciwon na karya, duk taurin kanta ba zata bijirewa maganata ba, kina nan zakiga ta gabatar da wani. Tana zuwa zan marairace mata akan ta nemo kada na mutu ban ga aurenta ba."

Hafsat ta ja da baya tana mai girgiza kai yayinda hawaye suke zubowa daga idanunta, ta d'aga labulen dake dakin ta kutsa kai.

Umma ta zaro idanu tana kallonta, Hafsat tana hawaye tace, "Umma mi yasa kikayi min haka? Jina nike kamar wacce aka koda yake bamu amfanin fad'a. Umma did you have to get this far. Nace maki zan bi zab'inki koda zuciyata bata so. Nace maki zan auri mai kudi kamar yadda kike so. Umma na sani dukkanin abubuwan da kikeyi kina yi ne saboda kina son rayuwata ta inganta, saboda baki son in shiga kwatankwacin halin da kika tsinci kanki a ciki. Amma tambayar a nan itace shin na shirya auren mai kudi? Shin na shirya rayuwa a dangin masu kudi? Shin zasu karbeni hannu biyu ko kuma zan ci karo da kalubale na gori irin wanda Umar yayi min, shi zancen duniya ba ya b'uya." Ta lumfasa tana sheshshekar kuka tace, "Umma an gaya min magana ance min kina da son abun duniya, ance maki mai idon cin naira amma na jure saboda nasan ba haka kike ba. Umma mi yasa zakiyi haka? Koda yake babu komai, ba sai kinyi haka ba, yadda kike so hakanan za'ayi. Umma mun gama wannan maganar a nan, kada a sake tadota, shikenan, magana ta k'are. Ba sai kin nemeni ba ina gidansu Jalila." Ta hade hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Umma na rokeki da girman Allah idan na dawo kiyi kamar wannan abun bai faru ba." Juyawa tayi ta fita tsakar gida, saida ta wanke fuskarta sannan ta fita waje tana tafiya dogon hijabinta yana sharar kasa.

Kai tsaye ta wuce gidansu Jalila, ta kwanta, Jalila ta dubeta tace, "Angel kwana biyu naji baki maganar Al'ameen ba." Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Mun rabu. Ban Dace Dashi Ba koda yake shine bai dace dani ba. Kin tuna kwanaki na fad'a maki ina ji kamar ana bibiyata." Jalila ta gyad'a kai tace, "Hakane." Hafsat ta mike daga kwanciyar da take ta gyara zama sannan tace, "Tabbas akwai wanda yake bibiyata kuma yau zan kawo karshen komai. Ki jirani ina zuwa." Ta zura takalma ta fita daga dakin ta dauki hanyar kofar gida.
Chapter 9 · 0% Book details