← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 47

Sashe 27

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsat ta ajiye wayar tareda fashewa da kuka, tun daga ranar bai k'ara ganin fara'arta ba, cikin saka mata yunwa yake, ci kamar tsohuwar gara, zata tusashi gaba ya girka mata abinci, ta saka dole ya ciyar da ita tana ci tana bashi wahala tana cizon hannunsa, yadda cikin yake wahalar da ita itama haka take wahalar dashi, ta hanashi zaman lafiya.
Ta dage da karatun Alk'ur'ani da azkhar, bata sakaci dasu, hankalinta ya kwanta da daina mafarkai da gane-gane.

Cikin haka ne haushinsa ya rinjayeta har tayi sakaci da addu'a, asirin yayi tasiri a kanta, abu kamar wasa ta fara mafarakai masu ban tsoro, ita kadai sai ta rink'a zabura, tana rufe idanunta zata soma ganinsu, babu dama ta kwanta bacci, dare yana kawo jiki zata fara razana tana firgita, fatalwowi suna farmakarta.

Kira ta gani da bakuwar number, tana amsawa Aysha tace, "Shine kika saki jiki har kikayi ciki, kin janyo wa kanki, ko ya sakeki idan baki zubda wannan cikin ba bazan rabu dake."

Hafsat ta ajiye wayar tareda fashewa da kuka, ta kira Umma ta sanar da ita komai, Umma tayi jim sannan tace, "Hafsat kece baki damu da addu'a ba, ki rink'a karatun Alk'ur'ani da azkhar, ki rage kallo musamman da dare, ki rink'a alwalla idan zaki kwanta bacci."

Hafsat ta gyad'a kai tace, "InshaAllah." Tana rike da maganar amma dare yana kawo jiki ta manta ta kwanta ba tayi ba, ta farka tare da fasa ihu, Hisham ya shigo da saurinsa ya kamata yana tambayarta abun da ya faru, baki daya jikinta rawa yake ta kasa magana, tun daga wannan lokacin ne ta koma kwana a dakinsa, zata wuni tana tunawa da alwallar kwanciya bacci amma dare yana yi mantuwa zata zo masu baki daya, su kwanta basu yi ba, mafarkai take masu ban tsoro, fatalwowi suna kawo mata farmaki, ta rame, ta fita daga hayyacinta, ta koma zautacciyar karfi da yaji, Hisham saidai ya daina fita kullum yana zaune da ita a gida.

Ranar ya shiga bandaki yana fitowa ya nemeta ya rasa, tashin hankali k'aramar magana ta zama babba, anyi neman duniya babu Hafsat babu dalilinta, Umma babu abun da take sai kuka tana nadamar abubuwan da tayi na tilasta mata auren mai kudi, ga dukiyar amma babu kwanciyar hankali, kwadayinta ya saka ta jefa gudan jininta a bala'i da tashin hankali.

Hisham yana kaiwa da komowa yana cikin tashin hankali, Momcy ta tada sallah tana mai sanar da Allah halin da suke ciki, Fatima tana daga gefe tana kuka, Jalila tunda taji labari take kuka har zuwa wannan lokaci, wasa-wasa har washegari babu Hafsat babu labarinta.

Suna zaune jigum-jigum, kira ya shigo wayar Jalila, tana dubawa taga 'Jameel Borno' tana ganin hakan ta gane cikin wadanda suka tab'a mata ciniki ne online, kamar ba zata d'aga ba sai tayi picking tareda komawa gefe, daga daya bangaren yace, "Jalila. An wuni lafiya?" Jalila tace, "Lafiya lau."

Ji tayi yace, "Ina k'awarki wacce nike ganin kina yawan d'aura status da hotunanku tare, Angel." Da sauri tace, "Ehhh. Ina jinka." Yace, "Yanzu naga wata mai KAMANNI da ita saidai kamar bata a cikin hayyacinta."

Jalila ta fashe da kuka tace, "Itace, tun jiya ta b'ata muka nemeta muka rasa, na rokeka da girman Allah ka saka a kamata a kulle a daki kafin muzo, kada ta gudu mu rasata, wahala take sha sosai, ciki ne da ita. Mahaifiyarta damu suna cikin tashin hankali."

Daga daya bangaren Jameel yace, "Karki damu za'a kaita gidan mai unguwa, sai ku kamo hanya."

Da gudu ta koma inda suke ta sanar dasu kiran da ta samu. "Cikin wanda suke ciniki dake Borno yaga Hafsat, shine ya kirani, ya ganeta saboda ina yawan daura hotunanmu a tare."

Da mamaki Umma tace, "Borno!." Hisham yace, "Borno kuma!."

Momcy tace, "Ta ya taje Borno!."

Suna mamaki la'akari da nisan dake a tsakanin Katsina da Borno."

Ta nuna masu hotonta da ya tura mata wanda suka dauka a lokacin.

Hisham ya amshi wayar tabbas kayan da take sanye dasu ne.

Umma tace, "Alhamdulillahi."

A private Jet dinsa suka wuce Borno, Hisham, Umma, Momcy, Jalila da Fatima, aka saukesu a gidan mai unguwa, a lokacin an bata rubutu tasha har ta fara bacci, suka ci suka sha, Hisham yayi godiya sosai wa Jameel tareda mashi sha tara ta arziki, da marece suka juyo suka dawo Katsina, tunda suka shigo gidan take k'ok'arin gudu.

Umma ta fashe da kuka tana nadamar tursasata da tayi ta nemo mai kudi duk da Umar ba mijin aure bane amma da ta dage mata da addu'a suna zaune Allah zai kawo dalilin rabuwarsu, ya kawo mata miji na gari. "Hafsat na cuceki, son kudina ya janyo maki."

Hisham tausayinsu ya kamashi, yayi nadamar aurenta da yayi, ya jefata a cikin damuwa. "Hafsat nayi nadamar kawoki da nayi a cikin rayuwata, na jefaki a cikin tashin hankali, dukkanin abubuwan dake faruwa dake nine sanadi."

Suka kulleta a daki ta fasa glass dake a kofar balcony tana k'ok'arin haurawa, har ta jiwa kanta ciwo, a ranar ya kira aka mayar da window na dakin na rodi, suka kulleta.

A koda yaushe yana tare da ita, da kanshi yake mata girki yana bata, dole Umma ta dawo gidan da zama, suna kula da ita a tare, a kowace rana abun k'ara ta'azzara yake.

Umma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Hafsat zan nema maki magani, ke daya gareni bazan bari a illata min ke ba."

Dukkanin inda Umma taji labarin mai magani sai taje, lungu da sako, garuruwa har ta tsallaka Niger da sauran kasashen kusa, cikin yana k'ara girma, abun yana k'ara ta'azzara, ta zama mahaukaciya tuburan, cikin wahalar da ita yake sosai, mintina kadan zata ce yunwa, idan ba'a bata ba ta fara kuka, tana ci aka dade zata k'ara cewa yunwa, an sauya mata KAMANNI tayi kib'a kamar ba ita ba.

Umma ta rame, kullum itace akan hanyar nemar mata magani, Alhamdulillah ana samun cigaba, cikin yana da wata tara, sun dage mata da saukar Alk'ur'ani da addu'a, ciyar da mutane da sadaka. Umma ta dage da tsayuwar dare, karatun Alk'ur'ani mai girma.

Karfe sha biyu na dare ta fara ihu tana kururuwa, Hisham yana tsaye baki daya hankalinsa a tashe yake, da taimakon Umma ta santalo yaronta Namiji mai KAMANNI da ita sak kamar an tsaga k'ara an karya, Umma ta janyo rubutu ta bata, tana sha ta fara atishawa, bacci yayi awon gaba da ita, tana farkawa ta fara bin dakin da kallo fuskarta dauke da mamaki, tace, "Umma a ina nike? Mi ya faru dani?"

Umma ta fashe da kuka ta rungumeta, tana kuka tana fad'in, "Alhamdulillah. Allah shine abun godiya."

Hafsat tana kallonta da mamaki tace, "Umma mi ya sakaki kuka?" Umma tana mai cigaba da kuka tace, "Hafsat haihuwa kikayi."

Hafsat tace, "Haihuwa kuma? Yaushe cikin ya girma har na haifeshi ban sani ba?"

Umma tace, "Haukata min dake tayi, har guduwa kikayi kikaje Borno, a halin hauka da wahala kika raini cikin kika haihu. Na nemar maki magani a wajeje daban-daban, sai a wannan lokaci Allah yasa muka dace. Hafsat ki yafe min, nice na janyo maki." Umma ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita.

Hafsat ta goge hawayen da zubo mata na tausayin kanta, tace, "Ina yaron da na haifa?" Umma tace, "Yana a wajen Hisham."

Hisham ya shigo yana dauke da yaron, Umma ta mike ta fita, Hisham ya zauna a gefen gadon tareda mik'a mata shi, ta amsa tana kallon yaron wanda babu abun da ya baro a KAMMANI da ita, yayi shiru yana kallonta, tayi kamar bata san ya wanzu a wajen ba, ya gaji da zama ya mike ya fita.

Suna zaune a parlour, Fatima ta sauko kamar wacce aka jefo tace, "Aysha ta hauka ce. Ta gudu. Har yanzu babu wanda yasan inda take." Momcy tace, "Alhaki kyuwkuyo." Umma tace, "Allah ba azzalumin bawansa bane. Mugun abu jakada, idan yaje zai dawo ya sanar da kai zuwansa."

Hafsat dake fitowa daga kitchen akan kunnanta saidai bata ce komai ba, ta sauke ajiyar zuciya jin babu sauran barazana, ta wuce sama.

Baby yaci suna Muhammad, Hisham ya kashe naira, raguna biyar ya yanka mata tareda shanu guda biyu, bayan kaji da zabbi da aka yanka, ya kashe naira babu k'arya, a ranar suna ne Hafsat taga Iyayen Bilkisu saida suka bata tausayi, har zuwa wannan lokaci magana bata hadata da Hisham ba, idan yazo karbar yaro zata bashi, idan ya maido mata ta amsa.

Momcy tana lura dasu saidai bata ce dasu komai ba, Hafsat bata tada maganar ba har tayi arba'in, Hisham ya tarasu baki daya, Umma, Momcy, Hafsat da Babansu Jalila.
Hisham ya lumfasa sannan yace, "Umma. Baba. Ina mai baku hakuri akan abun da ya faru. Dukkanin abun da ya faru da Hafsat nine na janyo mata. Angel, kiyi hakuri ki yafe min." Ya lumfasa sannan yace, "Akan aurena da Hafsat, zanyi farin ciki idan tace zata zauna dani, amma idan taga ba zata iya ba, zan sawwake mata amma zata bar Muhammad a hannun Momcy."

Hafsat ta dubeshi da sauri jin maganarsa ta karshe, duk wahalar da tasha da cikin amma yana k'ok'arin rabata dashi, tace, "Hisham mi yasa kake da sonka kanka ne? Nayi wahala da cikinsa amma kana min barazana dashi domin abun da fad'a ya fi kama da barazana wato idan ina son zama tareda yarona saidai in zauna da kai, wannan ba adalci bane ba." Hisham yace, "Kiyi hakuri ina son gudan jinina..." ta katseshi tace, "Sai aka ce ni bani son kasancewa dashi, miye ka daukeni muguwar uwa ko kuma sakarar uwa." Yace, "Ba haka nike nufi." Ta daka mashi tsawa tace, "Torh miye kake nufi? Kayi min bayani. Huh."

Baba yace, "Hafsat. Hukunci yana a hannunki, dukkanin hukunci da kike yanke muna tare dake."

Umma tace, "Hafsat dukkanin hukunci da kike yanke ina tare dake, na janye waccen maganar, ko waye kika kawo indai har nayi bincike na samu ba ya da damuwa zan aura maki."

Hafsat tayi shiru ba tareda tace komai ba. Idanun kowa suna a kanta suna jiran jin hukuncin da zata yanke.
Chapter 27 · 0% Book details