← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 47

Sashe 30

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji tayi haushi ya kamata, zuciya ta kawo mata wuya, ta daka mata tsawa tace, "Hisham baka da kudin da za ka bani, baka da abun da za ka bani, kudi indai har daga gareka ne bana buk'atarsu. Kasan waye Aliyu kuma kasan tarin dukiya da yake dashi, kasan shine wanda nike so, na aureka ne saboda na rasashi. Abun da na kawoni kuma zan koma da abuna, akwai ranar kin dillanci ranar da zaka gane kuskurenka akan rashin adalci da kayi min."

Hisham ya fitar da ita waje ya maida kofa ya rufe tana ji yana wa mai guard gargadi akan kada ya k'ara barinta ta shigo gidan, ya kira yana sanar da a siya mashi tikitin zuwa London.

Ji tayi hawaye sun zubo mata ta saka hannuwa ta gogesu, ta juya saida tayi tafiya mai nisa sannan ta samu Kekenapep ta hau ya sauketa ofishin Aliyu.

Ta zauna ta fashe mashi kuka, yana rarrashinta amma kamar k'ara tunzurata yake, ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar dashi. Ya fusata ranshi ya b'aci, "Ki tashi muje, a yau sai na nuna mashi cewa kina da gata." Tana sheshshekar kuka tace, "Please idan har kana sona ka rabu dashi." Ya daka mata tsawa yace, "Kiyi min shiru a nan, ki tashi muje." Ta fashe da kuka tace, "Shikenan idan na mutu kun hutu." Ya koma ya zauna yace, "Angel ina sonki shiyasa na fusata da abun da yayi maki." Tace, "Na sani amma kayi hakuri ka rabu dashi akwai ranar kin dillanci a ranar ne nike son ka nuna mashi b'acin ranka, a ranar ne nike son ka nuna mashi ina da gata."

Har gida ya sauketa da kansa yayi wa Umma bayani akan abun da ya faru, ran Umma ya b'aci sosai ta kira Malam Jafaru mahaifin Jalila ta sanar dashi, suka yanke akan washegari zaije har gida ya sameshi da maganar.

Tana kuka ta kira Jalila ta sanar da ita yadda sukayi, tana tuna abun da yayi mata tana k'ara jin ciwo a zuciyarta, tayi zaman aure dashi tayi mashi halarci na zama dashi duk da gaskiya da taji akan yaudararta da yayi amma ya rasa abun zai saka mata dashi sai butulci. Tana mai cigaba da kuka na tausayin kanta da kanta tace, "Jalila na je ko tsayawa ya saurareni bai yi ba, yana treating dina kamar wata annoba har da cewa zai daukesu har da Momcy da Fatima zuwa London a yau saboda kawai taje gidan, bai tsaya ya saurareni ya kama hannuna ya fitar dani waje ya kulle kofa, ina ji yana kiran waya akan a siya masu tikitin zuwa London, ina ji yana wa mai gadi gargadi akan idan ya k'ara barina na shiga gidan a bakin aikinsa."

Jalila ta jinjina kai tana mamakin butulci irin na Hisham shiyasa yake da kyau bincike kafin aure, Umma tace sai mai kudi, Hafsat ta fusata da abun da tayi mata ta yanke hukunci a cikin fushi, yanzu waye gari ya waya, su.

Daga daya bangaren tace, "Ki share hawayen ki daina kuka akan abun da muke da maganinsa, yanzu zan kira Baba in sanar dashi sai asan yadda za'ayi."

Hafsat ta ajiye wayar, tana mai fashewa da kuka, bayan mintina talatin Umma ta shigo ta sameta kwance akan gado tayi lamo, ta zauna a gefen gadon tace, "Hafsat kiyi hakuri ki yafe min, dukkanin abun da ya faru da ke ni ce na janyo maki. Kwadayin kudina ne ya jefaki a damuwa da kike a ciki."

Ta mike zaune tana mai girgiza kai tace, "Please Umma, babu abun da kika yi min. Na sa ni cewa ba kwadayi bane ya saka kika ce sai mai kudi, na sa ni kin ce sai mai kudi saboda kina son rayuwata ta inganta saboda kina son in huta a rayuwa. Abun da ya faru laifina ne, na auri Hisham ne saboda na yanke hukunci a cikin fushi. Umma kinyi min sadaukarwa mai yawa a rayuwata, kin soni fiye da komai, kin sadaukar da farin cikinki a saboda ni, saboda baki son rayuwata ta tarwatse. Komai da ni ke yi ina yi ne domin in faranta maki. Umma idan har ina raye ba zakiyi hawaye ba."
Umma tace, "Allah yayi albarka." Hafsat ta amsa da, "Amin."
Washegari da marece Malam Jafaru ya nemi ganin Umma da Hafsat, a motarta sukaje gidan wanda Hafsat ta siya masu a lokacin da tana auren Hisham.

Fuskarsa babu walwala yace, "Hafsat naje har gidanshi da gidansu amma an sanar dani cewa sunyi tafiya kasashen waje."

Umma tace, "Yanzu ya kike ganin za'ayi?"

Hafsat tace, "Umma. Baba. Ku rabu dashi. Allah yana sane dani kuma shine zai kawo min mafita."

Sun jima suna tattaunawa akan al'amarin saida marece sannan suka koma gida, ta cigaba da karatunta tareda kasuwancinta, tana mai rainon cikinta, Aliyu ya taimaka mata sosai a wajen kula da cikin musamman a lokacin da cikin yayi nauyi, he help her throughout the pregnancy, yana bata kulawa sosai, har a zuciyarta tana matuk'ar sonshi, bata da burin da ya wuce aurenshi domin ya nuna son da bata tunanin zata samu wanda zai sota har haka, tana mashi son da ba zata tab'a wa waninsa ba.

Da tsohon ciki tayi jarabawar karshe, ranar graduation saidai ta kanga graduation jacket dinsu tayi a saman jikinta, sukayi hotunan graduation.

Sati biyu a tsakani, da misalin karfe goma na dare nakuda ta kamata, hankali a tashe Umma ta kira Aliyu, mintina biyar a tsakani yazo a motarsa, Umma ta tayar da ita, ya wuce dasu asibiti, aka wuce da ita dakin haihuwa.

Hankalinsa a tashe yana kaiwa yana komowa, dukkanin wanda ya gansa a wannan lokacin sai ya dauka matarsa ce. Karfe hudu na asuba ta santalo d'anta namiji mai KAMANNI da Hisham sak kamar an tsaga k'ara an karya.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 14

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

Aliyu ya amshi jaririn yana kallonshi yana murmurshi, jin yaron yake tamkar gudan jininsa, Hafsat ta d'aga kanta dakyar tace, "Yaa Aliyu kayi mashi huduba da dukkanin sunan da kake so." Ya dan kalleta yace, "Kin tabbata." Ta gyad'a kai tana mai sakar mashi murmurshi, yayi mashi huduba da suna Aliyu, da murmushi akan fuskarsa yace, "Allah ya raya takwarana Aliyu." Tayi matuk'ar farin ciki da wannan sunan, tana son Aliyu, tana son sunansa da komai a kansa, ya nuna mata so, yayi mata halarci. Ta share hawayen da suka zubo mata a sanadin tunawa da tayi da wulakanci da kaskanci da Hisham yayi mata. Ta ce, "Babana." Ya dan dubeta, tace, "Ka zame min tamkar uba, ka zame min gata, ka zame min bango majingina, Ina sonka Aliyu." Yayi mata murmushi yace, "Koda wannan Aliyun yayi maki laifi," yayi nuna wa kansa ya dora da cewa, "Ga wani Aliyu a tare dake. Koda anyi nasarar rabaki da wannan Aliyun a karo na biyu, ga wani Aliyu a tare dake. Ki kula da Aliyu."

Ya zuba mashi idanu ban da kinta da mahaifiyarsa takeyi miye zai rabata dashi, yana matuk'ar sonta, yana tausayinta, ya damu da damuwarta. Tana zubar da hawaye ta ce, "Ban tab'a kin Aliyu ba. Burina shine in auri Aliyu." Yace, "Allah ya ba Aliyu ke." Ta amsa da, "Amin." Tana jin matuk'ar farin ciki akan addu'ar da yayi. Yadda yake kallonta ya sakata juyar da kai bata jure wannan kallon ba, ji tayi yace, "Aliyu ya gode da kauna." Tace, "Allah ya raya Babana." Aliyu yace, "Amin."

A ranar Jalila ta dauki hutu ta kamo hanyar Katsina daga Sokoto, a asibiti ta tarar da su, nurses da likitocin da suka karbi haihuwar Aliyu sukeyi wa kallon Mahaifin yaron saboda yadda yake zirga-zirga a kansu, washegari aka sallamesu suka wuce gida.

Siyayya sosai Aliyu yayi masu saidai ganinsa sukayi da kaya niki-niki, tun cikin yana k'arami ta sayi dukkanin abun da zasu buk'ata, har rago ta siya, da geron kunu, suger, da kayan abinci.

Ranar suna sai ga Aliyu da raguna har guda biyu, aka hada da wanda ta siya aka yanka raguna ukku, kwangilar abinci ya bada saidai suka ga ana shigowa da manya-manyan kulolin abinci, anyi shagali sosai, (a nan na hango Member na ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION, Mama Gee, Fahaus chambo, Diamond Bhatool, Mjungudo, Oum Hafsat, Maman Kamal, Mmn Useey, Garba Fatima, Fauziyya Ibrahim Kam, Oum Aftnoor, Aeesharh, Nudar Rabiu, Hauwau Abdullahi da sauran members suna ta kaiwa da komowa na hidimar baki, nidai babu ruwana tunda ba'a gayyaceni ba, atorh 😅 🤣 😂) anci, ansha, baby da maman baby suna samun kulawa sosai.

Cike da kulawa Hafsat take rainon Aliyu, sabon shafin soyayya suka bude ita da Aliyu, a koda yaushe sonshi k'ara linkuwa yake a cikin zuciyarta, Hajiya Zainab (mahaifiyarsa) har gida ta tarar Angel tayi mata tatas akan tayi gaggawar rabuwa da Aliyu domin diyar er uwarta zata aura mashi.

"Saboda rashin zuciya na rabaki da yarona kin manne mashi, tun wuri kiyi gaggawar rabuwa dashi domin ba sa'an aurenki bane."

Hafsat tana zubar da hawaye tace, "Amma Ummi ina sonshi yana sona, miye illata da har baki son ya aureni."
Ummi tayi mata kallon kaskanci tace, "Saboda ke talaka ce marar galihu, wacce bata da asali mai kyau. Na fi karfin in had'a jini da talaka kamar ki tun wuri ki nemi sa'an aurenki domin diyar er uwata Aliyu zai aura idan baki da labari a yau na sanar dake."
Chapter 30 · 0% Book details