← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 47

Sashe 16

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Magrib Hisham ya aiko direba ya kai Jalila gida.
Washegari aka saki Omar, duk da gargadi da aka yi mashi da rubutu da yayi amma taurin kai da zuciya ya kwasheshi kai tsaye ya wuce gidansu Hafsat, matan gidan suna zaune a tsakar gida suna gulmar Hafsat da Ummarta wanda ya zama maganar gulmarsu saidai idan basu zauna ba.

Ya fado masu ko sallama, suka mike da sauri suna kallonshi, yayi turus ganin dakinsu wayam babu komai a ciki, ya juyo tareda daka masu tsawa yace, "Suna ina?"

Farida muryata tana rawa tace,
"Sun tashi."

A tsawa ce yace,
"Ina suka koma?"

Saida suka mashi kwatance sannan ya fita, Jumala ta tab'e baki tace, "Gwara yaje yaci uwarsu, maganin kwadayayyu, shine daidai dasu. Rokona Allah ya saka su dawo su cigaba da zama a nan."

Murjah tace, "Allah yasa ya k'arya Hafsar muga yadda wancen zai aureka. Rayuwar k'arya kawai. Suna kai kansu inda basu kai ba."

*******

Hafsat tana zaune a tsakar gida ta baza takardu a saman carpet tana karatu, Umma ta fito ta dauki buta ta wuce bandaki, motsi taji ta d'ago wanda yayi daidai da shigowar Umar, gadan-gadan ya nufo inda take kamar mayuwacin zaki, da gudu ta shige parlour ta maido kofa ta saka sakata, ta kware murya tace, "Umma ki kulle kofa, Umar yana a tsakar gida."

Umma ta mike tareda saka sakata ta sama bayan ta kasa da ta saka tun bayan shigarta, hankalinta a tashe tace, "Angel kina ina? Mun boni."

Hafsat ta kware murya tace, "Umma ina a parlour na kulle, bazai iya shigowa ba."

Dukan kofar falon yake kamar zai b'allata yana cewa,
"Angel tun muna shaida juna ki bude kofar nan, idan kika bari na b'allata abun ba zaiyi mamu da kyau ba, yau za'ayita ta k'are, da in rasaki gwara kowa ya rasa."

Ta dafe kirji tana mai godewa Allah da suka baro wancen domin idan can ne bugu daya zaiyi wa kofar ya cimmata.

Ya daka mata tsawa, "Zaki bude kofar ne ko kuma sai na b'allata na had'a maki da hukunci." Ta zaro idanu yayinda baki daya jikinta rawa yake, Umma dake a bandaki itama a tsorace take.

Hannun Hafsat yana rawa ta zaro wayarta ta kira Hisham, ta fashe da kuka yayinda muryarta ta kasa fita saboda tsoro.

Ya murmusa yace, "Umma bata son zaman lafiya damu, miye kikayi mata yau kuma na tabbata kece baki da gaskiya."

Tana mai k'ara sautinta kukanta tace, "A tsorace nike, Umar yana tsakar gida yana dokan kofa zai b'alleta." Ta k'arasa maganar da muryarta da take rawa saboda tsoro. Ta kwashe abun da ya faru dashi ta sanar dashi muryarta tana rawa.

Zaro idanu yayi yace, "Ki shiga daki ki kulle." Tana mai cigaba da kuka tace, "Umma tana bandaki amma itama ta kulle."

Hisham yace, "Gani nan zuwa." Ya dauki makullin motarsa ya kama hanyar gida, Najeeb yabi bayanshi yana tambayarshi abun da ya faru. "Najeeb saida nace kubar yaran nan ya girbi abun da ya shuka amma kuka hanani, gashi nan yana baro ofishin en sanda ya wuce gidansu."

Jami'an tsaro suka zagaye gidan yayinda wasu suka shigo suka damkeshi, ihu yake yana hargowa, Hisham ya shiga ciki yayi knocking akan kofa yace, "Angel. Ki bude nine."

Hafsat ta bude da sauri tareda rungumeshi muryarta tana rawa tace, "Hisham a tsorace nike. Tsoronsa nikeyi."

Hisham yayi mutuwar tsaye jin shock a jikinsa, ya zagaye hannuwansa a bayanta yana bubbuga bayanta, ankara da katobarar da tayi ta sakeshi da sauri ta tureshi, ta kwankwasa kofar bandaki tace, "Umma ki fito, sun zo sun kamashi."

Umma ta bude kofa, suka rungume juna yayinda Hafsat ta fashe da kuka tace, "Umma na tsorata, yazo ne ya cutar dani, mun boni mun lalace."

Umar ya kufce ya nufo inda suke gadan-gadan, Hafsat ta fasa ihu ganin ya nufo kanta kamar mayuwacin zaki.

Kamar walkiya Hisham ya shiga tsakaninsu tareda kai mashi duka, a take Umar ya zube a kasa warwas, suka kwasheshi sukayi waje.

Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tace, "Umar miye haka? Soyayya ce, ba'a dole. Tun da ba tare aka haifemu ba, sai ka rabu dani."

Hisham yace, "Umma ku fito in wuce daku daya gidana wanda yake a titin gidanmu, zamanku ku kadai bazai yiyu ba, a wancen gidan akwai mai guard da security."

Umma ta mikar da Hafsat suka tattara abubuwan da suka zo dasu suka fito, Hafsat ta bude bangaren mai zaman hakanan ta shiga yayinda Umma take a gidan baya, Hisham ne yake jan motar, bodyguard dinsa suna biye dasu. A bakin wani katon gida yayi horn aka wangame mashi get ya danna motar ciki, da mamaki suke kallon gidan, katon gida ne gari guda wanda yake dauke babban harabar gida, wajen ajiye motaci, wajen wasan yara, garden, swimming pool, boys quarters yana daga gefe, gida ne mai girma sosai.

Mai guard ya rusuna yana kwasar gaisuwa, Hisham ya d'aga mashi hannu kawai, yayi gaba suka bi bayanshi, katon parlour ne wanda yake dauke da kusan setin kujeru guda biyar a wajaje daban-daban, akwai study room, kitchen, toilet, dinning area, dakuna ne birjik a kasan bene da saman bene.

Hafsat tayi turus, Umma tace, "Hisham wannan gidan yayi mamu girma." Ya girgiza kai yace, "Umma a nan ne kawai zan barku hankalina ya kwanta, akwai tsaro sosai, zamanku ku kadai bazai yiyu ba, akwai mai guard da security. Ku zauna." Ya k'arasa maganar yana masu nuni wa kujera. Gida kamar a kasar waje. Suka zauna, bai jima ba ya wuce.

Bayan ya sanar da Momcy abun da ya faru tace, "Hakan yafi. Allah ya k'ara tsarewa." Hisham yace, "Na aika a kai mata motar da na siya mata."

*****

Hafsat ce tsaye a harabar gidan tana kallon motar dake a gabanta cike da mamaki, irin wacce suka dawo daga school ce sak saidai kalarta ce ta banbanta, ta amshi makullin motar ta shiga, da murmushi kwance akan fuskarta ta danna mashi kira yana d'agawa tace, "Na gode sosai motar tayi kyau. Allah ya k'ara budi."

Daga daya bangaren yace, "Tunda tayi maki kyau kiyi min hira." Ta zauna a balcony tana mashi hira yana dariya.

A ranar ya saka aka cika masu store da abinci, ba na wancen gidan bane ba, wasu ne daban, Jalila ta taimakawa Hafsat suka saka fruit, ruwan gora da drink a fridge. Suka saka kaji a freezer.

Saida Magrib sannan Jalila ta wuce gida, washegari da safe suna a parlour aka yi kwankwasa, Hafsat ta yane kanta da mayafi sannan ta fita, daya daga cikin yaransa ne tareda wasu mata guda ukku, ya rusuna ya gaidata sai taji kunya ta kamata kasancewar ya girmeta, yace, "Ranka shi d'ad'e, yace in kawosu, en aiki ne." Tayi jim tana kallonsu sai kuma tace, "Okay, su shigo." Ta zaro kudi kimanin dubu talatin ta bashi tace, "Gashi ka saka fuel." Ya amsa yana godiya.

Kadan da kadan Hisham yake koyar da ita yadda masu kudi suke rayuwa, da kanshi ya bata kudade saboda irin haka.

Ta juya ta koma ciki yayinda sukabi bayanta, Umma da mamaki take kallonsu, ta jefa mata tambaya, "Su waye?" Tace, "En aiki ne inji ranka shi dade."

Umma ta ware idanu tace, "Kika ce?" Tace, "Masu aiki ne inji yaya Hisham."

Suna a tsaye, Hafsat ta tuna yadda tayi da aka gabatar mata dasu, tayi mamaki ne a lokacin amma idan aka had'a da yadda sukayi yanzu, matan zasu daukeshi a matsayin mutane masu wulakanci da izza ne.

Ta ajiye wayarta tace, "Ku zauna. Miye sunanku."

Suka zame a kasan carpet, daya tace, "Sunana Iman." Ta tsakiyar tace, "Ni kuma sunana Hajara." Ta daya gefen tace, "Sunana Mardiyya."

Hafsat ta jinjina kai sannan tace, "Iman. Hajara. Mardiyya. Kun san miye aikinku, ba sai na tsaya maimaita maku, a boys quarters zaku zauna, idan kuka zo kuka gama ayyukanku zaku koma wajen zamanku, ban san hayaniya, idan kuka kiyaye zamu zauna lafiya, ban san yawan shige da fice, babu girki a cikin ayyukanku har sai idan an umarceku ne, ku girka abincin da zaku ci a boys quarters ku baiwa mai guard da sauran masu kula da gidan nan, ban san inji wani yayi kukan yunwa kowa a zuba mashi daidai cikinsa. Ban san ganinku kusa da kitchen, da girkinmu, da gyaran kitchen zamuyi abunmu saidai idan muna buk'ata su tayamu zamu kiraku. A cikin ayyukanku ban da gyaran dakunanmu, da kaina zan rink'a gyara dakina da na Ummana, ku gyara sauran da kuma parlour. Bana san k'azanta, kowace tasan a inda tafi kwarewa sai kuje kuyi shawara da kanku, kowace ta dauki abun da zatayi. Ban san hayaniya, ban san gulma, da shiga harkar da babu ruwan mutum, zaman hira da maza masu aiki. Zaku iya tafiya." Ta ajiye masu kudi, daya daga cikinsu ta dauka sukayi godiya suka fita.

Suna fita, Mardiyya tace, "Da farko har jikina yayi sanyi ganin kamar tana da izza da wulakanci." Iman tace, "Koma miye hakuri zakiyi neman kudi kika zo, kowa kika gani yana hali mai kyau da marar kyau saidai wani ya rinjayi wani. Idan kikayi zama da masu ne zaki samu alheri a wajensu."

A falo, Umma ta dubeta tace, "Hafsat. Miye haka?" Hafsat tace, "Umma nayi mamaki ne, mune da masu aiki, saura kadan dariya ta kufce min shiyasa na fuske nayi haka. Umma gidan nan mune muke zaune a ciki, dole mu lura saboda gudun samun b'araka daga wajensu."

Umma ta gyad'a kai tace, "Amma kamar abun yayi yawa." Hafsat tace, "Umma kin fini sanin hakan, idan aka barsu sakaka kowa cewa zaiyi yayi abun da ranshi yake so." Umma tace, "Hakane." Ta tuna kalubale da ta hadu dashi a gidajen da tayi aiki kafin ta samu gidan da take aiki a yanzu.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 9

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
Chapter 16 · 0% Book details